Breaking News

TUMFAFIYA 16

 


 

  Allah Allah yake ya gama ya fita ya koma wurin maikayan yaji ko yaya zasuyi dashi kan wanan kudin akarshe dole ya maida hankalinshi wurin abinda yakeyi din.

    Dije wace ta dawo wurin malam tanimu da dan kullin hayakinta data karbo a wurin shi daki ta shiga ta aje ta fito ta gwama wuta duk abinda takeyi hankalinta na kan uwar garke dake kwance tana binta da kallo ko ina tabi.

    Ruwa ya diba ya zaga ban dakin har ya fito yazo ya canza kayan jikin shi lokacin ya fara jin kamshin hayakin da Dije ta buda yana tashi a cikin gidan.

    Da farko ya dauka hancinshine ke shako mai kanshin a makwabta kafin ya tun kari kofan Dije din yaji kamshin a nan yafi tashi sosai ya fara dan sunne sunsune.

   Mikewa yayi tsaya da kyau yana fadin Dije wai me nake ji yana fitowa ne haka wai kai dan Allah ka faye surutun tsiya wallahi ta fada a hasale sai yabi kakan nasa da kallon mamaki a wurin.

    Kayan ya daure yadda ya saba kafin ya leka wurin Dije yana fadin tau Dije ni zan tafi   ga wanan sai ki kara yana miko mata dari biyun daya bata da farko.

   Amadi shigo daga ciki ta fada a sanyaye ya dago yana mamakin tsohuwar ya fada dakin don ganin bakon yanayi a fuskanta na damuwa daya nuna hakan gareta.

  Dije lafiya kike kuwa Amadi ba lau ba gidan ya canza tun dawowan uwargarke gidan nan nake jinshi ba daidai ba sai jiyan kuma na kara tabbatar da hakan.

  Dije uwar garke kuma tace kwarai uwargarke dai Amadi daka sani yanzu kamar ta hurhura ba ita bace a gida  nan yanzu don wanan halinta ya bambanta da wacan.

   Dije don me kikace hakan yanzu tace kwarai don tana bamu alama saidai ganewa ne bamuyi da hakan ba Dije don Allah kada ki firgitani ya fada ya juya yana kallon uwargarke dake kwance tana tuka tana lumshe idonta.

  Bayanin komai daya faru ta fara mai yace gaskiya zancen ki dutse nima naso gane hakan Dije don ko yanzu fitan nan naki saida ta ban wani alama ya fadawa wa Dije din komai har kudin daya tsunta din tace kaji ba na fada ma akwai lauje cikin nadi wanan lamarin gaskiya .

    Koma dai meye Allah ya gani bamuyi niyar cutar wani ba kada Allah yaba wani ikon cuta muna muma ni zan tafi ya fada a karshe ka kula don Allah yace in sha Allahu.

   Ba zaka karya bane yace ki bari zan karya a waje idan na fita don yau kan ba zancen makara bane a wurina don nasan na rasa darasin safe kan.

    Har ya fita ya dawo yana fadin Dije ki rike addua kada kiji tsoron komai in sha Allahu inma ta hurhura Allah zai karemu ga ko meye tace ai wanan hayakin dana karbo tunda na turara naji faduwan gaban ya daina.

  Ki dai hada da addua shine mafita yafi hayaki kaifi duk kikaji wani abu ki karanto addua tsari a wurin Allah tacw ba komai ai tana kanyin hakan itama.

    Amma kadai yi shawara kafin ka koma wurin mutumin ka samu wani ka tambaya zaifi yace zaiyi hakan kasan mutane yanzu ba abin yarda bane yace hakane Dije ya fita.

   Na san na gama makara saboda rikicin su mana dana tsayawa don ko kannina saida ga baya aka kaisu makaranta don kawai gudun zuciyar zama tare da ummah keyiwa yaja muna makaran.

   Na iso makaranta sai dalibai kadan ne a wurin suke shawagi a nan zama nayi cikin mota ina kallo  abinda ke wakana a wajen.

   Sam ban san da zuwan mutum ba don hankalina daya dauku ga tunanen su mama why mama zata dinga yiwa ummah irin wanan halaiyan hakane ?

   Nocking din window motan akayi wanda hakan yasani dan firgita kadan ina kallon wanda ke wajen tsaye.

   Manir ne na gani yana dariya tare da fadin let coma  yau ma kin makara ke nan don gaki a waje dan murmushin yake na sake a fuskana lokaci guda ina fadin wallahi yanzu na shigo nasan na makara na tsaya nan ina jiran har su fito.

    Ashe mun zama daya don nima minti daya na kara na samu har ya shiga ko kinga mutumin ki can tafe ya fada hakan yasani dagowa ina kallon inda yake kallo.

  Watau gaskiya MAYANA dan uwanan naki ina son rayuwan shi donshi haka yake da simple life bai dauki karyan duniya ya dorawa kansaba .

