Breaking News

Sakayyah Book 2 Page 7

 

                         By


      *GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2 page 7*

          Na

*Aysha Aliyu Garkuwa*

 

Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha'awa. ƘaiÆ™ayin gaba Kiji idan ya fara miki Æ™aiÆ™ayi kamar zakiyi hauka. Warin ko Æ™arnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su É—an fetso Æ™ananan ko Æ´an manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni'ima. BuÉ—ewar gaba, domin har budurwa infection na iya buÉ—ata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al'ada, rashin haihuwa, domin har baÆ™in mahaifa take toshewa. Ko kirinÆ™ajin wani abu na miki yawo Æ™asan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban  lissafa. Sune manyan alamomin infection.

Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.

Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni'ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya Zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.

KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe Æ™yamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni'imomin ki, da sha'awarki, duk kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji Æ´an uwa da abokan arziÆ™i da Æ™awayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA'AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau,  duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha'awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor's suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic infection ne yar uwa.

INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi'izinillahi ta'ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma'ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya'ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER'N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA'AURATA.

 

 

 

Khausar kuwa cikin sanyi da rauni tunowa da M Jameel da ya dawo mata sabo ahankali ta kife kanta abakin gado tafashe da kuka mai cike da fargaba da kuma tsoron Allah.

Kallonta Mommy tayi cike da tausayawa tace.

“Kiyi haÆ™uri ki daina kuka Khausar addu'a zaki yiwa  Jameelu sannan Insha Allah za acika masa burinsa da wasiyyar daya bari in Allah ya ya nufa”.

Ta ƙare mgnar tare da sauƙe numfashi.

 Idanta ta tsaida kan Khausar da har zuwa lokacin kanta ke kife jikin gado cikin tausasawa tace.

“Amma kisa Aranki cewa haÆ™uri zakiyi da duk rayuwar da zakije ki tarar, sannan wasiyya zaki cikawa Jameel, sannan ki sani shi zaman Aure kansa Ibada ne, koda ana son juna wata ran akanji babu daÉ—i, bare ke da dama kin san matsayinki a wurin wanda kike ganin kina da Æ™arfin guiwar zama dashi,

  dan haka kisa Aranki cewa ba lallai ne kiji daÉ—in zama da Moddibo ba, amma tunda kince kinji kin gani zakiyi abinda Jameel ya buÆ™ata kafin barinsa duniya zan biki da addu'a Ubangij ya tabbatar da al'khairi tunda har iyayensa duk ya gayawa kuma tuni suma sun sa baki a mgnar, kinga ni bani data cewa tunda kun mamayeni”.

Cikin rauni Khausar ta sake fashewa da sabon kuka tabbas gaskiya Mommy ta faɗa ba Lallai tayi zaman daɗi da Moddibo ba tunda baya sonta hasalima koda kallonta ne baya sonyi tuno da hakan yasa wasu hawaye masu masifar zafi suka zubo mata tama sani tabbas cikin uƙuba zata rayu dashi, to amman ya zatayi rayuwa Yah Jameel al'ƙawarin amincewa da batun auren Amininsa.

 

Cikin sanyin murya Mommy ta cigaba da cewa.

“Sanin bake kaÉ—ai Jameelu ya barwa wasiyya ba yasanarwa da Kakar Moddibo sannan ya sanarwa Umminsa da kuma Abbansa nima da farko hankalina ya tashi.

Amma yanzu barina É—akin Abbanku yake cemin shekaran jiya da daddare Abban Jameel da Malam Ahmad da malam ArÉ—o sunzo da batun, abinda yasa baiyi mgnar ba Hajja Nana bata bashi dama bane daya mata bayani”.

Wani irin rauni, Kunya,damuwa da rasuwar Jameel ne suka dawowa Khausar alokaci É—aya.

Cikin sanyi jiki ta miƙe ta nufi ɗakinta tana shiga ta faɗa kan gadonta kana ta cigaba da kuka cikin rauni tasan dai iyaye keyiwa ƴaƴansu auren dole a tarihin duniya, sai gashi ita dai itace zatayiwa kanta da kanta auren dole bisa wasiyar Yan Jameel malami na musamman mai matsayin babban Yaya wanda ita dai da fari har ranta shi takeyiwa kallon mai iya jiɓantan lamuranta.

 

Washe gari da safe Misalin ƙarfe 8:00 Anutse Moddibo ya fito daga falonsa cikin wani ɗanyen Boyel Sky blue Fuskarsa tayi fayau manyan Idanunsa dake lumshe sun sake girma sabida ramar da yayi, sajensa ya sake yawaita yayi fadi da cika, yana kuma ɗan hargitse alamun an kwana biyu ba'a gyarashi.

Kafadarsa na dama rataye da jakar laptop ɗinsa daga zip ɗin gefen wayoyinsa ya zira, sai hannunsa dake riƙe da jakar kayansa, a hankali yake tafiya, yayinda jikinsa ke fitar da sanyayyan ƙamshin tularen sa.

Kai tsaye sashen Innayi ya nufa ahankali Innayi dake breakfast ta ɗago Kai ta kallesa Anutse ya ƙarasa tare da zama gefenta.

Da mamaki take Kallonsa ganin kamar alamar cikin shirin tafiya yake.

Cikin sauri tace.

“Aliyu”.

Kallonta yayi da sauri domin bata fiye kiransa da Aliyu ba sai da babban dalili.

Cikin sanyin murya yace.

“Na'am Innayi”.

Hannunta riƙe da kofin tea tace.

“Ya haka? ya na ganka kamar mai yin tafiya?”.

Kai ya gyaɗa mata tare da tanƙwashe ƙafafunsa kana ya fuskanceta cikin ƙoƙarin danne damuwarsa kana yana mai jin farin cikin zai bar garin Gembila haka nan ya tsinci kansa da jin farin cikin yau dai zai bar Jahar Taraba domin baki ɗaya garin ya fice masa arai cikin sanyin murya yace.

“Innayi ba kama bace tafiyar ce”.

