Breaking News

Sakayyah Book 2 Page 2

 

          *GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 2*

 

 


Spbnɗettett. Cikin ɗan sakin fuska Mommy ta miƙe tare da cewa.

“Wa'alaikum Salam Hajja Nana sannunku da zuwa”.

Hajja Nana na zama aÉ—aya daga cikin kujerun falon tace.

“Yawwa Aysha sannunki”.

Cike da farin ciki Khausar ta miƙe tare da riƙe hannun Dije kana ta jata suka zauna akan 2sitter.

Murmushi Mommy tayi tare da juyawa ta shiga kichen.

Ta kawo mu abin taɓa,

Fuska É—auke da murmushi Khausar dake riÆ™e da hannun Dije ta juya tare da kallon Hajja  data zuba mata Ido, cikin sanyi  tace.

“Maraba Hajja Nana ya gida ya Baffa Liman, Baffa Jauro,Baffa Sadu, Baffa, Garga Yaya Sadik? Duk kowa da kowa dai”.

Harara Hajja Nana ta watsa mata kana tace.

“Sai yanzu kika ganni wacce ta dameki ai gashi tun shigowarta kika jata jiki, kuke gaisawa idan kin matsu da sanin yanda suke sai kije ki duba su da kanki”.

Uhum kawai  Khausar ce tare da loggobar da kai dan har yau bata dawo dai-dai ba cikin sanyi tace.

“Kai wannan tsohuwa ke dai akwai ki da kishi, da mita ina ce dai yanzu gashi na gaishe ki amaimakon ki amsa shine sai kin cakaleni”.

Riƙe haɓa Hajja Nana tayi tare da maka mata Harara kana tace.

“Yo ki riÆ™e abinki mana ko wata tsiyar gaisuwar ki zai min?”.

Ta ida maganar tare da sauÆ™a ta É—auki Cup É—in tea da Mommy ta zuba mata kana ta kurÉ“a”.

Taɓe baki Khausar tayi tare da cewa.

“Oho dai ai ko bazai miki amfani ba kin nema bare ma amfanin zai miki”.

 

Mommy da fitowarta daga kichen kenan tayiwa Khausar alamar tayi shiru kana ta zauna gefen Hajja Nana cike da girmamawa ta gaisheta tare da tambayar mutane gida.

 

Miƙewa Khausar tayi tare da riƙe hannun Dije tace.

“Zo mushiga ciki”.

Saurin Kallonta Hajja Nana tayi tare da faÉ—in.

“Dawo ki zauna”.

Tsayawa tayi tare da kallon Hajja Nana still hannunta na riƙe da Dije tace.

“Toh  me kuma zan miki?”.

Sassauta murya Hajja Nana tayi tare da faÉ—in.

“Ke kam ki dawo ki zauna mana”.

 

Sake hannun Dije tayi tare da tsare Hajja Nana da ido kana tace.

“To wai mai zan miki zamuje muyi hiranmu irin na Æ´an Uwanta kema kuyi hiranku mana ko sai dole na zauna ne?”.

Harara Hajja Nana ta maka mata tare da cewa.

“Wato ke dai daga zuwana sai kinsa mun raba hali, ko ba a isa ace yi kiyiba sai kinyi musu?”.

 

Kallon Khausar Mommy tayi tare da cewa.

“Ke dai ki dawo ki zauna mana koma menene ai zaki ji”.

Kai ta gyaÉ—a tare da janyo hannu Dije suka zauna gefen Mommy ya zamana Khausar na fuskantar Hajja Nana.

Hajja Nana kuwa zamanta ta gyara tare da fuskantar Mommy Cike da isa, gadara, taƙama, Iko, kana da Power da take jin tana dashi akan Khausar da kuma rigima irin ta tsofaffi tace.

“Alhamdilillah mun godewa Allah daya nuna mana lokacin da Khausar ta gama karatu lafiya”.

Cikin sauri Khausar ta kalleta tare da cewa.

“An gama karatu lafiya ko kuma anfara taka matsayin karatu? Ko tsakiyar karatu ma naje ne bare akai ga maganar gamawa?”.

Wani kallo Hajja Nana ta watsa mata tare da cewa.

“Karatun Æ™a'ida kam nasan angama shi tunda kinyi haddar Alkur'ani kin sauÆ™e sannan kinsan, Ahallari, Kinsan  ishmawi, Kinsan Fiqhu, Kinsan Arbauna, Kinsan Sira da sauransu yanzu wani karatu ya rage miki”.

 

kallonta kawai take sai data gama jerawa kafin tace.

“Karatu kam wanda ya ragene yafi yawa aisharan fage kawai nayi acikin karatu”.

Harara Hajja Nana ta watsa mata cikin yanayin zafinta tace.

“A'a sannu Al-huda-huda sarkin karatu dole kika ce sharen fagi kikayi mana, tunda kin samu anbarki kinyi wannan É—in”.

Sake baki Khausar tayi tare tura baki kana tace.

“Ikon Allah dana samu anbarni nayi da mekike nufi kenan, ko kuma dama kece zaki tsara min abinda zanyi?”.

 

Gyara zama Hajja Nana tayi cikin ƙanƙance Ido tace.

“Ke ko kunya bakya ji dube ki fa duk kin gama girma agida shekarunki kusan Ashirin ai wannan ma taumaka miki za'ayi dan kin gama tsufa”.

 

BuÉ—e baki Khausar tayi tare da kallon kanta kana ta kalli Hajja Nana cike da Isa Hajja Nana tace.

“Kalleni da kyau yo Æ™arya na miki, Æ™annen bayanki nawa aka Aurar wasu da yara bibbiyu wasu kuma É—addaya ke kam wannan wani sai dai yace bazawara ce ke dan kin gama girma”.

Wani kallo Khausar ta mata tare da cewa.

“A'a Hajja Nana ya isa haka cin fuska dan wlh bazan juraba.Wanda suka fini dubu nawa ne basuyi Aure ba, sai dai idan A Rugar kune ake irin wannan Auren, amma nikam yanzu ma nayi Æ™arama da  Aure.

Mommy kuwa kallon Khausar tayi tare da É—aga mata hannu kana tace.

“Haka naki Khausar kiyi mana shiru”.

 Sunkuyar da kanta Æ™asa tayi batare da ta sake cewa Uffan ba kawai dai tasan in ba ita ke tare Hajja Nana ba Mommy kam ba abinda zatace tanaji tana gani za'a tauyeta.

 

Hajja Nana Khausar ta nunata da É—an yatsa tace.

“Ki kiyayeni bada ke nake magana ba fitsararriya mara kunya!”.

Gyara zama Khausar tayi tare da juya mata manyan Idanunta da kawar da kai gefe.

Murmushi Dije dake gefen Khausar tayi tare  da riÆ™e hannun ta da ido tayi mata alamar ta daina.