  Yanzu fa kayan gwanjon sayarwane ya dauko haka abinshi ba tare da damuwa ba wallahi gayen na bala,in ban tausayi sosai idan na ganshi.

   Wai me zamuyi mai kan karatun dayake karamune naso mu hadu a hada mai wani abu ina ganin hakan zaifi don kada mu takura ma rayuwa  shi wana  ba matsala bane idan kun shirya saina bada nawa dana Hannatu ai.

  Ah Master salamu alaikum ya fada lokacin daya dan karaso inda muke tsaye din yana washe baki kamar yaga mastern gaskiya a gaban shi.

    Bai amsa ba sai cewa da yayi lafiya dai na ganku ana  ana class yanzu lokacin nake kokarin fitowa daga motar sai cewa da Munir yayi wallahi master mun makarane.

   Kasan halin malami nan da rashin nasiha gara kawai mu tsaya waje har sai ya fito mu shiga sai kuma hankalinshi ya dauke ga wasu daya sani ya nufi wajen su ya barmu tare da master din a wurin .

    Meyasa kike son makarane hakan zai iya jawo maki matsala ga karatunki fa naji ya fada nasan dani yakeyi yasa nace yau mun tashi babu dadine a gidan mu wasu baki mukayi sai dayan ya bata ana neman shi hakan yasani zuwa yanzu.

    Allah ya baiyana muna shi na amsa da amin ya juya kamar zai tafi kuma sai yaja ya tsaya nadago na dubeshi muka hada ido yace dama son Allah wani zance siri nake son yi dake ko zaki fahince ni ban sani ba.

  A take naji gabana ya fadi girman shi na batun barewa a idona a cikin daurewa nace ina jin ka sai naga yana tura hannu a aljihunshi ya ciro wani dan wallet a ciki na fata ya bude ya zaro dollars din Europe ya miko min yana fadin don Allah ko kinsa  wanan kudin wace kasane ?

  Jiya baya na zaro kayana na tsunceshi a ciki har guda goma gasu nan harda address din mai shi a ciki na karbi kudin daga hannun shi na duba Allah ya taimake mu nasan kan kudin don rana  mun zauna da yaya musa muna hira falon mama yai muna bayanin yadda suke.

    Nace ai wanan kudin ketarene kudine masu daraja da kima a idon duniya kudine wanda sunfi kowani kudi daukaka a nan duniya naga alama ya fada .

  Kinga wanan katin kuma ina ganin na mai wanan kudine ya mata ya sako kayan a cikin gwajo ko wata kila ansace mai sune suka shigo nan din.

   Kallon mamaki nayi mai yaci gaba da fadi cikin muryan damuwa da ace da hanyar da zanturawa mai kudin nan da kudinsa su koma wushi danayi hakan na sauke nayin hakkin shi a kaina.

   Haba dai kaiko wana  ai kamar kyautane ubangiji ya bakasu don a matsayin rabo sukazo hannun ka duba nisan tafiyan da suka sha a cikin duniyan amma ba wanda yasan da kudin nan saika.

 Eh to nasan da hakan amma kuma shi maishi kamar bada sanin shi ya bar kudin a ciki ba ai nidai da zan samu a kira min layin naji saina fadawa mai shi cewa kudin yana hannuna zaifi.

   Wai wanan ai long process ne idan har kudin basu kwantama a raiba zaka iya yin sadaka dasu ka huta ai wanan kuma kin kawp shawara babba zan kara bincika inji ya matsayin su suke a wajena.

    Ban katin mugani ko za a samu lanban maishi a ciki sai kayi magana dashi to kina ganin hakan ba zai ja muna matsala ba ko babu wani matsala indai zai fahinci abinda kake fada.

   Katin ya sake miko min nabi katin da kallo na dan lokaci kafin na gane lamban da aka rubuta na waya a ciki nasa na danna kira yana tsaye yana kallona.

   Turancin da ake min yafi karfina na mika mashi wayan tawa kiran iPhone ya karba yana saurare sai kawai naji ya buge da turanci kamar wani wanda ya tashi a kasan waje.

   Turanci sosai yake bugawa da mutumin saida yai mai bayani dala dala baturen ya gane sukai magana ta fahinta dashi yayi maigodiya suka kashe wayan ya miko min wayana yana godiya.

    Mai karatu wanan abin ya kara jawo shakuwa da yarda a tsakanin mu don a tare mukai shawara har na binciko mai inda zaikai a canza mai cikin mutunci ta hanyar bashi lamban ya musa sukai magana dashi.

   Na karbi kudin muka tura mai Abuja ya canzo mashi su in naira sai gashi ya tashi da wurin dubu dari hudu da dan kai wanan ba karamin tsoron hakan yaji ba.

   Kallona yayi da mamaki yace kanwata kin san me ki rike wanan kudin a hannunki ki ban dari na fara juyashi ta wani hanya zan dan dinga zuwa kauye ranan sati in sayo kayan masarufi na kawo cikin unguwar mu in kasa.

