Breaking News

TUMFAFIYA 45

 

 


AFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH  ,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

4️⃣5️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

 

   Abu kamar wasa karamar magana ya zama babba don mazajen su Aisha sunzo da lokacin da suke son bukin su aahe mama kuma ta gama shiryawa hakan.

    Don haka zancen auren su dai ya taso lokacin gadan gadan don kowa yasan lokacin buki a cikin dangi duk da ba,a sani ba hakan bai hana in saka kaina a cikin zancen ba.

   Tunda gidan mune za,ai sha,anjn bukin nima a bangarena ina nawa shirin a hankali abinda bamu sani ba shine harda ni ake shirin wanan bukin wata rana ummah ce da girki ta shiga gun Abba.

   Yake fadi a gadarance ki fadawa yarki ta turo min wanan yaron yazo mu zauna dashi a cikin mamaki umma ta kalli Abba din tace wani yaro ke nan fa ?

   Abba ya kalli ummah fuska daure don anfi wata yana daure mata fuska hakanan daga ummah harmu babu mai ganin fuskan Abban din a yanzu  idan yana gidan.

    Wanan dan iskan yaron data nace masa kika daure mata gindi a kansa kuma nayi nadama sosai a rayuwana danayi sakaci har hakan ya faru dani.

   Mamakin ummah ya kare a lokacin don haka bata san lokacin data bude baki tace da Abban kwarai kuwa yadda kayi nadama nima hakan nake nadama a kullun a kanka.

    Mutumin da ya kawoka gari bai damu da damuwan ka ko sanin halinda kake ciki ba sai son zuciya da bata kawai kasa a gaba duk abinda aka fada maka a kanmu ya zaunu a zuciyar ka.

  Kaje mun barka da Allah duk wullakancin daka shirya zakui muna Allah yana sane da hakan maamah dai yata ce don haka aka biyo ta gareta a kuntata min Allah yana tare da mai gaskiya ko yaushe.

    Zuwa lokacin hawaye ya gama wankewa ummah fuska ta juya ta fita daga falon suka hade da mama da zata shigo tabi ummah din da kallo ta fada falon.

    Zaune ta samu Abban din rashi a bace shima take fadin lafiya naga kowan ku haka rai a bace dan tsuki Abban yaja yana fadin barsu kawai.

   Wai na fada mata zahra ta turo min yaron nan shine take fada min maganan banza mama tayi saurin fadin ita salma din yace ni suke son batawa suna a banza.

  Aidai shike nan tunda kace su turoshi in ma wani abin ne su sukajawa kansu hakan ai kace kai baka iya kwaban yaro sai duk abinda yayi daidaine gareka.

   Daga baya kuma azo aga laifin mutane a banza hakan dai da kayi shine daidai din yanzu a hadata da yan uwa a wankesu kowama ya huta yafi.

    Abban bai kara magana ba don yadda yake jin zuciyar shi game da zancen a lokacin har ta gama ta koma part din ta tana labartawa su Aisha abinda ya faru.

  Budan bakin Rukaiya tace a,a nikan baso hakan ba gaskiya ga zahra dadai an barta ta fito da wanine mama zaifi gaskiya..

    Wani harara uwar da Aisha suka jefeta dashi Aishan tace aisai ki nema mata wanda kike ganin ya dace da ita ko ki bar mata kabir din ki ta aura shike nan.

   Tasan cowon kantane ita wanan din aida itace haka ya sameki farin cikin hakan zatayi a ranta tunda yan iska suke gara na nuna ma salma bata kai ba wallahi .

   Haka zasu kare daga ita har yar nata a cikin wahala da tsiya ko yaushe wasa take dani kawai bata sanni ba har yanzu sai sunyi kukan jini da idanunsu gidan nan.

    Miji kan wane ita tace ra fiku shi saidai ta nuna maku kyau da baida rana a gidan badai ta fiku mijin nunawa tsara ba kan.

   Na dawo a gajiye na san Abba na gari don haka ban warganta ba koda din dai bana tsayi saurin dai na ranan yafi na kullun.

   Na iso part din mu ina sallama duk da ummah na falon zaune nayi mamakin kin karba min sallaman da batayi a ranan har na karasa na gaida ita ta amsa min da kyay da gani tana cikin yanayin bacin rai sai naji ba dadi a raina.