Gyaran murya Hajja Nana tayi tare da cewa.

“Aysha Ni dake nake magana bada Khausar ba, ya batun maganar da mukayi tunda Allah yasa tagama yanzu, sannan makon daya gabata Baffanta yazo daga Adamawa aranan daya zo aranan ya koma”.

Sai kuma ta kalli Khausar tare da watsa mata Harara kana ta maida kallonta kan Mommy dake sauraronta tace.

“Toh dama ace yazo da niyyar kwana zamu Æ™ara so nan, ayi magana to amma ke me kikace tsakaninta da Aliyu É—an Uwanta!?”.

Ahankali Mommy ta sunkuyar da kanta ƙasa kana tayi shiru cikin yanayin sanyinta da Kawaici, da mutumtaka da kuma kamala tace.

“Toh Hajja Nana wannan magana duk yanda kuka zantar ai hakane  Baffanta shine me Aurar da ita, dan haka duk abinda ya yanke akanta shine dai-dai”.

 

Jinjina kai Hajja Nana tayi tare da tura kallabin kanta kana ta gyara zamanta cikin jin daÉ—i tace.

“Shima yace min Insha Allah nan da wata É—aya ko sati uku zai zo idan ya samu sarari zaizo su zanta da Uban goyon yarinyar, shima abashi mutuncinsa tunda shi ya raineta tun tana da wata wata uku shi yamata komai”.

Kai Mommy ta gyaÉ—a tare da faÉ—in.

“Bakomai duk abinda kuka tsara yayi Idan har Auren Khausar da É—an Uwanta Al'khairi ne Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa”.

 

Cikin sauri Khausar ta tura bakinta tare da cewa.

“Ni dai bana sonshi kuma ke dai Mommy ayita Addu'ar alkhairi”.

Wani kallo Mommy ta watsa mata alamar rufe min baki, shiru Khausar tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa Mommy kuwa kallon Hajja Nana tayi cikin sanyin murya tace.

“Ni dai Allah ya tabbatar da al'khairi idan al'khairi ne Allah ya tabbatar ya kuma zaÉ“a musu abinda yafi zama al'khairi atsakanin su.

Gyara zama Hajja Nana tayi kana tace.

“Ammen,Kuma Insha Allahu ma alkhairi ne”.

Kai Mommy ta gyaÉ—a tare da cewa.

“Adduar da mukeyi kenan”.

Miƙewa Khausar tayi tare da riƙe hannun Dije da alamun ɓacin rai tace.

“Dije mu tafi”.

 

Harara Hajja Nana ta watsa mata tare da sake tura daurin Kallabinta gaba kana tace.

“Aikuwa wannan magana ya zama dole ki saurareta tunda batu ne na Aurenki akeyi”.

Cikin ƙankance Ido Khausar tace.

“Nifa bazanyi Aureba ehe  ke baki da aiki sai Æ™aÆ™ale Æ™aÆ™alen magana ina ruwanki da batun Aurena!?”.

Afusace  ta kalleta kana tayi Ƙwaffa tare da cewa.

“Aikuwa dan Ubanki nike da ruwa dake kuma dole kiyu Aure”.

 cikin tsirawa Hajja Nana ido tace.

“Amma dai na faÉ—a miki ki daina zagin mahaifina Aure kuwa idan Allah ya nufa zanyi amma ba wanda kike cewa ba kam!?”.

Ajiyar zuciya Hajja Nana ta sauke kana tana kallonta bako ƙyaftawa sai kuma ta sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.

“To wa kike so ki Aura?”.

Juya ido Khausar tayi tare da cewa.

“Aini nasan wanda zan Aura, kuma dan haka babu ruwanki dani sai kace ke lokacin da zaki yi Aure zaÉ“a miki wanda zaki Aura akayi ba ke kika zaÉ“a da kanki ba!”.

 

Girgiza kai Mommy tayi tare da nunawa Khausar hanya da hannu alamar tabar wajen ita har ga Allah bata so ma Hajja Nana ta tsaida Khausar a cikin mgnar ba in bana tsohuwaba taya zata tsaida Khausar bayan tasan yadda suke da juna.

Tura baki Khausar tayi tare da jan hannun Dije dake murmushi sam bata gajiya da kallon Dramer Khausar da Hajja Nana.

Khausar da Dije na isa ƙofar Bedroom ɗin zasu shiga Akuma dai-dai lokacin Asma'u tayi sallama cike da ladabi tsugunna agaban Mommy ta gaisheta Cike da kulawa Mommy ta amsa tare da tambayarta ya Umminta ta amsa da tana lafiya.

Kana ahankali ta maida kallonta kan Hajja Nana dake cin Inabi tace.

“Hajja Nana inayini fatan kunzo lafiya?”.

Kai Hajja Nana ta gyaÉ—a tare da cewa.

“Lafiya lau Alhamdulillah Allah ya miki albarka kar dai ki riÆ™a É—aukar hallayar wasu Æ™awaye na tsiwa”.

Ɗan murmushi Asma'u tayi kana cikin sanyi ta gyaɗa kanta Khausar dake tsaye bakin ƙofa ta wani ɓata fuska tare da kawar da kai gefe.

 

Miƙewa Asma'u tayi ta nufi wajensu Khausar suka shiga Bedroom cikin ɗan sakin fuska da sanyi Asma'u tace.

“A Dije sannu da zuwa ya gida ya mutanen Jauro yaya!?”.

Murmushi Dije tayi cikin yanayin sanyin ta tace.

“Duk lafiya lau?”.

Kallon Dije Khausar tayi kana cikin sanyin tace.

“Ayyah Dije yayan Asma'u Malam Jameel Allah ya masa rasuwa kwanan nan Æ´an Kidnapping suka kashesa!”.

Cike da tausayawa Dije tace.

“Ayyah Ubangiji Allah yajiÆ™an sa da rahma sukuma Allah ya tona musu asiri”.

Atare Asma'u da Khausar suka amsa da.

“Ameen”.

Asma'u kuwa Idanunta ne suka ciko da ruwan hawaye.

Cikin sanyi Khausar ta dafa kafaÉ—ar ta kana tace.

“Dan Allah Asma'u kiyi haÆ™uri kin sani babu abinda Yah Jameel ke buÆ™ata awajenmu face addu'a Insha Allah Yah Jameel na cikin rahamar Allah”.

Jinjina kai Asma'u tayi kana cikin sanyin murya tace.

“Insha Allah muna yi kuma zamu cigaba dayi”.

Miƙewa Asma'u tayi tare da kallon khausar cikin sanyin murya tace.

“Toni zan tafi”.

Da sauri Khausar ta É—ago kanta cike da kulawa tace.

“Sauri-sauri haka”.

Kai Asma'u ta gyaÉ—a tare da lumshe Idanunta cikin sanyin murya daya zame mata jiki tace.