   Don wanan da kika ban da wanda na sayar da uwar garken Dije sune yanzu nake harkan gwanjona dasu muna samun rufin asiri a ciki kuma sosai.

  Idan ban fadi karya ba ke alherice don haduwana dake dana rabe ki na samu alheri sosai a rayuwana ba zan boye maki ba.

    Kai haba brother kawai dai nazo a daidai lokacin abine kawai yace ba zaki gane hakan bane kawai abar zancen nace shike nan.

   Sam yanzu banda matsalan kan karatuna don muma haduwan mu dashi ya zama muna alheri a karatun mu sosai sai gashi ana hada babban group yana kara muna darasi saidai ba kulun hakan ke faruwa ba don hankalinshi ya kara daukuwa ga sana,an shi yanzu sosai.

    Kusan sati daya bamu sashi a ido ba gashi karatu ya dau zafi sosai muna yawan test lokaci lokaci sai hakan ya tayarwa yan uwan karatuna da hankali.

   Suka yanke shawaran cewa mu hada kafa muje har gidansu a dubashi ko lafiya da bama ganin shi dole yasa ba bisu don bani zuwa ko ina daga makaranta.

   Munir ne ya binciko muna sunan unguwarsu din da kwatancen gidan nasu a inda zamu samu isa a saukake ga sayayan da muka hada kudi akayi za a kai gidan nasu.

  A motana muka shiga saita munir din da maza suka shiga sune a gaba muna biye dasu a bayan su zuwa gida da dan nisa sosai da school din mu.

    Dije ne kadai a gidan ban daki ta zagaya ta fito ta tsaya tana wanke hannayen ta idon ta ya sauka kan tsiron daya fito daga gefen dan gatangan kasan daya zagaye gidan nasu .

    Ido ta kurawa wurin kafin ta taka zuwa gaban dan tsiron ta kara kura mai ido sosai hannu takai zata cire don kada haki ya jawo masu sauro don hakane gidan ko yaushe fes yake a garesu.

   Wani kuka uwargarke tayi wanda yasa Dije firgita tana fadin ke yanzu nasan kukan ki da ma,ana yake watau kina nufin na nabarshi kada in cire ko ?

  To Allah ya sauwaka ta fada tana barin wurin da sauri don lamarin uwargarken ya fara bata tsoro yanzu sosai yasa ta kara rike addua da karban magani a wurin malam tanimu da har saida ya shigo da kanshi kallo  uwargarke.

  Inda ya kara tsora Dije da fadin indai ba sun shigeta ba to tana da shafansu a jikinta gaskiya don alamu sun nuna hakan sosai ga dabban.

   Haikan dije ta tsani uwargarke yanzu saidai tana tsoron nuna hakan afili don gudun wani abu yazo ya sameta wanda ya shafi iskokai.

    Da tambaya Allah ya kaimu gidan nasu a kofa muka tsaya inda ba iya gidan ba kusan unguwan nake karewa kallon mamakin ashe akwai irin wanan unguwar tallakawan a cikon gari haka har yanzu.

    Kofan gidan da naga munir din ya tsaya sai mamakina yakaru lokacin layin shiru sai motsin daka da mukeji a wasu gidan unguwan.

    Fitowa yayi daga motanshi kiran honda ya nufo inda muka tsaya yana fadin to ai saiku fito ku mata ku shiga kuyi muna sallama ciki muji dole muka fito na tako da kyar ina bin bayan su zuwa cikin gida .

 Hannatu ce a gaba muna biye da ita kusan nice fa karshe don haka akaji sallamana daga bayan su .

  Wani kuka mai ban tsoro mukaji saida kowan mu ya kadu saboda sautin kukan nata har zamu juya  muryan tsohuwar daga ciko tana fadin sannun ku da zuwa su waye ?

   Nikan tsakiyansu na shige don ga bakidaya tsoro nakeji mama Ahmed muke nema mama Hannatu ta fada Ahmed a gidan nakuwa eh mama nan akai muna kwatancen gidansu.

    Wanda ke karatu a jami,a babba kamar yadda yan gari ke fada kodai Amadi tsohuwar ta fada kai tsaye sai hannatun tace shi mama Amadi kuke ce masa ko ?

   Ai saiki yawace unguwan nan kaf kuna neman shi da sunan nan ba a gane ba amma dakunce Amadi kowa yasan nan ne .

    Yanzun nan ya dawo daga kauye kwana biyun nan duk bai fita don ciwon kafana daya tashi yana gidan nan yana kula dani.

  Yaune dana danji sauki ya tafi kauye dauko hatsi kuma har sun dawo don naga an fara shigo da kayan su daga bayan mu mukaji suna shigowa yana fadin tunda kunzo aisai kun shigo kunga kakata Dije.

  Turus yayi don ganin mu gaba dayan mune ashe mukazo don bai farga da motana dake can gefe dana parker ba a unguwar don samun saukin fita idan zamu koma.

No comments