Cike da mamaki ta É—ago kanta kana tace.

“Aliyu tafiya zaka yi amma ban sani ba sai dai in ganka kana fita da jaka haka?”.

Ahankali ya riƙo tafin hannunta acikin nasa cike da mmkia yace.

“Kiyi haÆ™uri Innayi tafiyar ce nima tazo min a bazata kuma  ba jiya Abban Jameel ya gaya mikiba”.

 

Kai ta girgirza tare da cewa.

“A'a bai gaya minba zakayi tafiya ba, ya dai cemin yana neman al'farma ni kuwa nace umurni kawai zai baka kamar yadda yake bawa Jameel ni na amince duniya da Æ™iyama, ban bari yamin bayaniba sabida kar yaga kamar zan hanaÆ™a yaji ba daÉ—i. To waima Tafiya zuwa ina zakaje?”.

Cikin kwantar da murya yace.

“Tafiya zuwa Marocco!”.

Cikin tsananin kaÉ—uwa ta zaro idanunta baki É—aya lokacin É—aya ta Æ™ware tare da fara tari sakamakon Æ™warewa da tayi da dankalin dake bakinta”

Moddibo kuwa ganin yanda ta ƙware yasa yayi saurin daukan kofin ruwa ya miƙa mata tare da cewa.

“Sannu”.

Amsa tayi tasha amma still tarin bai tsaya ba lokaci ɗaya Idanunta yayi ja zufa ya shiga tsats-tsafo mata agaba ɗaya ilahirin jikinta shi kuwa Modibbo ido ya zuba mata tare da jera mata sannu da kuma ɗan bubbuga bayanta kaɗan-kaɗan yana mmkin wasu al'amuran a ranta domin ya sani tsawon zamansu da J ta hanashi zuwa Marocco wanda bai san me dalilntaba, kasancewar sa ba mutum ne mai yawan bincikeba yasa bai taɓa mata musuba ko bincike.

Ahankali ya ke mata sannu cike da tausayawa takai kimanin minti biyar kafin tarin ya lafa sannu Ahankali ta fara maida numfashi.

 

Tana sauƙe ajiyar zuciya ta juya ta kallesa kana tace.

“Marocco!!!! kuma Aliyu?”.

Jinjina kai yayi cikin sanyin murya yace.

“Eh Innayi Marocco zanje amma idan har kin amince, idan bakya so, bazanje ba sai in bawa Abba haÆ™uri”.

Ahankali ta gyara zama tare da fuskantar sa da kyau kana tace.

“Toh amma mai zakaje kayi a can?”.

Tayi tambayar zuciyarta na mai cigaba da bugawa da ƙarfi.

Lumshe Idanunsa yayi tare da sauƙe Ajiyar zuciya kana yace.

“Abba ne ya nemi al'farma da Inje in kula da Company'nsa sannan kuma jiya daya zo nayi tunanin kunyi cikekkiyar maganar ne dashi kafin ku shiga wurina, shiyasa ni ban faÉ—a miki ba, ya nemi taimako da Inje in taimaka masa akan batun Company sa buga Abaya, jallabiya, Carpet, Sallayu blanket's da dai sauransu”.

Kallonsa kawai Innayi keyi yayin da take ji tamkar zuciyarta zai fito saboda yanda yake bugawa.

Cikin sanyi Moddibo ya riƙe Hannunta dake cikin nasa yace.

“Akwai sabbin injinan aiki da za'a sauÆ™e na Company,  sannan kuma za'a fara aikin dasa Injina  za'a kakkafa toh akwai É“uÆ™atar sa ido da kuma kula da abubuwan,  amma Insha Allah bazan wuce wata biyu zuwa uku ba zan zo Innayi”.

 

Girgiza kai tayi tare da jingina bayanta da jikin bango ta lumshe Idanunta kana ta shiga maida numfashi.

 

Moddibo kuwa ido ya zuba mata kana Asanyaye yace.

“Amma Innayi idan har bakyason Inje zan kira Abba in FaÉ—a masa yayi haÆ™uri”.

Uffan bata ceba kana bata buÉ—e Idanunta ba daga ita sai Ubangiji kaÉ—ai suka san mai take tunawa aranta takai kimanin minti biyar ahaka kafin ta É—ago Idanunta ta kallesa kana taja dogon numfashi ta sauÆ™e tare  da sakin Murmushin mai tarin ma'anoni  sannan tace.

“Bazan hanaka tafiya ba Aliyu, domin ko baka tafi yanzu ba, dama lokacin tafiyar ya Æ™arato. na amince kayi masa duk kan abinda Jameelu zai masa daya kasance araye, domin hakan zai rage masa raÉ—aÉ—in ciwon rashin Jameelu”.

Kai Modibbo ya gyaÉ—a yana kallon yanayin fuskartar ahankali yace.

“Toh shikenan Insha Allah zanyi hakan”.

 

Innayi kuwa kallonsa tayi kana cikin sanyin murya tace.

“Amma yanzu-yanzu tafiyar kenan Aliyu?”.

Kai ya gyaÉ—a kana yace.

“Eh Innayi zanbi jirgi zuwa Abuja ne, in naga komai biza na ya fito zan wuce”.

Jinjina kai tayi tare da cewa.

“Shikenan Ubangiji Allah ya sanya alkhairi Allah ya tabbatar da alkhairi sai nazo”.

Saurin Kallonta yayi cike da Mamaki yace.

“Sai kinzo kuma?”.

Sunkuyar da kanta ƙasa tayi tare da Girgiza masa kai kana tace.

“Mantawa nayi sai ka dawo nake son cewa".

A hankali ya zaro ATM É—inshi na Zenith Bank daga al'jihunsa,  cikin tafin Hannun ta yasa matashi kana a hankali yace.

“Ga ATM É—ina na Zenith Bank, kin san pin number É—in, akwai kuÉ—i a ciki kusan 5 Million”.

Da sauri tace.

“Ina ka samosu?”.

Gyara zamanshi yayi kana yayi mata bayanin yadda sukayi da Abba sannan ya É—aura da cewa.