“Wallahi gidan Innayi nake son zuwa dama na biyo ne akan ince muje ki rakani kuma sai na ganki da baÆ™uwa, shiyasa nayi shiru bance komai ba”.

Ajiyar zuciya Khausar ta sauke tare da tsira mata ido cikin fesar da numfashi tace.

“Ayyah wallahi kuwa badan baÆ™uwar ba ai da naje na rakaki amma lafiya kuwa?”.

 Kai Asma'u ta gyaÉ—a tana gyaran zaman hijabinta tace.

“Eh Ummi ce ta aikeni wajen Innayi akan Inje wajen.

Yaya Moddibo yau kusan sati kenan bai sake zuwa gidanmu ba sannan kuma Innayi ma ta kirata tana faÉ—a mata ko cikin gida baya fita”.

Jinjina kai Khausar tayi cike da tausayinsu tace.

“Allah sarki Malam Moddibo dole ya shiga cikin tashin hankali da alhinin rashin.

 Yah Jameel insha Allahu jinin Yah Jameel da hakkinmu ba zai taÉ“a bari wannan mutanen su samu salama acikin rayuwarsu ba!”.

Kai Asma'u ta gyaɗa cikin sheshsheƙan Kuka tace.

“Tabbas sun cutar da rayuwar mu, cuta mafi muni sun zalunce mu kana sun É—auke mana duk wani farin ciki da walwalarmu. Yah Jameel shine Komai namu Yah Jameel shine fitilar dake haska zukatanmu amma dare É—aya suka rabamu da wannan hasken kuma jigonmu”.

Cikin sanyi da tausayawa Dije tace.

“Asmau'u kiyi haÆ™uri Allah baya zalunci sannan baya bari ayi zalunci da sannu Ubangiji zai fallasa asirin wanda suka aikata wannan ta'asar sannan sai sun wulaÆ™anta wulaÆ™anci mai muni insha Allah”.

Cikin sanyi da Khausar da su kaji mutuwar ya dawo musu sabo suka hada baki wajen cewa.

“Ameen”.

Miƙewa Asma'u tayi tare da faɗi.

“Bari na tafi dan Ummi tayi ta kiran wayarsa baya É—auka sannan itama Ummi baki daya bata jin daÉ—in jikinta sosai ta dawo tamkar majinyaciya.

 Khausar  sai kinga gidanmu baki É—aya duniyar bata mana daÉ—i”.

Cikin sanyin da rarrashi Khausar tace.

“Ayyah Asma'u am haka rayuwa ta gada Ubangiji Allah ya jikan Yah Jameel da rahma mu kuma Ubangiji yasa mana dangana azuciyarmu sannan mu cigaba dayi masa addu'a gatan da zamu nuna masa kenan”.

Kai Asma'u ta gyaÉ—a kana tace.

“in sha Allah, na tafi”.

Kai Khausar ta gyaÉ—a sannan ta kalli Dije tace.

“Muje mu rakata”.

Miƙewa Dije tayi sannan suka fita bayan Asma'u ta yiwa Mommy da Hajja Nana sallama har bakin hanya suka rakata saida ta samu adaidaita ta hau sannan suka koma.

 

Asma'u na isa gidan direct Sashen Innayi ta nufa zaune ta hango Innayi kan barandar ta tayi tagumi da hannunta na dama jin anɓude ƙofa yasa tayi saurin ɗaga kanta ganin Asma'u yasa ta saki Ajiyar zuciya.

Cikin sanyi Asma'u ta ƙarasa tare da zama agefenta cikin sanyin murya tace.

“Innayi”.

Numfashi Innayi ta fesar tare da tsira mata ido cikin alamun damuwa tace.

“Na'am Asma'u kin zo ya jikin Umminki!?”.

Kanta aƙasa tace.

“Innayi da sauÆ™i Ina Yah Moddibo fa?”.

Ajiyar zuciya me nauyi Innayi taja kafin ta sauƙe cike da damuwa tace.

“Asma'u bansan wani irin yanayi Moddibo yake Æ™oÆ™arin shiga ba baki É—aya ya zama wani iri ya dawo tamkar mara lafiya ya zama abin tausayi koda fitowa bayayi”.

Sai kuma ta runtse Idanunta cike da damuwa kana ta buÉ—e su tare da cewa.

“Ko abinci idan bana nuna masa É“acin raina ba baya ci banda ruwan tea Babu abinda yake sha baki É—aya ya sauya duk hankalina ya tashi na rasa yanda zanyi.

  Gaba daya Æ™asar nan tafi raina duniyar ta isheni”.

Sunkuyar da kai Asma'u tayi tana jin hawaye na cika kwarmin Idanunta.

 

Cikin raunin murya Innayi ta kalli Asma'u tare da cewa.

“Na rasa yanda zanyi da Moddibo É—azun nan ma Abban Jameel ya fita dalilin zuwansa da yayi masa.

 Nasiyya da kwantar masa da hankali shine ma muka samu É—azun yasha kunu”.

Numfashi mai zafi Asma'u ta fesar tare da kallon Innayi tace.

“Ummi ma tace tana som ganinsa baki É—aya ta damu da rashin zuwansa kuma koda ta kira wayarsa baya shiga bare taji muryarsa, Innayi barin shiga wajensa”.

Kai Innayi ta gyaÉ—a kana tace.

“Shikenan ba matsala muje”.

 

Miƙewa Asma'u tayi tare da nufar Sashen sa Innayi na biye da ita.

 Innayin ce ta tura Æ™ofar falon suka shiga ahankali Idanun Asma'u suka sauÆ™a akan Moddibo dake zaune kan 1sitter Ƙirjinsa Rungume da Alkur'ani yayinda idanunsa ke lumshe suna tsiyayar da hawaye kana dashash-shiyar muryarsa na rera karatun Alkur'ani.

Cikin mutuwar jiki Asma'u ta zauna daga gefen ƙafafunsa Innayi kuma ta zauna daga saman kujeran.

Ganin yanda hawaye ke fita Shar-shar-shar a idanunsa yasa Asma'u fashewa da kuka mai gunji hadda sheshsheƙa.

 

Jin sheshsheƙan Kukan Asma'u yasa Moddibo da idanunsa ke lumshe saurin buɗewa ganin yanda Asma'u ke kuka da sheshsheƙa yasa yayi saurin sanya tafin hannunsa yashiga goge hawayen dake saman kuncinsa.

Cikin sanyi Innayi ta kallesa tare da cewa.

“Moddibo!, Moddibo!!, Moddibo!!!”.

Ahankali ya ɗago kumburarrun Idanun sa da suka jiƙe da hawaye kana Eyelashes ɗinsa sun kwanta cikin sanyi ya kalleta.

Innayi kuwa cikin tsaresa da Ido tace.

“Moddibo za kayi fushi da hukuncin Ubangiji ne?”.