    Haka na shige daki na kwabe kayan jikina nashiga bandaki na dan jima na fito na saka kaya ajikina falo na fito naci abinci lokacin ummah bata falon tana daki suna waya da hjy karima lokacin.

  Don ta samu labari shine ta kira ummah din suna maganan da ita kanzancen sai da batun sune na kishiyoyi da bai karewa kowa nason ganin bayan dan uwa ko wani tashin hankali ga dan uwa.

    Ta dai gama dadin bakinta a lokacin sukayi sallama ta kashe wayan anyi kiran magariba na shige ciki dama dabia tace bana fitowa inci abincin dare idan naci na yamma.

  Don haka sai ban fito ba a ranan bansan wainar da ake toyawa a gidan ba ke nan don ummah tabi shawaran hjy karima ta koma wurin Abba sunyi ba dadi ga zancen.

  Har Abba ke fadin an fada mai ko kwanaki angan mu da Ahmed a bakin wani layi mun tsaya muna magana dashi akwai zubar da mutuncin dayafi wanan.

  Meye dalilin sai mun motan da yayi don in ta tsayawa da maza ya saya min ko don me zai saya min mota ina yawan banza a gari.

   Don haka zai hadani da yaron muje can mu karata kuma ummah ta sani zai saka dokoki masu tsauri a kaina saina gane kurena na kin maganan shi da nayi.

   Wa,iyazubillah ummah kan ta shiga tashin hankali don ranan kwana tayi buge bugen yawa saidai kamar hadin baki magana daya ake fada mata cewa tayi min adduan Allah yasa hakan shi yafi zama alheri a gareni.

   Karshe data kira aminiyarta ita ta kwantar mata da hankali tayiwa ummah din nasiha sosai ta lurar da ita abinda ta kasa hangowa a tunanenta.

   Hakan yasa ummah ta kwantar da hankalinta taci gaba da al,amuranta kamar komai baya damun ta a rai da safe ina dakina ina shirin fita makaranta sai gata ta shigo dakin nawa.

   Nayi mamakin hakan sosai saidai a fuskanta na fahinci akwai maganan da take son muyi da ita lokacin don haka na bar abinda nakeyi na dawo kusa da ita na tsuguna.

   Naji tace dani bayan na gaisheta maamah mahaifin ku yace in fada maki ki turo wanan yaton yanzo ya ganshi kafin ya koma  .

   Kallon mamaki nayiwa mahaifiyar tawa don ban fahinci wani yaro take zance ba lokacin sai naji tace wanan yaron da dai kina nacewa tunda an rabaku kin ki rabuwa dashi.

    Ummah wake nan kike nufi wai Ahmed ko wa ni yaushe rabon dana ga Ahmed a idona mutumin da yanzu bai ma garin nan sosai yana karatu a zaria tun bayan gama school din mu marabina dashi haka.

   Kada kimun karya maamah don Alh yace ko kwanakin baya an fada mashi anganku a wani layi dashi kuna magana don haka yanzun dai yace ki turoshi yana son ganin shi.

    Kasa na zube na fara rantsuwa ga ummah ta daka min tsawa tana fadin kimun shiru ki saurareni kiji mezan fada maki.

  Ko kusa bana son inga kin nuna wani abu cikin zancen nan ki natsu kiyi yadda kikaga nayi din idan anyi don aga bayan mu na roki Allah ya mayar muna da hakan alheri a garemu.

   Nasan bana nufi dan kowa da mugun nufi a zuciyata don haka Allah yasan dalilin haka garemu duk abinda za,ayi ko Alh ko wani zaice dake kan haka  kiyi hakkuri ki shanye hakan a zuciyar ki.

   Nasan anyi hakane don an dade ana neman hanyar da za a tozartani cikin garin nan Allah bai basu dama  yin hakan gareni ba sai yanzu suka biyo gareki suga sun tozartani nidake.

  Don haka duk ritsi da wuya kada ki yarda ki nuna hakan ya bata maki rai ni zan biki da addua ako yaushe Allah ya bashi yaton ikon rikeki amana ya hore masa abinda zai kula dake a rayuwa.

    Kuka sosai na fashe dashi don hawayen da naga ummah din nayi a lokacin da take wanan maganan gareni ta mike kawai ta fita har takai kofa ta juyo tana fadin kada ki manta da kiran nasa na fada maki.