“Akwai wasu a wurina, wannan ki riÆ™e kiyi dukkan abinda kike buÆ™ata kafin in dawo, in haÉ—asu muyi Æ™oÆ™arin barin garin nan, domin ya fita raina”.

Yayi mgnar yana tuno kalaman Hajja Nana ita kuwa Innayi cike da sanyi tace.

“Uhmmm Aliyu in Sha Allah kamar ma mun barima ai kama barin kai kam”.

Cikin sanyi ya jinjina

Kai tare da miƙewa yace.

“Toh shikenan Innayi amma dai bakiyi fushi dani bako?”.

Da sauri tace.

“La la la Aliyu banyi fushi da kaiba”.

hannunta ya riƙo tare da ɗaurawa a kanshi kana yace.

“Toh kuma baki samin Albarka ba”.

Cikin sanyin Murya tace.

“Allah yasan ya Albarka Ubangiji ya tsare gabanka da bayanka Allah maidakai lafiya ya kuma tsareka da lafiyarka, Ubangiji ya rabaka da sharrin duk kan abin Æ™i walau mutum ko aljan ko  wani irin abune ya *Tsareka da Tsoffin magauta ya hanasu ganeka bare cutar da kai kafin isarka tushenka”.*

Lumshe Idanunsa yayi kana yace.

“Ameen ya Allah Innayi ni zan tafi”.

Kai ta gyaÉ—a tare da cewa.

“Toh ka tsaya bari na zo".

Kai ya gyaÉ—a sannan ya tsaya É—aki tashiga ba daÉ—ewa ta fito sanye da hijabi, suka nufi  wurin motarsa,

“Yau innayi zafa ki koma gidan Abba ko Ummi dan zamani ke É—aya a nan bai minba”.

Cikin sauri tace.

“Eh toh gsky k nima ina tsoro Ni kaÉ—ai a nan to amman, gsky gwara min gidan Ummin Jameel kaga ita kamar É—iya take a gareni gidan Abba kuwa ba wani sabawa nayi da matansa ba, amman can zamu zauna É—akin Asma'u nasam Malam Ahmad kuma baida matsala”.

Cikin gamsuwa da haka yace.

“Gsky kam hakan yafi, zan gaya Abban in kin gama haÉ—a kayanki Asma'u zata zo ku tafi”.

Kai ta jinjina cikin gamsuwa tace.

“Ba laifi”.

Jingina yayi da jikin motar bayan yasa jakarsa gefen mai zaman banza.

Ita kuwa Innayi a hankali ta matso kusa da marfin motar zira hannunta tayi ta ciki, zip É—in jakarsa tabuÉ—e tasa jim kaÉ—an kuma ta maida ta rufe kana sukayi sallama ya mota ya tafi.

 

Kai tsaye gidan Ummi Moddibo ya nufa cikin nutsuwa yake Driving yayin da yake sauraran ƙira'ar Ahmad Sulaiman cikin suratul An'am yana isa gidan Ummi yayi Parking aƙofar kana ya fita ya shiga coumpund ɗin yana tafiya ahankali yana ɗaura ƙafarsa akan farandar sautin muryar Khausar ya ratsa Dodon Kukensa cikin sauri ya tsaya tare da rumtse idanunsa.

Sabida jin yadda tsikar jikinsa ya fara tashi tun daga tafin ƙafarsa har tsakiyar ƙwaƙwalwan kansa, ahankali ya jingina bayan sa da jikin bango yayin da zuciyarsa ta shiga bugawa da kaso Cassa'in da tara cikin ɗari.

 Aransa yakeji kamar ya koma domin gaba É—aya ya rasa meke sashi shiga wani yanayi da zaran yaji sautin Muryanta zaiji tamkar ana tsikara masa allura yama rasa ta wani irin yanayi zai misalta yanda yake ji akan yarinyar shin kunyarta yake ko kuma tsoronta yakeji, ko shakkarta shi kansa ya kasa tantancewa, taune Lip É—insa na Æ™asa yayi da Æ™arfi tare da buÉ—e idanunsa da suka sauya launi kana ya tura Æ™ofar falon tare da sallama yana mai tsare fuska.

 

Ummi dake zaune ta tsira masa ido tare da cewa.

“Babana har ka shirya kenan?

Kai ya gyaÉ—a tare da faÉ—in.

“Eh Ummi”.

Kana ya zauna agefenta ya zamana yana facing É—in kichen.

Kallonsa Ummi tayi cike da kulawa tace.

“Amma dai ba kayi breakfast”.

Kai ya girgiza kana yace.

“Uhm-Uhm”.

Da Mamaki tace.

“Toh ya za'a ayi ka tafi da  yunwa ba zaiyu ba Babana ba zaka tafi da yunwa ba”.

Langwaɓar da kai yayi tare da Marerece murya yace.

“Ummi bana jin yunwa fa”.

Fuska ta ɓata kana tace.

“Bafa zaiyu ba Babana baza ka tafi da yunwa ba”.

 

Khausar na fitowa daga kichen ta girgiza kai tare da kallon Asma'u tace.

“Toh ni zan tafi sai anjima”.

Da mamaki Asma'u ta kalleta kana tace.

“Bangane ba kamar ya sauri kike?

Dama ba nan kika zoba ne?”.

Khausar kuwa kai ta girgiza tare da kallonta kana tace.

“A'a ba nan nazo ba dama gidan Aunty RuÆ™ayya naje to da naje sai na sameta tare da baÆ™i shine na kira Mommy nace zan Æ™araso nan mu gaisa.

 Mommy kam  cewa tayi wai da safiyar nan zanzo”.

Moddibo kuwa tunda yaji sautin Muryanta akusa dashi ya kasa É—auke idanunsa akanta duk da cewa kallon Kasan ido yake mata.

Cikin sanyi Khausar ta cigaba da cewa.

“Toh shine nace tayi hakuri ba daÉ—ewa zanyi ba shine fa tace inzo amma kada in daÉ—e saboda mune da aikin rana zan koma in ta yata nazo muyi wata mgna ce, kuma nafasa”.