Cikin sauri ya girgiza mata kai tare da cewa.

“Astagafirullah³”.

 

Ajiyar zuciya ta sauƙe kana ta tsira masa Ido tace.

“Toh Meyesa Moddibo baka fita, baka cin abinci sannan baka walwala, kenan fushi kake da Ubangijin daya bamu Jameelu sannan ya É—aukesa!?”.

Kai ya girgiza mata batare da yace Uffan ba!.

Cikin sanyi da rauni Innayi ta zuba masa Ido baki ɗaya Garin Jahar Taraba da maƙasar Nigeria yafi ta ranta, fesar da numfashi kana tace.

“Toh Meyesa sai dai ka É—auki Kur'ani ka rungume kana karatu kana kuka”.

Cikin wata dashash-shiyar murya me cike da rauni da tashin hankali yace.

“Innayi mai zan fita nayi acikin garin Gembulan? Innayi da waye zan fita? Innayi baki É—aya garin nan ya fita raina bana son garin nan na tsani garin nan garin nan ya fita min araina”.

Sai kuma ya runtse Idanunsa da ƙarfi yayin da jijiyoyin kansa suka tashi ruɗu ruɗu dasu kana zuciyarsa ta shiga bugawa da masifar ƙarfi cikin dauriya ya buɗe idanunsa da suka yi masifar Ja yace.

“Innayi duk inda na wulga acikin garin Gembulan zanga kamar J É—ina na akusa dani, shin Innayi taya zan fara fita da waye zanyi yawo da waye zanje masallaci da waye zanyi dariya da wa zan dawo gida da wa zan zauna inci abinci!?”.

 

Asma'u kuwa kife kanta jikin kushin É—in da yake zaune tayi tare da fashewa da wani irin kuka tabbas sunyi rashin da baza su sake samun kwatankwacin saba sannan kuma anzalince su zalinci mai muni da raÉ—aÉ—i.

Jin yanda Asma'u ke kuka kamar ranta zai fita yasa Moddibo juyawa ya kalleta cikin sanyi da tausayinta yace.

“Asma'u ki daina kuka ki yiwa J addu'a domin shine abinda yake buÆ™ata atare damu”.

Innayi kuwa kallonsa tayi har zuwa lokacin hawaye na zuba daga idanunsa ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.

“Toh Moddibo kaima fa kukan kake ya za ayi Asma'u ba zatayi kuka ba”.

Kallon Innayi yayi tare da lumshe idanunsa wasu hawaye masu masifar zafi suka zubo masa.

 Anutse ya goge tare da cewa.

“Innayi idan har bana samu na rungume Kur'ani ina karatu ba bana samun damar hawaye suna zubo min, sannan aduk lokacin da hawayena ke zuba inaji kamar ana zare min wani abu mai nauyi ne acikin Æ™oÆ™on raina, shiyasa nake  rufe kaina ni kaÉ—ai nayi ta kuka”.

 

A tausashe ya kalli Innayi data tsaresa da ido ya cije Lip É—insa kana yace.

“Innayi idan har banyi kuka ba menene amfanin Idanuna da hawayena? idan ban zubar dasu arashin J ba J fa Innayi J É—ina”.

Numfashi Innayi ta fesar cikin sanyi tace.

“To ai addu'a zaka yi masa Moddibo”.

Cikin dashash-shiyar muryarsa daya dishe da kuka da tashin hankali yace.

“Innayi to ai ina masa addu'a”.

 

Asma'u kuwa ahankali ta ɗago Idanunta dake jiƙe da ruwan hawaye ta kallesa cikin sanyi tace.

“Yah Moddibo Meyesa ka daina zuwa wajen Ummi?.

Baki É—aya hankalinta ya tashi ta dawo kamar mara lafiya?”.

Girgiza kai yayi tare da kallonta kana cikin sanyi yace.

“Asma'u ki cewa Ummi tayi haÆ™uri insha Allah zan zo amma ina jin wanin irin yanayi ne taya zan kalli al'amarin tayaya zan iya zuwa wajen Ummi ba tare da J na kusa dani ba?”.

Numfashi mai zafi ya fesar da karfi kana yace.

“Baki É—aya rayuwa tayi min Æ™unci na rasa madafa, komai ya min duhu acikin duniyar nan na rasa yanda zanyi da kaina baki É—aya na rasa yanda zan fuskanci al'amarin”.

 

Ajiyar zuciya Asma'u ta sauƙe tare da fesar da nunfashi ta kallesa tare da faɗin.

“Ni dai Yah Moddibo mu tafi, idan har baka jeba Ummi na cikin tashin  hankali da damuwar rashinka, koda magana da Ummi ba tayi idan ba mun matsa mata ba amma sai ta zauna shiru ita kadai afalo baki É—aya gidan ya daina yi mana daÉ—i”.

Ahankali Moddibo ya taune Lip É—insa kana yace.

“Insha Allah zan zo ki cewa Ummi tayi haÆ™uri”.

Girgiza kai Asma'u tayi kana tace.

“A'a Yah Moddibo nidai gaskiya Ummi tace sai dai muje tare”.

Gyara zama Innayi tayi tare da fuskantar Moddibo cike da kulawa tace.

“Toh ka tashi kuje matuÆ™ar kana son farin ciki da kwanciyar hankalin Ummin ka, kada ka haÉ—a mata ciwo biyu Moddibo kasan rashin ka awajen Ummi babban matsala ne”.

Cikin sauri Asma'u tace.

“Wallahi kuwa Yah Moddibo baki daya Æ™uncin ya mana yawa, ba kai babu Yah Jameel. Baki É—aya zuciyarmu acunkushe yake da damuwa amma ganinka zai É—ebe mana kewa”.

Cikin sanyi da rarrashi Innayi tace.

“Ka daure kaje ko hankalinsu zai kwanta kuma kaima za kaji sauki  acikin ranka”.

Ta ida Maganar tare da miƙa masa key tsohuwar motar data fara saya mishi.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da karɓa kana ya miƙe cikin sanyi ya Murɗa handle din ƙofar

tare da fitowa wajen, cikin sauri ya lumshe idanunsa rabonsa da ganin haske irin haka ko kuma ya taka kofar falon yau tsawon kwana biyar kenan ko da sallah agida yake baya fita jam'i kai tsaye inda Motarsa yake ya nufa ya shiga sannan yaja  suka tafi.

 

Innayi kuwa na ganin tafiyarsu ta kira Number Malam ArÉ—o bayan ya É—aga tace.

“Dan Allah Malam ArÉ—o idan babu damuwa kazo ina da magana da kai”.

Kai ya gyaÉ—a kana yace.

“Toh badamuwa Insha Allah zan zo”.

