Breaking News

TUMFAFIYA 61


 

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[4/28, 5:52 AM] +234 706 815 1331: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH  ,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

6️⃣1️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

 

 

Daidai lokacin da nazo gittawa ta gefen shi sai gaji nayi ya zabura da karfi kamar wani abu yabi ta saman kanshi yasashi tashi firgice har saida na tsorata daga inda nake nakai kofa na tsaya ina kallonshi

 Ya dan kama wajge waige kafin ya mayar da kanshi kasa na dan lokaci can kuma ko ya tuna cewa ina wurin ne sai ya dago ya dan kalleni.

  Lafiya dai na tambayeshi ya girgiza min kai tare da fadin ba komai anyi sallah ne nace da dan saura lokaci sai naga ya mike ya shiga daki .

   Ruwa ya watsa ya dauro alwala ya fito ya tafi massalacin yayi sallah daga can ya wuce zuwa kasuwa ya karaso sayayyan su ya dawo .

   Ina daki don ni nasaba da zaman dakin idan ba wani abu ya fito dani waje ba lokacin ko yaushe zaka sameni a dakina zaune .

    Indana gane ya shiga kasuwa ledan da nagani dauke a hannunshi lokacin yasa na fahinci hakan wai ashe tsaraba ya sayo da zamu kaiwa kannena a gida.

    Saida ya fara cin abinci yake fadin anjima saiki shirya muje gidan mu gaidasu kafin intafi don in tafi zuwan zai zama maki matsala kuma.

    OK yau din zamu tafi ke nan na fada ehmana ko zaki iya hawa mashin din garba zuwa ya tambaya yana kallona don kinga yau din idan mun tafi tare nima sai in samu in masu barka ai.

   Hakan nada kyau kuma zanji dadin hakan mashi kuma me zai hanani hawa tunda sunsan ba mota muke dashi ba dama ba kunya a cikon hakan ai.

   Nasan ke yanzu baki jin kunyar hakan gaskiya amma ummah ba zataji dadin ganin mu haka ba ai ita ya fada a cikin wani irim murya mara dadi nace baka ko fahinci ummah ba har yanzu gaskiya.

    Zahra irin wanan dalilin yasa kikaga ina jajircewa ga karatun nan don mu samu abin rike kammu nan gaba dana iyalin mu masu zuwa don kada ki fito daban a cikin yan uwa.

    Ka daina irin wanan tunanen don Allah Allah fa bai manta damu ba master ko yaushe kaga bawa a wani hali yana sane da rayuwanshi ko a hakan mungode ai in anfimu mu kuma munfi wasu ai.

   Hakanane wallahi irin wanan halaiyar naki zara ke kara kwantar min da hankalina da ace ni wanine zahra ba abinda zai hana banyi sharia da mahaifina ba don a yanzu shidin wanine a cikin kasan nan.

   Wananne rana na farko daya sako min zancen mahaifinshi a hiran mu duk zamana a gidansu dan haka da sauri nace don me zakayi sharia dashi kaiko ?

   Don an tabo min inda ke min kaikayi saboda na kasa gane zancen mahaifin nasa gaba daya har nakanyi konkwanto ince waiko dai zancen mutane akansa gaskiyane wani lokaci.

   Sai naga ya girgiza kai kaiwa cikin takaici ba tare da yace min komai ba a lokacin yaci gaba da cin abincin shi yana tunane a zuciyarshi lokacin.

   Nima dai tunanen nakeyi na cewan da yayi mahaifin nasa wanine yanzu a kasan nan don me ya fita batun danshi mutum kamar Ahmed ace baya tare da mahaifin shi.

  Wai a ina matsalan takene nasan dai matsalan ba babba bane don da babbane yadda ake fada Abba ba zai yarda ya aura mashi niba haka duk da naji su mommy na fadin ba haka a banza Abba ya daura min aure da Ahmed din ba ai .

    Akwai shige da ficen da wasu bangare sukayi aka fitar mai da hankali don a tozarta ummah dani a idon mutane koma meye nidai nasan ina son mijina sosai.

   Muna idar da sallah magariba muka fito cikin shirin mu na daiji yanacewa Dije zai kaini gida mu gaidasu bai fada masu yar uwata ta haihu ba don haka nima naja bakina nayi shiru.

   Har zamu fita naji yace yar uwantace ta haihu zamuje barka Dije ke fadin madalla karuwa aka samu ashe to muna masu barka ita kuma inna sai cewa tayi.

  Kaji mata masu biyan bashi ba akawo a cinye a juye a masai ba kullun mutum na kiwo ana zama kamar bata kiwo a gida ko dabbobi keci haka ai suna biyan maishi.

    Nagane nufin ta sosai amma ban nuna hakan ba don naji Dije tace aikowa yaci bashi da niyar biya yake dauka Allah ya horewa kowa ya biya da hannunshi sai naji ya lalubu hannuna alaman mu tafi.