Da sauri Asma'u tace.

“Dan Allah muyita”.

Kai ta jujjuya tare da cewa.

“Ba damuwa in kin samu dama kizo zamuyita, yanzun sauri nake”.

Ta ida maganar tare É—ago kanta.

Idanunta ne suka sauƙa cikin idanun Moddibo.

 Atsorace ta zira Idonta cikin nasa tare da juya su acikin nasa wanda hakan ya zama kamar hararansa tayi ita kuma cikin mamakin yadda ya rame ya wani zama shiru, ne yayi matuÆ™ar bata mamaki da tausayi domin da dane da tuni ya danna mata harara.

Cike da tsoro ta janye kwayar idanunta daga garesa, tana mai mamakin sauyinsa rayuwa, cikin wani irin sauri ta nufi ƙofar falon yayin da jikinta ke tsuma Muryanta na rawa tace.

“Ummi ni na tafi”.

Kallon yanda ta nufi ƙofar Ummi tayi kana ta kallo Moddibo da har zuwa lokacin idanunsa ke ƙasa da mamaki tace.

“Ya da sauri kamar kinga Dodo?”.

Kai ta girgiza batare data juya ba tace.

“A'a Ummi nikam na tafi”.

Cike da kulawa Ummi tace.

“Toh ki tsaya Kiyi breakfast mana”.

 

Kai ta girgiza still jikinta na tsuma tace.

“A'a Ummi Allah Mommy na za tayi faÉ—a idan na daÉ—e”.

Jinjina kai Ummi tayi kana tace.

“Toh shikenan nagode  ki gaida Mommy ki gashi kin ki kitsaya kiyi breakfast”.

Da sauri tace.

“Allah Ummi sai da nayi breakfast agida kafin na fito”.

Kai Ummi ta gyaÉ—a kana tace.

“Ki gaida Mommy naki da Raudat dasu Haiydar”.

Cikin sauri ta fice daga falon bayan tace zasuji.

 

Moddibo kuwa ahankali ya jinginar da kansa da jikin kujeran tare da lumshe Idanunsa kana ya cije Lip ɗinsa na ƙasa, sai kuma yayi saurin buɗesu sabida ganin surar jikinta da yayi ziraran miraran.

Gashi  da zaran yaji muryan yarinyar zai riÆ™a jin wani irin abu mai wuyar fassarawa kana lokacin da Æ™wayar idanunsu suka haÉ—u babu abinda suka hango masa face.

Ƙirjinta tamkar zasu tsole mishi idanu.

Asma'u Mommy tasa ta kawo masa É—an waken da sukayi sai ruwan Tea ba laifi yaci danwaken da É—an dama kana yasha ruwan Tea.

Malam Ahmad ne yashigo tare da yi masa addu'ar Allah ya tsare miƙewa yayi ya fita kana yaja tsohuwar motarsa zuwan gidan Abba yana isa yayi Hong mai gadi ya buɗe masa Parking Yayi aharabar gidan kana yashiga sashen Abba bakinsa ɗauke da sallama ya shiga falon Cike da kulawa Abba da Hajiya Turai dake zaune gefensa suka amsa masa.

 

Anutse ya ƙarasa tare da zama gefen Abba cike da kulawa Abba yace.

“Aliyu ka Æ™ara so?”.

Jinjina kai Moddibo yayi cikin sanyin murya yace.

“Eh Abba ina kwana ya Æ™arfin jikin”.

 

“Jiki da sauÆ™i Aliyu”.

 

Bayan sun gama gaisawa Abba yayiwa Moddibo duk kan wasu bayanai kana ya bashi wasu takardu da duk wani abu daya kamata sai da Abba ya masa bayani.

Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe kana yace.

“Toh Abba ni zan tafi”.

Ahankali Abba ya sanya hannu a aljihu tare da ciro key mota sabo dal Æ™iran PRADO  ya miÆ™a Masa tare da cewa.

“Ga wannan Aliyu za'a kaika Airport dashi, in Manu driver ya dawo kuma gidan ku zaije ya ajiye maka ita”.

Cikin sauri Moddibo ya É—ago kansa tare da Kallonsa.

“Abba mota kuma?”.

Kai Abba ya gyaÉ—a masa alamar eh.

Cikin sanyi Moddibo ya sake kallon key motar kana yace.

“Abba to ai ina da mota”.

 

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe kana yace.

“Uhm-Uhm Aliyu kenan. ÆŠan Allah kada kayi min gardama ka karÉ“a kawai ka sanya albarka aciki”.

Sunkuyar da kai Moddibo yayi batare da  da yace Uffan ba.

Kallonsa Hajiya Turai tayi kana tace.

“Ka karÉ“a mana Aliyu ai yanzu kam an zama É—aya”.

Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.

“Toh shikenan Abba Nagode Allah yasaka da Akhairi Ubangiji Allah ya mayar maka da dubunsa”.

Murmushi Abba yayi kana yace.

“Ameen”.

Nan take ya ɗauko takardun motar ya miƙa masa tare da cewa.

“Jiya mukayi magana da Alhj Abubakar nasa ya kawo min da yamma gatanan lafiyarta Æ™alau anyi mata dukkan abinda ya dace”.

Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.

“Nagode Abba Allah yasaka da alkhairi ni zan tafi”.

Ahankali Abba yace.

“Allah ya tsare Aliyu Allah ya bada abinda akaje nema”.

Ameen ya amsa kana ya miƙe Abba ya rakasa da kansa ya buɗe masa bayan motar ya shiga, sabuwar motarsa sosai motar ta burgesa duda bai wani damu da bakin abuba, amman collor bakin yayi masifar kyau dan sai sheƙin sabunta takeyi,

Manu ne ya shiga yaja motar suka fita.

 Kai tsaye gidan Malam ArÉ—o ya wuce dashi bisa umarninsa.