  Komawa nayi na zauna na bude babin kuka mai tsuma zuciya ta yaya haka har ya faru har Abba ya yadda da sherin da ake bina dashi a yanzu kala kala komai a fada masa cewa nayi kuma ya dauka haka din ne.

    Wayana ya dauki kara na duba hannatu ce nasan bataga na shigo school bane zata tambayeni ko lafiya bata ganni ba.

   Ban dauki wayan ba har ya katse ba a jima ba ta sake kirana naki dagawa don banda courage din daukan waya sam a lokacin yadda nake jin kaina kamar bani bace.

   Layin ummah ta kira don tayi serving a wayanta takan kirata su gaisa tana tambayan ummah din ko lafiya bata ganni ba kuma ta kira ban dauki waya ba ?

   Ummah din tace da ita bana jin dadine yau tayi Allah ya sauwaka ta kashe wayan shine ummah din ta shigo dakin ta sameni tana fadin hannatu ta bugo dazun.

   Ganin yadda na koma yasaka ummah din tsayawa tayi min fada sosai ta kara da fadin hakan dana fara nunawa zaisa suji dadi sugane abinda suke nema garemu ya fara samuwa a garesu.

   Ko shi Ahmed din yaji ina bore a kanshi ya dauka ko bansonshi ne sai lokacin na dago kai na kalli ummah dakyar na bude bakina nace ummah ba soyyaya a tsakanina dashi sai mutunci.

   Da sannu zaku saba na kalleta ina mamakin saukin kai irin nata haka tace eh idan makiyin ka yana jifan ka da sheri nuna masa baka damu da hakan ba sai abin ya koma ma taki karshe suji kunyan hakan.

   Kedai abinda nake so daje har in Allah yayi shine mijin naki son Allah maamah ki zauna dakin ki lafiya kiyi biyayya ga mijin ki ba wanda yasan abinda gobe zai haifa ga bawa.

    Lokacin dana auri mahaifin ku kusan hakane baida komai banda takardun shi sai lokacin da akaga ya fara samu ya samu wanan aikin lokacin ne dangi sukai ta kawo mashi yayan su ya aura.

   Sai ita mamaku dayake itace uwar yayan nasa duk da a lokacin kowa yasan tayi girma a cikin mu amma haka akayi aurensu har take yadda taga dama yanzu a gidan nan.

   Don haka ki natsu ki bi mijin ki ku zauna lafiya kada naji wani abu ya fito daga bangarenki nima yin auren naki a yanzu shine saukina don hankalina zaifi kwanciya da hakan.

  In sunga su  kai inda suke tsamanin zaki cutu nasan zasu fita zancen ki kuma su kama wani don dama abinda ake so ke nan a gareki aga rayuwan mu a lalace kawai ba karuwa.

   Niko na yarda da arziki na Allahne shike ba wanda yaso a lokacin da yaga daman hakan ga bawansa don haka ki dauka dama wanan na cikin kadaran ki.

    Nayi kuka kamar raina zai fita bayan fitan ummah dakin gashi ta kara fada min lalai in kira Ahmed din in fada mai sakon Abba yazo don an kasa kunnuwa aji kome zai faru.

   Idan kuma ban kira ba din za a iya cewa shima Ahmed din ya gama danine ya gujeni kai jama,a uwa mai kishiya ko yarta bata huta ba wani lokacin.

    Don haka fitanta dakin na dan wani lokaci na lalubo wayana ina neman layin Ahmed djn zuciya cike da zargin abinda zan fada mashi din ko yaya shima a bangareshi zai dauki maganan nawa don nasan baida zarahin aure haka gagauce gaskiya.

   Kira daya biyu gana uku ya daga yana dan zolayana ta fadin yan makaranta ba lectura ne a ajin kika samu lokacin kirana yanzu ?

    Ahmed kazo inji Abban mu yana son ganin ka yau din nan da yamma ina ji yai wani kara yana fadin what ni Abba keson gani kuma zahra mekikayi ko ince me akace mashi kuma munyi.

    Da kyat na iya tattaro karfin hali na bude baki ina fadin saidai kazo din kaji don nima dai bansani ba dazun maganan yazo min haka .

  Innalillahi naji ya ambata tare da fadin Allah yasa dai ba wani kake bane kuma akai muna a wurin shi yake son daukan mataki a kan mu saidai idan kazo din na fada na kashe wayan.