 

Modibbo kuwa suna isa memory sa ya shiga tariyo masa hoton fuskar J É—in sa cikin sauri ya juya gefen damansa jin kamar sautin murya J É—insa cikin dariya yana cewa A.J tsayuwar me kakeyi Please kazo mu shiga inga Ummina kasan dai nayi missing dinta da yawa.

 afili ya furta.

“J kai ko nima ainayi kewarta kuma dan na tsaya jiranka ne da tuni na taho”.

Murmushi yaga M Jameel ya sakar masa sannan ya janye hannunsa daga cikin nasa ya juya ya fara tafiya yana jujjuya masa hannu alamar Byebye.

Da sauri Moddibo ya juya tare da cewa.

“J ina kuma zaka je ba kace ka matsu kaga Ummi ba?”.

Cikin sauri Asma'u dake Kallonsa ta tashare hawayen dake kwaranya a Idanunta kana tace.

“Yah Moddibo Yah Jameel fa baya nan sannan bazai taÉ“a zuwa inda muke ba”.

 

Moddibo kuwa ido ya tsirawa Asma'u kamar mai son fahimtar abinda take faÉ—a sai kuma yayi saurin dafe kansa tare da maimaita Kalmar Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n shi kansa yasan zuwa zuwa yanzu dai kamar zautacce yake.

Numfashin ya fesar sannan ya nufi falon bakinsa É—auke da Sallama Asma'u na biye dashi.

Ahankali idanunsa suka sauƙa akan Ummi dake zaune kan 3sitter ta daura guiwar hannunta duka biyu akan cinyarta tayi tagumi tare ta tsirawa waje ɗaya Ido baki ɗaya ta rame fuskarta yayi fayau.

Cikin sauri Moddibo ya ƙarasa shiga falon tare da zama agefenta kana ya janye tagumin da tayi ya maida hannunta kan gwiwoyinta.

 

Ummi kuwa cikin sauri ta sunkuyar da kanta nan take hawaye suka fara zuba Shar-shar-shar cikin sanyin murya ya kalleta kana yace.

“Ummi dan Allah kiyafemin. Insha Allahu bazan sake nesa dake ba, kinji Ummina ki daina zubar da hawayenki, dan baza mu iya juran. Kallon hawayen ki na zuba ba”.

Kallonsa Ummi tayi cikin wata raunan'niyar murya tace.

“Babana idan har baka zuwa wajena ya zanyi?Kana so ka haÉ—a min zafi biyu alokaci É—aya ne?

Babu Jameeluna sannan kaima baka kusa dani mekake tunanin zanji arayuwata, kana so inshiga wani hali ne?”.

Cikin sauri ya girgiza mata kai kana muryarsa na rawa yace.

“Insha Allahu bazan sake nesa da keba,  zan kasance atare daku tamkar yanda J ke kasancewa atare daku, zan sanya ku farin ciki tamkar yanda J É—ina ke saku insha Allah zan kiyaye”.

Ya kalli Ummi da har zuwa lokacin hawaye ke zuba a Idanunta ya É—aura tafin hannunsa akan nata cikin rawan murya yace.

“Insha Allah zan zame muku farin ciki kuma Garkuwa kamar yanda J É—ina ya kasance agareku Ummi. Asma'u Bashir Insha Allah bazan bari hawayenku ya zuba ba tamkar yanda J É—ina baya bari su zubo ba nayi al'Æ™awarin zan zame muku farin ciki zan maye muku gurbin J É—ina”.

Ya ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka kasa rarrashin sa Ummi tayi kawai itama hawaye ya cigaba da zuba daga idanunta haka Asma'u da Bashir suka riƙa kuka harda sheshsheƙa baki daya Moddibo baya jin zai iya hana kansa kuka bare kuma ya samu kuzarin rarrashinsu hakan yasa aka rasa wanda zai rarrashi wani acikinsu.

 

Malam Ahmad da dawowansa kenan ya zuba musu ido cike da tausayinsu ganin yanda suke kukan kasan daga ainihin zuciyarsu yake fitowa.

Cikin sanyi malam Ahmad ya zauna gefen Ummi ya zamana yana fuskantar Moddibo, Asma'u da Bashir dake ƙasa cike da tausayawa da kuma rinƙa rarrashisu da basu baki.

 

Ahankali Ummi ta maida bayanta da jikin kushin É—in ta jingina hawaye na cigaba da zubo mata Moddibo kuwa kasa yayi da kansa yana jin wani irin yanayi azuciyarsa shikenan J ya tafi ya barsa bari na har abada.

Kallonsu Malam Ahmad yayi kana ya cigaba da cewa.

“Insha Allahu da yardan Ubangiji Jameelu yana cikin rahama, salama nutsuwa da kwanciyar hankali domin Jameelu ya kasance bawa mai tsananin Biyayya ga dokokin ubangiji sannan Jameelu yaro ne me biyayya ga Iyayensa akullum burinsa yaga ya sanya Iyayensa da shalinsa acikin farin ciki”.

 

Jinjina kai sukayi Atare cike da gamsuwa da maganarsa tabbas ta ko wanni fanni Jameel bashi da makusa.

Ajiyar zuciya Malam Ahmad ya sauƙe kana yace.

“Jameel ya kasance mutum mai tsananin tausayi da temakon al'umma Jameel baya taÉ“a kallon mutum acikin halin neman temako sannan ya wuce batare daya temakesa ba, duk wanda yasan Jameel da addu'a yake binsa na Ubangiji ya jiÆ™ansa dama mutane masu Kirki da karamci Ubangiji bai fiye barinsu tagayyaraba sam Jameelu bai cancanci kuka agare kuba, addu'a ya cancanci ku masa domin da izinin Ubangiji yana can cikin rahmar Allah da yardan sa”.

 

Kai Bashir ya gyaÉ—a tare da share hawayen saman fuskarsa kana cikin sauri yace.

“Hakane ma Abba abinda kake faÉ—a yanzu shine abinda.

 Yah Jameel ya faÉ—a min acikin Mafarkina jiya da daddare yace. in faÉ—awa Ummi ta daina yi masa kuka domin duniyar da yake ayanzu tafi wannan duniyar da muke ciki daÉ—i, nutsuwa, salama, da kuma aminci”.

Cikin sharce hawaye ya gyara zamansa tare da fuskantar Ummi kana yace.

“Sannan yace bayason wannan kukan da Ummi ke masa, shikam addu'a yake buÆ™ata duk wannan koke koken bayaso adaina yi masa.”

Kallonsa ya mayar kan Moddibo tare da cewa.

“Sannan kaima Yah Moddibo acikin mafarkin da nayi da Yah Jameel yace in FaÉ—a maka ka cigaba da yimasa addu'a sannan kayi Æ™oÆ™ari ka cika masa wasiyyar da yayi maka ta gefen Innayi ya jadda min kuma ka taya Abbansa kula da lamuran kasuwancinsa”.