Sallama yayi masa kana daga nan suka ɗauki hanyar da zata sadasu da cikin Taraba Jaligo ja gari na Baba Abasu babban birnin Gembila kenan wanda kuma tsakanin local government ɗin nasu zuwa cikin ƙwaryar birnin Taraban tafiyace ta musamman.

Koda suka isa cikin Taraba, basu tsayaba suka nausa hanyar Adamawa Yola.

 

Jauro yaya

Baffan Liman ne zaune agaban Hajja Nana cikin sanyi murya da ladabi yayi ƙasa da kansa tare da cewa.

“Hajja kiyi haÆ™uri bai kamata ace kina fushi akan abinda bai kai ya kawoba, wannan al'amari ba wani al'amari mai girma bane bai kamata ace ki É—auki zafi akansa har haka ba”.

Kallonsa kawai Hajja Nana keyi tana girgiza ƙafa tare da girgiza kai.

Ajiyar zuciya Baffa Liman ya sauke kana ya cigaba da cewa.

“Idan kin lura Khausar fa jika ce agareki ba Æ´a bace, kinga kuwa duk ikon ka akan jika yana zama mai rauni, bare wannan zamanin da muke ya bambanta dana baya dan Allah Addah Hajja kiyi wa wannan al'amarin Kyakkyawan fahimta”.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da fesar da numfashi kana tace.

“Na lura sannan na fahimci Liman da kai dasu Garga, Sadu, Jauro baki É—aya bakin ku É—aya akan al'amarin Khausar tun da haka kuka ce ni bani da abinda zance kuje kuyi duk yanda kuka ga dama”.

Ahankali Baffa Liman ya É—ago ya kalleta kana ya sake sunkuyar da kansa.

Cikin alamun ɓacin rai ta cigaba da cewa.

“Amma fa kusa ni ba zata Auri wannan yaron ba, tunda har ta iya buÉ—e baki ta kalli tsabar idona tace bata son. Aliyu jikina kuma É—an Uwanta toni babu hannu na akanta kuyi mata yanda take so amma banda Auren mara tushe da asali”.

 

Gyaran murya Baffa Garga yayi kana yace.

“Dan Allah Addah Hajja kiyi haÆ™uri shikansa. Muhammadu Jimeta yace zai zo amma yafi so yazo ya sameki cikin farin ciki kada akan batun Khausar ranki ya dinga É“aci abanza a wofi”.

 

Fuska ta ɓata tare da Kallonsu ɗaya bayan ɗaya kana tace.

“Idan yayi niyyar zuwa yazo idan kuma baiyi niyyar zuwa ba yayi ta zama tunda shi kansa bayanta yake bi, tun da wai har cewa yake bazai yi mata dole ba”.

 

Baffa Liman ya sake sassauta muryarsa yace.

“Dan Allah Addah Hajja kiyi haÆ™uri ki bi lamarin asannu da izinin Ubangiji komai zai dai-dai-ta amma bama son ganinki cikin damuwa”.

Haka suka riƙa Rarrashinta tare da kalamai masu kwantar da zuciya.

 

Acan É“angaren Moddibo kuwa tafiya tsakanin  Taraba da Yola tafiya ce mai zaman kanta sai dai bata wuce awa biyu zuwa uku,  tuÆ™i Manu keyi cike da Æ™warewa ga samun sabuwar mota.

 

Shi kuwa Modibbo a hankali ya fesar da sassayan numfashi.

Sabida ji yake wani irin yanayi yana lullubeshi gaba É—aya tunanin J É—in sa ya dawo masa ji yake tamkar idan ya juya gefen damansa zai ga J É—in sa, ahankali ya zira  hannunsa ya kara volume din Æ™ira'ar da yake ji acikin Suratul Nisa'i, sai kuma ya koma baya ya jingina bayanshi da jikin Seat É—in.

Domin idan har ba karatu yake jiba ko kuma yake yi sam baya taÉ“a samun nutsuwa, saidai kuma ta wani É“angaren haka nan  yake jin wani irin farin ciki da yabar garin Gembila, ji yake tamkar yabar wani yanki da yake da tarin Æ™unci, ji yake tamkar yabar wani waje mai duhu da zafi ji yake tamkar ana zare ransa da ruhinsa daga waje mai Æ™unci da azaba, kana kamar ana nufar dashi awaje mai tarin nutsuwa da salama yakeji.

 Domin tun bayan rasuwar Amininsa garin Gembila tayi masa zafi da Æ™unci kana tayi masa duhu baya kallon haskenta gaba É—aya ya tsani garin, to dama Meya rage masa da garin Innayinsa ce kaÉ—ai sai kuma Ummi dasu Asma'u.

 

Sai Misalin Æ™arfe biyu da rabi ya shiga cikin Adamawa suna isa cikin  Adamawa.

Manu yayi Parking A dai-dai Masallacin jum'ae dake cikin Atiku Abubakar shopping mall É—insu nan  sukayi Al'wala sukayi sallar Azahar Kasancewar hanya zai kama, É—an tafiya yasa a gaba shiyasa yayi niyar Æ™asaru  ya haÉ—a da sallar La'asar domin karfe uku dai-dai jirginsu zai tashi.

Baya jin zai iya cin wani abu haka yasa ya kalli Manu cikin mutuntaka yace.

“Manu sannu da yunwa”.

Cikin girmamawa Manu yace.

“Laa ba komai ai kafin mu fito ma naci abinci”.

Kai ya jinjina kana yace.

“Muje ka kaini cikin Airport É—in, sai kayi sauri ka juya, kada kayi dare a komawa”.

Cike da gamsuwa Manu yace.

“Toh”.

Daga nan ya kaishi Airport sannan shi kuma ya fito, ya ɗan samu abin da ya taɓa kana ya kama hanyar komawa Taraba, Gembila.

 

 

Ƙarfe uku Dai-dai jirginsu Modibbo ya tashi daga Adamawa zuwa birnin tarayyar Nigeria Abuja.

 

 

Alhamdulillah cikin kwanaki huÉ—u bizi'nsa  ya fito da yake business bisa ne ba wuya.