    Kai ya dafe lokaci guda don dama a tsaye yake suna lissafi na kirashi lafiya wanda yake tare dashi ke tambayan shi yake fadin bari wani zance naji daya tayar min da hankali .

   Allah yasa alherine yace amin amma gaskiya da wuya hakan ya kasance sai dai addua kawai sukaci gaba da lissafin da suke saidai shi zuciyan shi cike yake da maganganu lokacin.

     Don har in ba matsala bace me zaisa Alh yace yana nemansa kuma a yadda yaji muryana yasan ba lafiya don ya fahinci nayi kuka sosai a lokacin har muryana ya dakushe alaman kuka.

    A gagauce ya gama komai ya nufo gida ba abinda yake tunane sai zancen su da su Dije da mahaifiyar shi lokacin gaban shi yaji yana faduwa.

   Yana anyana wanan karon zai iya kyale Abba ya sake ci masa fuska irin wancan karon nasa dashi kuwa kada kuma yasa ai masa wullakanci jami,an tsaro su kamashi kamar yadda Alh ya fada a baya.

  Shi yaba  akanshi amsa akan me yarsa ce yace in rabu da ita na barta sai dan zumuncin da mukeyi yanzu sama sama dashi kawai.

   Ya goge yan kaya  da zai saka wasu yadi farare an mashi dinkin daidai gwiwa ya saka hula a saman kanshi ya tunkari gidan namu.

    Yayi sa,a Abban baida wasu mutane sosai don haka bai dade ba ya samu ganawa da Abba din daya dade tsungune bai juyo gareshi ba har tsawon wani lokaci.

  Sai can ya dago yana fadin kaine kwanaki nanemi kazo gidan nan akan zancen zahra ko Ahmed din ya gyara yana fadin nine Abba OK Abba din ya fada kafin yace wani mataki kake dashi ga karatu ?

   Ya dan kara dukawa a ladabce yake fadin yanzu na jona A,B,U zaria ne ina hada masters dina kan kimiya sai Abba din yai mashi wani kallo kafin yace.

   Hakan na da kyau Allah taimaka saidai ina fatan kana da inda zaka aje ta a yanzu don zan hada bukin kune dana yan uwanta taje can gurin ka ta hada karatun ta a can din.

    Wani irjn zufane ya karyowa Ahmed din don ba hakan ya zaci ji daga bakin Abban ba lokacin sai da yayi ta maza ya iya ffadin eh to ba za a rasa ba daidai iya karfina Abba.

   Koma meye wanan matsalan kace daga baya yanzu ina son ka turo min magabatan ka in gana dasu zan fada masu lokaci idan sunzo daga haka Abba ya mike ya barshi nan sai dai muryan shi da Abban yaji cikin dan sanya yana fadin.

   Abba nahode Allah ya kara girma da daukaka bai jiyo ba don haka baisan ko ya amsa mashi ba lokacin yasa kai ya shige ciki shi kuma ya tashi ya fita gwiwa a sanyaye.

    Yana fita yaji kamar jiri zai daukeshi saida ya dafa bango ya saka takalmin shi a kafanshi ya nufi hanyar fita get din yana ji kamar mafalkin komai yakeyi ba da gaske bane lokacin.

   Gida ya nufa kai tsaya saidai bai iya shiga gidan nasu ba nan ya tsaya a kofan gidan yana faman tunanen ta inda zai farawa zancen ke nan ?

    Yana zaune saman mashin dinshi wayanshi ya dauko daga cikin aljihun shi ya fara neman layin zahra don yaji meke faruwa daga bakinta har hakan ya faru ?

    Ya kira har kiran ya kusa katsewa kafin na daga har lokacin muryana a dakushe yake bai fita sosai Zahra meya farune naje wurin Abba naji zancen da ban taba zato ba daga bakin shi yau.

    Nima yadda kaji haka naji yau din nan nan na kwashe yadda mukayi da umma na fada mashi amma ba duka ba naji ya nisa yana fadin ikon Allah yafi gaban mamaki.

    Zahra bansan me zance dake a rayuwana ba sai dai godiya da addunan fatan zaman lafiya mai daurowa a tsakanjn mu nida ke.

   Zan kiraki an soma kiran sallah yanzu zan kiraki zuwa anjima mu karasa maganan mu insha Allahu nagode kwarai ya fada ya kashe wayan.

 

 

No comments