Saurin É—ago kai Moddibo yayi tare da cewa.

“Ummi wani wasiyya kuma J É—ina ya bari akaina??”.

Girgiza kai Ummi tayi tare da fashewa da matsanancin kuka batare da tace Uffan ba.

 

Ajiyar zuciya Malam Ahmad ya sauƙe tare da kallon Ummi dake sheshsheƙa kana yace.

“Fatima yanzu kuka za kiyiwa Jameelu? shin kinsan Rahman da Ubangiji ya tanadar wa da duk wa'anda aka zalunta da rabasu da rayuwarsu?

Kada fa ki manta Ubangiji ya tana dar da rahma wa duk rayukan da aka kashe batare da hakkinsa ba”.

 

Ahankali Ummi ta É—ago kanta kana ta sanya tafin hannunta ta share hawayen ta Numfashi malam Ahmad ya fesar kana yace.

“ki tuna ni'imomin da Allah yayiwa muminai tanadin su.”

Lokaci É—aya Ummi ta saki murmushi wanda tun bayan sace M Jameel ba tayi irinsa ba wani irin nutsuwa da salama taji yashigeta lokaci É—aya tabbas tana ji ajikinta Jameelun ta na cikin rahmar Ubangiji.

 

Moddibo ma murmushi yayi wanda ya fito daga ainihin zuciyarsa in sha Allah J dinsa yana cikin kwanciyar hankali da salama da izinin Ubangiji addu'a kawai J dinsa ke buƙata atare dashi Insha Allah kuwa zai cigaba da masa hakan yasa suka cigaba da hirar rahmar da M Jameel zai kasance da izinin Ubangiji cikin sakin fuska suka cigaba da hira.

 

Acan gidan Lamiɗo kuwa ƙarfe biyar dai-dai Hajja Nana ta mike tare da kallon Dije dake zaune gefen Khausar suna hira tace.

“Ke Dije tashi mu tafi”.

Kai Dije ta gyaɗa tare da miƙewa cike da girmamawa Mommy ta haɗa mata tsaraba sannan ta bawa Khausar ta riƙe suka fito.

Suna fita coumpund É—in Hajja Nana ta kalli Khausar tare da cewa.

“Insha Allah idan Baffa Jimeta yazo zamu zo tare”.

Ko uffan Khausar bata ce da ita ba haka zalika Mommy, bayan Khausar sun koma falon ta kalli Mommy cikin sanyin murya tace.

“Mommy yanzu dan Allah biye mata zakiyi?”.

Ahankali Mommy ta zauna tare da kallon Khausar cikin sanyi tace.

“Yanzu Khausar idan ban biye mataba wa kika tsayar?  sannan tsohuwar nan tunda ta rantse akan dole sai anmiki aure tofa babu makawa, sannan babu yanda zanyi dole sai an Aurar dake ke dai kiyi fatan Allah ya miki zaÉ“in alkhairi, sannan ya baki mijin da zai barki ki cigaba da karatunki ki kuma cika burin ki”.

Wani abu mai masifar É—aci Khausar ta haÉ—iye cikin raunin murya tace.

“Mommy nifa Banason sa”.

Kallonta Mommy tayi kana cikin tsareta da ido tace.

“To idan bakya sonsa wakike dashi ko kuma wa kika tsayar babu wani saurayi dake zuwa wajenki Naseer da ake maganar sa yanzu ya fita sabgarki kuma hakama yafi min.

 Ni yanzu abinda na fahimta ma kamar soyayya suke da Amina”.

Khausar kuwa kallon Mommy tayi tare da tura baki kana tace.

“Eh Mommy soyayya suke to amma.

Ni me ruwana dasu ni dai bazan Auri Yah Aliyu ba Naseer kuwa bana sauraron maganarsa bare insa shi araina”.

 

Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da gyara zaman ta cikin sanyin murya tace.

“Toh Allah ya mana zaÉ“in alkhairi”.

ta faɗa tare da miƙewa tashiga Bedroom ɗin ta Khausar kuwa jingina bayanta da jikin kushin tayi tare da lumshe Idanunta.

 

Da yammaci Misalin ƙarfe biyar da rabi Hajiya Bunayya da Hajiya Lami ce zaune agaban Boka Kar'uzu.

Cikin farin ciki Hajiya Lami ta gyara zamanta tare da kallon Boka Kar'uzu dake taune laɓɓansa na ƙasa duk yayi muni ba kyan gani cikin sassauta murya tace.

“Na gaishe ka Boka Kar'uzu Uban bokaye La'anannen Uban La'anannu ina mai farin cikin sanar da kai shekaran jiya Alhj ya tafi Saudia kaga yanzu sai ka shirya ka koma gidana kaje kayi sati ba matsala”.

Wata mahaukaciyar dariya Boka Kar'uzu ya fashe dashi wanda yasa ganyen bishiyar dake wajen suka soma zubowa yana mai ƙara wangale wawakeken bakinsa yace.

“Anjima da daddare zanzo, maza ku tashi ku tafi da Æ™afar hagu yanzu zanyi manyan baÆ™i da kukar bulikiya ÆŠan JaÆ™unana mai Æ™aho Atsakiyar kai da da jela zai Æ™araso”.

Ai cikin sauri suka miƙe suka fita daga wajen kamar yanda ya faɗa.

 

Acan gidan Innayi kuwa zaune suke da Malam ArÉ—o asaman baranda Moddibo.

Cikin nitsuwa Innayi ta kalli Malam ArÉ—o cikin sanyin murya tace.

“Toh kaji yanda mukayi dashi, yanzu abinda nake so idan Allah ya nufa zaka je kasamu Abban Jameelu kayi masa bayani idan yaso sai mu isar da manufarmu ga mahaifin yarinyar”.

Jinina kai Malam Arɗo yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya kana yace.

“Insha Allahu idan Allah ya yarda zan shiga wannan maganar da iyakacin Æ™arfina zan shigeta da izinin Ubangiji”.

Kai Innayi ta jinjina tare da cewa.

“Toh ba matsala Insha Allah Nagode matuka”.

 

Acan gidan Ummi kuwa bayan fitar Malam Ahmad Moddibo ya kalli Ummi cikin sanyin murya da damuwa yace.

“Ummi nayi al'Æ™awari da izinin Ubangiji da yardan Allah sainayi duk yanda zanyi sai an gano waÉ—anda sukayi mana wannan cuta.

“Domin duniya tasan irin baÆ™in zunubin da suka aikata, sannan akamasu ayi musu hukunci dai-dai da zunubinsu, domin wasu su tsira agaba kada su sake cutar da wasu  kamar yanda suka cutar damu, da zukatanmu da kuma ahalinmu”.

Numfashi Ummi ta fesar tare da sauƙe ajiyar zuciya kana tace.

“Hummmm?".

Cikin sauÆ™e numfashi Asma'u tace. 