Alhamdulillah ranar Al'hamis da misalin ƙarfe biyu dai-dai jirginsu ya ɗaga daga Abujam Nigeria.

 Zuwa Rabat babban birnin Æ™asar Marocco kenan

 

A hankali ya fesar da wani irin zazzafan numfashi dai-dai lokacin da tayun jirginsu ke raÉ“uwa da Æ™asar Nigeria, rumtse idanunsa yayi da karfi sabida wasu irin zafafan hawaye da yaji  suna tsastsafo mishi ta cikin dukkan jijiyoyin idanunsa.

Wani irin yanayin da bai taɓajiba duk tafiye-tafiyen da yakeyi yaji yana dabaibaye rayuwarsa haka kawai yakeji kamar ya bar kasar kenan bari na har abada.

Lokaci É—aya tunanin Jameel ya dawo masa, wanda hakan yasa yayi saurin jingina bayansa da kujerar jirgin.

Yana mai jin wani irin sassayan kuka na taso mishi daga can cikin ƙahon zuciyarsa, hakanne yasa ya fara karatun Alqur'ani mai girma a hankali.

 

Yayinda mutanen cikin jirgin kuwa kowa keta hidimar gabansa.

 

Shi kuwa Modibbo tunda ya zauna bai É—ago kansa ya kalli kowaba.

Sabida yanayin da yakeji.

 

A hankali dai tafiya ta fara nisa, tuni sun kutsa cikin sararin samaniya jirgi ya kama hanyarsa.

 

Koda akazo tambayarsu me yake buƙata.

Cewa yayi baya buƙatar komai.

 

A ƙalla sunyi tafiyar awa uku a sararin samaniya.

Zuwa yanzu kam mafi akasarin matafiyan kowa ya nitsu hada-hadar ta ragu matuƙa, wanda zuwa lokacin kuma sauran musu 57 minutes su dira cikin birnin Rabat sabida daga Abuja zuwa can tafiyar awa uku da minti hamsin da bakwai ne cib-cib.

 

A hankali ya gyara zamansa tare da kallon farin matashi da ya zo ya zauna gefensa wanda bazai wuce sa'anan ba.

Murmushi matashin yayi tare da miƙa masa hannun yana mai mishi wani irin kallo mai cike da tambayo al'ajabi da kaɗuwa.

Shima É—an murmushin yayi tare da bashi hannu sukayi musabaha.

“Jabeer bin Jabeer JoÉ—a. Wanda ya kira kansa da Jabeer É—an Jabeer JoÉ—a É—in ya kare mgnar cike da masifar mamaki da zurawa fuskar Modibbo idanu yana matuÆ™ar mamakin kamanninsa.

Shi kuwa Modibbo cikin yanayin sanyi yace.

“Aliyu Youssef Muhammad Mouley”.

Cikin tsananin bayyanar mamaki ya zazzaro idanu waje tare da juyowa garesa da kyau cikin alamu rawan jiki ya juya harshe zuwa larabci yace.

“Yah Salam toh kuma yaushe kazo”.

Cikin É—an sanyi Modibbo shima juya harshe ih zuwa asalin amintaccen larabci yace.

“Nazo kuma? Nida Æ™asata, me zanje yi a Marocco dai zaka ce”.

Kai Jabeer bin Jabeer JoÉ—a ya jujjuya tare da juyawa yayi mishi mgn da hausa yace.

“Kamar yaya Æ™asar kuma?”.

Ga mamakin Jabeer sai yaji Moddibon na bashi amsa da harshen hausa.

“Sabida ni É—an Nigeria ne girman Nigeria”.

Da sauri Jabeer yace.

“A'a wannan ai ko makaho ya shafa yasan kai ba É—an Nigeria bane kuma ma sunan da ka fadi ai ya isa shaidar inda ka nufa komawa zaka yi ba zuwaba”. Ya Æ™are mgnar da iya haÆ™iÆ™anin gskyrsa da  rawan jiki.

Cikin ɗan ƙosawa da surutun sa Modibbo yace.

“To sabida me?”.

Da sauri Jabeer yace.

“Sabida kafi kama da Larabawa”.

 

“Toh gashi kuma kaima da larabawan kake kama”.

 

Gyara zama Jabeer yayi tare da cewa.

“Kuma ni dai ba fullatanine”.

A hankali shima Middibo yace.

“Minfu mi pullo”.

To zuwa yanzu kam mamakin Jabeer ya tsananta.

Ya buÉ—i baki da niyar zaiyi wata mgnar kenan aka kirashi a baya bisa dukkan alamu Kakanshi  ne da sauri ya tashi ya nufi can bayan.

 

Shi kuwa Modibbo a hankali ya fesar da numfashin gajiya da surutun da Jabeer ya sashin.

Tare da fara karatun Alqur'ani mai girma.

 

Jim kaÉ—an da tafiya Jabeer sai gashi ya dawo zama yayi bakinsa cike da tarin mgn to amman samun yana karatun Alqur'ani mai girma yasa dole ya haÉ—iye dukkan rogowar mgnarsa da tarin tambayoyinsa.

 

A hankali Moddibon ya É—ago manyan idanunsa tare da kallon taswirar kasar Rarat da suka iso tsakiyarta.

Wanda tuni an sanar musu.

Haka nan yake jin wani irin salama da kwanciyar hankali kana da nutsuwa tunda suka shiga yankin ƙasar Marocco yake jin wani irin sanyi da more happy Wanda har ya iya jure surutun Jabeer.

Numfashin mai sanyi ya fesar tare da ƙara ware manyan idanunsa yana kallon garin ta window'n jirgin.

Haka nan yakeji tamkar yabar damuwarsa baki ɗaya acikin Nigeria ya kuma saki dukkan ƙuncinsa a cikin Taraba.

Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yake bin tsarin dogayen benayen gidajen garin da kallo kana sassayan muryarsa na ratsa kunnuwansa yana jin sautin karatunsa da yakeyi jikin suratul Kahf.

 

Misalin ƙarfe shida saura minti uku rak.

Jirginsu yayi sauƙar angulu a cikin babban Airport dinsu.

 Rabat Sale international airport.

Wanda dai-dai lokacin kuma ya dire ayar ƙarshe ta Suratul Kahf ɗin tuni kuma jirginsu ya dai-dai-ta da'irar tsayuwarsa.

Da sauri Jabeer ya kalleshi sai kuma yayi sauri ya mayar  kallonshi gefen damanshi ganin har an buÉ—e Æ™ofar jirgin.

Juyowar da zaiyi kuwa sai ganin Middibo yayi a tsaye yana jawo jakarsa daga drower dake samansu.

Da sauri ya miƙe shima, sai kuma yaji ana kiransa a baya, da sauri ya nufi bayan.

Shi kuwa Modibbo agogon dake hannunsa ya kalla, da ɗan hanzarin sa ya nufi wajen sabida ƙaratowar lokacin sallan magrib.

 

A hankali ya fesar da sassayan numfashi, dai-dai lokacin da ya taka step na forko wanda ya fito da kanshi sararin garin Rarat, duk da dai duk Arfica ne amman ƙasar Marocco sunyi mana rata zarrama mai girma, sunada ci gaba na musamman.

A hankali ya furta.

“Yah Salam”.

Sabida wani irin ni'imtaccen iskane mai cike da salama ke ratsashi yana shiga duk ta inda hudar gashin jikinsa yake.

Wani rin amintaccen numfashin mai cike da yanayin sauƙe ajiyar zuciya ya shaka, like ɗan da ya daɗe baiga mahaifiyarsa ba, kuma yayi kuka.

A hankali yaci gaba da taka steps din yana sauƙo ƙasa.

 

Wani saurin runtse idanunsa yayi lokacin da ya dire tafin ƙafarsa kan ƙasar Marocco cikin yankin Rarat.

Wani irin tsuma yaji naman jikinsa nayi tun daga can cikin jikinsa da zuciyarsa yakejiyo wani irin tsuma.

Wanda ya ta'allaƙa hakan da tsananin yanayin sanyin garin ne.

“Alhamdulillah!!!”.

Ya furta a saman lips inshi sabida, tunda Allah ya halicce shi bai taɓajiba irin yanayin da yakeji a yanzu, ko Saudia yaje bayajin yanayin nan.

 

Yana mai shaƙar sassayan iskan garin ya fara bin ayarin sauran matafiya.

Yayinda can gefen kuma manyan motocine na al'farma wanda bisa dukkan alamun wani babba akazo É—auka.

 

Su kuwa a cikin yanayin gajiya suka ƙaraso inda masu tarɓarsu suke.

 

ÆŠan dube-dube ya yayi.

Da sauri ya nufi wani Balarabe dake jingina da Taxi yana riƙe da ɗan allon tarba wanda aka rubuta Aliyu Youssef Muhammad Mouley.

Yana isa yayi masa sallama.

Cike da tsananin girmamawa Balaraben yayi saurin buÉ—e masa marfin motar tare da cewa.

“Marhababuka”.

Kai ya jinjina masa cike da gajiya da ƙosawa.

Yasan Taxi Abba ne ya turosa.

 

Da sauri shima ya shiga Taxi É—in kana yaja suka fita daga cikin Airport É—in.

A hankali yayi miƙa tare da jingina bayansa da seat ɗin dai-dai lokacin da suka ratso ta cikin unguwar Ben slimane.

Anƙuwace ta masu alfarma, haka yasa tsarinta na musamman ne.

haka nan yaji yanayin Weather yayi masa masifar daÉ—i da kyau.

 

Gashi yanayin damuna ne Iska mai sanyi da ratsa jiki na kaɗawa gashi duk ta inda ka wulga ido bishi yoyin dabinone masu kyan tsari ke rausayawa sunyi kore shar dasu iska na kaɗawa suna rangaji ga kasar garin ajiƙe yake alamun anyi ruwa.

 

Ƙarfe shida da minti sha biyar dai-dai mai Taxi ɗin ya juya hancin motarsa kan wani gini mai kyau da ɗaukan indo wanda a samansa aka rubuta.

Belere Hotel Rabat.

Kai da ganin masifar kyau da tsaruwan hotel É—in kasan zaiyi masifar tsada.

Cikin taushin murya ya kalli Balaraben dake riƙon.

Tare dayin mgn da larabcin.

“Muje wani wanda bai kaishi ba”.

Cikin sanin darajar aiki mai Taxi É—in ya É—an kalleshi ta madubi tare da cewa.

“Toh".

Daga nan ya juya akalar motar ya É—auki hanyar da zata sadashi da unguwar Sidi bettache.

Tafiya kaÉ—an sukayi suka fito kan babban titinsu.

Da sauri Modibbo yace.

“Masha Allah”.

Dai-dai lokacin da

 Idanunsa suka sauÆ™a akan tamfatsetsen masha'hurin hotel mai masifar kyau da tsari daga can sama tsololuwan ginin an rubuta.

Welcome to Sofitel Youssef Mouley hotel.

Da sauri yace.

“Tsaya mu shiga nan”.

Yayi mgnar still idanunsa na kan sunan hotel ɗin da yayi kama da sunanshi hakan don sunan hotel ɗin yaji yana son sauƙa a nan.

Murmushin mai Taxi É—in yayi tare da cewa.

“Toh ai wannan yafi wancan tsadama”.

Da sauri ya gyaÉ—a mishi kai tare da cewa.

“Eh shi yayi”.

 Ya Æ™are mgnar da lumshe idanunsa jin sautin kiransan salla a masallacin dake cikin hotel É—in.

Haka yasa shima mai Taxi É—in saurin shiga.

 

 Numfashi mai sanyi ya fesar tare da buÉ—e Idanunsa daya lumshe kana ahankali.