“Toh ammn ta ina zamu fara  Yah Modibbo!?”.

Ahankali Ummi ta kalleta kana ta kalli Moddibo ta sauke ajiyar zuciya mai sanyi tace.

“Nima abinda nake tunani kenan, ta ina zaku fara wannan ba Æ™aramin case bane dole yakasance mutum nada Æ™wararan hujjoji kafin ya tun kari lamarin mu kuma bamu da sahihiyar Hujja dan haka mu barwa Allah lamarinsa”.

Jinjina kai Asma'u tayi tare da gyara zaman ta tace.

“Makama É—aya muke da shi batun Khausar”

 

Cikin zurfafa nazari Moddibo yace.

“Kin tabbata Asma'u zata bamu haske kan batun?”.

Kai ta gyaÉ—a masa kana cikin gaskiya da gaskiya tace.

“Na tabbatar Yah Moddibo”.

Kallon Ummi dake Kallonsu yayi kana cikin ƙarfin gwiwa yace.

“Ummi”.

Cikin sanyi da tausayinsa tace.

“Na'am Babana”.

Cikin alamun samun nasara da jin daÉ—i yace.

“Ummi zamu fara bincike”.

Kai Ummi ta gyaÉ—a kana cikin wani irin yanayi tace.

“Nikam ina tsoro Babana ina tsoron kada kaima Azo acutar mana da kai ina tsoro kada wani abu ya sameka kawai abar maganar nan”.

Cike da mamaki da kuma sanyi Moddibo yace.

“Ummi tayaya”.

Girgiza kai Ummi tayi kana tace.

“Babana Abar Maganar kawai”.

Kai ya gyaÉ—a mata sannan suka dauka wani hiran sosai kowannen su ya samu nutsuwa sosai sukaji damuwar suya fara raguwa kaÉ—an sai bayan da Moddibo yayi sallar maghariba kafin yayiwa Ummi Sallama ya tafi.

 

Bayan Sallar Isha'i Malam ArÉ—o ne zaune gaban Abba wanda baki É—aya ya rame yayi wani iri dashi.

Kallonsa Malam ArÉ—o yayi kana yace.

“Toh Alh kaji yanda akayi kuma shine abinda ya  kawo ni”.

Jinjina kai Abba yayi cikin yanayin sanyinsa yace.

“Nima nasani Jameelu ya faÉ—a min”.

Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe tare da faɗin.

“Masha Allah abu yazo da sauÆ™i kenan”.

Jinjina kai Abba yayi kana cikin sanyi yace.

“Ba matsala Insha Allah zuwa jibi zamuyi kokari muyi maganar”.

Kai Malam ArÉ—o ya gyaÉ—a tare da cewa.

“Ayyah Jameelu Insha Allah zamu cika masa burinsa tunda har yayiwa Amininsa zaÉ“in mata yayi fatan ya haÉ—a wannan Auren kafin ya tafi zamu cika masa burinsa da izinin Ubangiji zamuyi Æ™oÆ™arin cika wasiyyar daya bar mana”.

Kai Abba ya gyaÉ—a cikin sanyi ya gyara zamansa tare da lumshe idanunsa kana yace.

“Insha Allah zan tsaya akan lamarin sannan zanyi iyakacin bakin Æ™oÆ™arina ganin ancika masa duk kan wasiyyar daya bari”.

Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe tare da jinjina kai yace.

“Insha Allah babu damuwa idan Allah yakai mu jibin zanzo ba matsala”.

Godiya Abba ya masa sannan Malam ArÉ—o ya masa Sallama ya tafi.

 

Bayan kwana biyu: Moddibo ya fito daga gida jikinsa sanye da Gezner fari soll yayin da kansa ke sanye da hula tangaran baƙa yalwataccen sumar kansa irin na Fulanin Usul yana kwance aƙeyarsa fuskarsa tayi fayau manyan Idanunsa na lumshe yayinda jikinsa ke fitar da sanyayyan ƙamshin tularen Oud Khareem kai tsaye gidan Ummi ya nufa bakinsa ɗauke da sallama ya shiga coumpund ɗin Abaranda ya hango Asma'u na Morping Jin ƙaran buɗe ƙofa yasa Asma'u ta juya ganin Moddibo yasa tace.

“Yah Moddibo sannu da zuwa ka iso mana”.

Ahankali ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.

“Ummin fa naji gidan shiru?”.

Tana matse mopan dake hannunta tace.

“Bata nan”.

Kai ya gyaÉ—a tare da faÉ—in.

“Ke kaÉ—ai ce agida?”.

Girgiza kai tayi kana tace.

“A'a Bashir na ciki?”.

Kai ya gyaÉ—a tare da gyara zaman hular dake kansa kana yace.

“Ina Ummi taje?”.

Ahankali ta jinginar da Moper kana tace.

“Ummi ta tafi asibiti saboda kwanan nan ciwon kai yana yawan damunta taje adubuta”.

 

Cike da kulawa da kuma sanyi yace.

“Subhanallah toh Allah ya sawwaÆ™e”.

Ahankali Asma'u tace.

“Ameen”.

Moddibo kuwa gyara tsayuwar sa yayi cike da nutsuwa da kuma sanyi yace.

“Asma'u zo muje ki rakani gidansu.

 Khausar akwai tambayoyin da nake so nayi mata”.

Kai Asma'u ta gyaÉ—a cike da jin daÉ—in hukuncin da yake son É—auka tace.

“Toh Shikenan Yah Moddibo bari in kira Ummi in FaÉ—a mata”.

Cikin sauri ya girgiza mata kai kana yayi ƙasa da muryarsa yace.

“A'a kada ki faÉ—awa Ummi,  zata hana mu binciken idan kika faÉ—a mata zata hana amma yanzu kiyi sauri muje kafin ta dawo yanzu zamu dawo”.

 

Jinjina kai tayi tare da faÉ—in.

“Toh shikenan”,Sannan tashiga ta dauki Maroon hijabinta har Æ™asa kana ta kalli Bashir dake karatun wani littafi na addini tace.

“Bari muje gidan su Khausar nida Yah Moddibo”.

Ta Ida maganar tare da fitowa.

 

Miƙewa Bashir yayi tare da fita kana yace.

“Laa Yah Moddibo Sannu da zuwa”.

Kai Moddibo ya gyaÉ—a kana yace.

“Yawwa Bashir koda Ummi ta dawo kada ka faÉ—a mata can mukaje kace gidan Innayi muka je”.

Ahankali Bashir ya gyaÉ—a masa kai kana yace.

“Toh shikenan Yah Moddibo sai kun dawo”.

Suna fita suka shiga mota kana Moddibo yaja  suka tafi.

 

Acan gidan Lamiɗo kuwa cikin sauri Khausar ta fita daga side dinsu ta nufi sashen Gimbiya Bunayya tun kafin ta ƙarasa shiga tace.