 

Wani irin hotel ne mai masifar kyau da tsari da girma duk da cewa a farfajiyar akwai masallaci sai dai ba wani Babba bane, amma farfajiyar babbe ne me kyau da tsari daga gefen dama wajen Parking din Motoci ne wanda aÆ™alla zai É—auki motoci settu zuwa saba'in da biyar kana daga jikin doguwar kantamgar kuwa bishiyoyin kwakwane zagaye da ginin daga can gefe kuma wasu irin flowers ne dake wadace  da damshin ruwa haka yasa jikinsu sai sheÆ™i  kayi, tafiya kaÉ—an zaka samu side É—in shiga Reception É—in.

  Atsakiya daga gefe da gefe kuma hanya ce kana daga baya wani Æ™aton gardin ne wanda yana iya hango bishiyoyin dake ciki kana yana jiyo sautin kukan tsuntsaye kala da ban daban.

Ahankali É—ago daga jingina da seat din da yayi.

 Yana Jin zuciyarsa na harbawa kaÉ—an kaÉ—an cikin sauri mai taxi É—in  ya rufe marfin gefensa   cikin sassarfa ya zagoyo gefen da Modibbo yake tare da buÉ—e masa murfin motar kana fuskarsa É—auke da murmushi yace.

“Lalle marhaba fatan an ka isa Marocco lfy”.

Cikin sanyin murya da tarin gajiya yace.

“Yawwa”.

Kana ahankali ya ziro ƙafafunsa waje ya sauke aƙasa.

 Da sauri ya rumtse idanunsa tare da kuma buÉ—esu a lokaci É—aya yaji wani irin abu mai masifar sanyi ya zira masa tun daga tafin Æ™afansa har zuwa Æ™waÆ™walwar kansa irin dai abinda yaji daya taka Æ™afarsa a Airport. cikin sauri ya kuma lumshe idanunsa tare da furta.

“Yah Salam”.

Kana ya fito dai-dai lokacin da mai kira sallah a masallacin hutel É—in yazo dai-dai wurin kalmar shahada.

 

Cikin sanyi ya fara bin kalmar shahadar, wanda hakan ya ankarar da mai  taxi dinma ya amsa, tare da bin addu'a'o'in da yaji Moddibon yanayi.

 

Cikin sanyin murya Mutumin yace.

“Sannu da zuwa”. Lokacin da yaga ya É—an juyo ya kallesa.

Kai Modibbo ya gyaɗa masa tare da buɗe bayan motar ya ɗauki Breafcase ɗinsa tare da jakarsa, da sauri mai taxi ɗin yasa hannunsa ya amshi jakar kan nasa tare da kuma miƙa masa hannun zai amshi Breafcace ɗinma.

Kai Modibbo ya girgiza tare da faÉ—in.

“Barshi, zasu yi maka yawa ai”.

Cikin jin daÉ—i  yayi gaba tare da

cewa.

“Bismillah  kashiga ciki gashi ma Maghariba ta tayi”.

Cike da salama Moddibo yace.

“Bismillah”.

Yayi mgnar tare da nuna masa gabanshi alamun yayi gaba.

Cikin sauri  yashiga gaba kana Moddibo yabi bayansa.

Cikin hanyar da flowers ke ajere gefe da gefe sai É—an mawadacin hanya dake tsakani sukabi.

 Ahankali Moddibo ya taka step É—aya biyu ana ukun ya hau kan barandar Kofar falon.

Ya sanya ƙafarsa na dama aciki tare da furta.

“Masha Allahu laÆ™uwwata Illah billahi”.

Sosai komai na hotel É—in keda tsari na Muslunci da burgewa.

 

Cikin yanayin gajiya ya ƙarasa gaban ma'aikatan dake binsa da kallon ƙurilla.

Bayan sun gaisane ya kama É—aki, cike da mutuntaka da martabawa suka gama komai, É—aya daga cikinsu, ya amshi jakarsa dake hannun mai taxi É—in.

Kana yayi gaba tare dace masu bismillahi.

Cike da gajiya yabi bayanshi.

 

Lifter suka shiga cikin minti biyu suka isa hawa na biyu inda na É—akin daya kaman yake.

Ma'aikacin hotel É—in ne da kansa ya buÉ—e É—akin ya shiga kana ya shimfiÉ—a beshit tare blanket, kana ya wuce da sauran kayan kamarsu Towel da Bathrobe da makilin da Brush sabulu ya ajiyesu bathroom tare da feffesasa Air freshner kana ya fito tare da cewa mishi.

“Sir akwai abinda kake buÆ™atane?”.

Kai ya jujjuya mishi alamun a'a.

Ganin haka yasa ya fice.

 

Shi kuwa Modibbo cike da gajiya ya ajiye woyoyinsa yana mai shaƙar ƙamshin Roomfreshner tare da kallon tsarin komai na ɗakin, komai na cikin falon Ash & maroon colour ne mai masifar kyau kama daga Cottins carpet dama kujerun.

 

Cike da gajiya a shiga bathroom al'wala yayi tare da fitowa da sassarfa.

Lifter ya shiga ya sauƙa kana kai tsaye masallacin dake cikin hotel ɗin ya shiga da sassarfa jin an tada iƙama.

Ya samu tuni sahu forko da na biyu duk sun   cika sai ana uku suka tsaya

Suna shiga suka tada kabbara dai-dai lokacin kuma aka tafi ruku'un Farko.

Bayan anyi Sallah an idar Moddibo.

 Yayi Adduo'insa na yau da kullum, ya kara da na neman aminci cikin wakilcin da zaiyiwa Abba tare da samun nasara da roÆ™on Allah yayi riÆ™o da hannayensa ya bashi ikon riÆ™e amana.

Yana so ya jira Isha'i amma saboda yanayin gajiya da yake ji bazai iya jira ba yana so yayi wanka duk da cewa garin akwai sanyi,

Amma yana son yayi wanka dan yaji daɗin jin kinsa da sauƙin gajiyar hanya.

 A hankali ya yunÆ™ura da niyyan tashi, cikin sauri ya juya bayansa tare da fito da Idanunsa cike da tsananin son tabbatar da ganinsa ya miÆ™a da sauri saboda gani fuskar da bashi da hauki ko kokonta a kai cewa fuskar J...!

 

No comments