“Ummah!, Ummah!!Ummah!!!”.

Daga ciki Hajiya Bunayya tace.

“Na'am”.

Khausar na karasa shiga tace.

“Ummah Raudat tashigo?”.

Kai Hajiya Bunayya ta gyaÉ—a kana tace.

“Eh tashigo”.

Ƙarasa shiga Khausar tayi tare da Hararan Raudat dake ɓuya tace.

“Raudat kizo muje in miki wanka amma sai wani bauÉ—ewa kikeyi tun É—azu kina ta gudu”.

Maƙale ka faɗa Raudat tayi tare da tura ƙaramin bakinta tace.

“Ni dai na faÉ—a miki bana son wankan nan akwai sanyi”.

Cikin rarrashi Khausar tace.

“To ai da ruwan É—umi zan miki”.

Girgiza kai Raudat tayi tare da tura bakinta tace.

“Ni dai Banason gaskiya”.

Ganin tana son ɓata mata lokaci yasa Khausar ta shiga tare da janyo hannunta tace.

“Maza wuce muje in miki  zan baki waya kafin fito kiyi game”.

Bubbuga kafa Raudat tayi cike da Shagwaɓa tace.

“Addah Khausi Ni dai ki Æ™yaleni bana so”.

 

Ahankali Khausar tayi ƙasa da muryanta tace.

“Harda Game É—in bakya so?”.

Ware Ido Raudat tayi tare da ƙyalƙyala dariya kana tace.

“Allah dagaske Addah Khausi zaki bani?”.

Murmushi Khausar tayi tare da lakace mata hanci tace.

“Eh”.

Suna shiga Bedroom É—in Raudat ta zauna gefen gado sannan Khausar ta mika mata wayar bayan tasa mata game É—in _Subway surf_ ta bata murmushi Raudat tayi kana ta fara buga game É—in.

Khausar kuwa dogon rigar jikinta ta cire tare da ɗaura towel iya ƙugunta ta shiga toilet.

 

Akuma dai-dai lokacin Moddibo yayi Parking afarfajiyar gida dai dai nan Lamiɗo ya fito da motarsa ganin Moddibon yasa Lamiɗo yayi Parking din motarsa ya fito cikin sauri Moddibo ya ƙarasa kusa dashi tare da basa hannu sukayi Musabaha cike da kulawa Lamiɗo yace.

“Moddibo bar kadai ya gida ya kuma Ƙarin haÆ™urin rashin Jameelu?”.

Cikin sanyin Murya Moddibo yace.

“Alhamdulillah hakuri mungode Allah”.

Cike da kulawa LamiÉ—o yace.

“Allah ya gafarta masa ayi ya masa addu'a”.

Cikin sanyin yace.

“Ameen Mai Martaba Nagode.

 dama munzo wajen Khausar ce”.

Cike da kulawa LamiÉ—o yace.

“Toh ba matsala Asma'u ku isa”.

Ahankali Moddibo yayi ƙasa da kansa tare da cewa.

“A mai Martaba baza'a a bari daga nan ba”.

Girgiza kai LamiÉ—o yayi  kana yace.

“Ku shiga ba matsala bari na kira Aysha in FaÉ—a mata”.

Hannu ya sanya a aljihunsa tare da ciro wayarsa yayi dearling number Mommy tana É—agawa yace.

“Aysha ga baÆ™i Moddibo da Asma'u zasu shigo”.

Cike da kulawa Mommy tace.

“Toh ba damuwa su shigo mana”.

Katse wayar LamiÉ—o yayi tare da yi musu Sallama kana ya shiga motarsa ya fita.

Moddibo da Asma'u kuwa suka nufi sashen Mommy suna isa bakin barandar Moddibo ya tsaya Asma'u ta ƙarasa shiga falon tare da cewa.

“Assalamu Alaikum”.

Shiru falon ba Kowa sai dai ko ina tsaf-tsaf kana ga ƙamshin dake tashi. Ajiyar zuciya Asma'u ta sauƙe tare da nufar Bedroom din Mommy tana cewa.

“Mommy!, Ta Æ™arasa tare da shiga Bedroom din Mommy dake sanye da hijabi tace.

“Asma'u kun Æ™ara so Ina Moddibo?”.

Kai Asma'u ta gyaÉ—a tare da cewa.

“Eh amma yana waje”.

Mommy na zama gefen gado tace.

“Toh kice masa yashigo mana ya zaki barshi atsaye”.

Kai Asma'u ta gyaÉ—a tare da cewa.

“Toh Mommy”.

Sannan ta juya tare da fita falon ta leƙa ƙofan Falon cikin sanyin Murya tace.

“Yah Moddibo wai kashigo”.

Ahankali ya É—ago kansa tare da buÉ—e Idanunsa dake lumshe yace.

“Toh”.

Sannan ya shiga falon da komai ke kintse yana fitar da sanyayyan ƙamshin ahankali ya zauna akan 1sitter dake fuskantar ƙofar Bedroom din Khausar.

 

Asma'u kuwa juyawa tayi tare da kallon Moddibo kana tace.

“Yah Moddibo bari in sanarwa Mommy ka Æ™ara so”.

Bata jira amsar saba ta nufi Bedroom É—in Mommy.

 

Khausar kuwa ahankali ta fito daga toilet tare da juya kanta yalwataccen sumar kanta dake jiƙe ya mannu da wuyanta da kuma gefen fuskarta dake da damshin ruwa fararen cinyoyinta masu haske da santsi na ɗauke da damshin ruwa.

Ware Ido Raudat dake Game tayi  tare da kife wayarta akan gadon kana ta dira tare da ficewa da gudu saida ta isa kofar Bedroom din kafin ta tsaya.

Cike da mamaki Khausar ke kallonta kana tana tafiya ahankali tace.

“Raudat ina kuma zaki je?”.

Tura baki Raudat tayi tare da juya Idanunta tace.

“A ni dai Banason wankan nan da kwai sanyi”.

Sake baki Khausar tayi wato ita Raudat zata yiwa wayau, ɓata fuska tayi tare da cewa.

“Aikuwa baki isa ba kisa in. Baki wayata kiyi game sannan yanzu kinga na fito kice zaki gudu”.

Gwalo Raudat ta mata tare da fita da gudu.

 Ware ido Khausar tayi tare da bin bayanta da gudu dariya Raudat ta Æ™yalÆ™yale dashi tare da nufar hanyar fita sai kuma ta karya kwana ta nufi Bedroom É—in Mommy.

Khausar kuwa garin zata karya kwana ta nufi Bedroom din Mommy santsin ruwan dake ƙafarta da kuma santsin tlyes ya jata tayi baya Suuuuuu ta faɗi a ƙasa kana towel ɗinta ya since ya zame yayi ƙ...!

 

 

No comments