   Mukai masu sai mundawo muka fice daga gidan yana jaye da mashin dinshi da yake shigowa da ita har cikin gida saboda tsaro.

  In kuma dare tayi zai jawota zuwa part din mu ya tura cikin kitchen din mu a kulle idan kuma zai tafi school dakin Dije yake ajewa duk saboda tsaro.

    Ya tada mashin din na hau yafara tafiya sai naji yace irin wanan halin na inna nadaga cikin abinda yasa nake son barin gidan nan zahra duk abinda ya faru da ita kwanaki bata daddara ba har yanzu.

   Wai kwanaki kinsa uwar garke ta taba ita kuma tayi mata irin waibuwan su na dabbobi amma har yanzu baisa inna ta daddaraba ga halin ta ji wanan maganan da take fada yanzu don Allah .

   Me uwar garke tayi mata na tambayeshi a gagauce kovya mantane ya shiga labarta min abinda malamin da aka kaishi wurinshi ya fadamasu.

   Ai dabba taiwa rashin mutumci wanan uwargarken akuyan namu tunda kinsan in dabbata kosa tana da waibuwa akace shine nan ta rikide ta bata tsoro a dakin tunda bata tausaya mata ba.

   Daga bayan mashi nace what da dan karfi sai lokacin yagane katobaran da yafarayi yace ke bafa wai ita din aljanna bace ko wani abu ita din a,a wani lokacine dai sai aljannu su shiga jikinsu su yiwa mutane abinda zai basu tsoro idan sunga ba daidai ba sai su tsorata mutum shi nake nufi.

   Ai bansan da cewa tsoro yasa nayi mai wani danka ba a lokacin daga baya inda nake zaune nayi shiru yana magana banma jishi ba son tunanen da makeyi a lokacin.

   Zahra fa ya ambata da dan karfi  firgigit na amsa mai yace ina hankalin ki yaje kuma ina magana kefa kin faye tsoro wallahi wanan maganan ina abin tsoro a cikin sa kuma ?

   Ba zan kara kaiwa dabbobin nan abinci ba ko wani abu ko inda suke ba zan kara kallo ba gaskiya sai naji ya kwashe da dariya yana fadin banda abinki ai kyautatawan da kike masu zaisa su ganeki su san kamshi ki da muryan ki ko wani lokaci.

   No a dai bari kawai kaima da kake kyautata masu baisa sun bar mahaifiyarka ba ai balle ni bakuwa a cikin ku dama idan ina gida naga rana yayi nakan kai masu ruwa in zuba masu abinci son naga Dije ke wahala dasu yasa nake hakan.

   Don Allah kici gaba duk na sani wallahi su kadai na gada daga kudin mahaifina daya barmin shiyasa kikaga dije na kulla min dasu yanzu kuma gaki kin karbeta zakice kin daina kuma princess ?

  Nifa tundaka fadi hakan tsoron su nake ji yanzu kuma gaskiya tunda mutum ba sanin ya masu laifi zaiyi ba kai ina ilimin ki ya shiga kike wanan maganan haka nimafa bawai na yarda da wanan maganan bane kawai dai abinda mutumin ya fada nake fada maki.

   Daidai lokacin muka kawo kofan gidan mu ya faka na sauka a hankali muka kwankwasa maigadi ya bude muna kofa muka shiga muna gaisawa dashi.

    Duk da yana ganin duhu a lokacin babu abindake fita bakinshi har cikin zuciyar shi sai kalman innalillahi baiyi aune ba yaji hawaye yana zubo mashi a fuskanshi lokaci guda.

  Tabbas yasa yana da yaron daya haifa da matarshi ta farko Rashida basulluba yar zamfara da sukai aure na saurayi da budurwa a lokacin da yabar gida a baya can da kurciyarshi.

   Ada can baya yana yawan tuna yaron yana kuma da sha,awa  ya daukoshi ya dawo kusa dashi ya zaune dashi ya tashi a gabanshi amma sannu a hankali zancen yaron nasa gaba daya yafita a zuciyarshi.

   A baya yana tuna yaron amma sai yakanji kiyayyan yaron da uwarshi da tan uwanta ya ziyarci zuciyar shi a irin hakane har yaji kwata kwata yaron ya fita a zuciyashin baki daya.

   Shaf ya manta da zancen shi ga baki daya sai gashi lokaci guda a yan watanin nan ya fara mafalkin wanan yaron da baisan kowaye ba sai bai kawo cewa wanan dan nasa bane ruhinshi ke bibiyan shi a yanzu.

    Amma yau zancen abokan nasa ya tunasar masa da hakan ko yana raye ko yana mace yanzu Allahu ya alamu don baisan ta inda zai fara nemanshi ba yanzu.

   Tunda an yamusa garin a yanzu an maida ita jaha mai cin gashin kansa itama yasan a yanzu ba Gusau din da yasani bane a baya don zasu samu cigaban zamani.

   Kai anya kuwa yaron nan yana raye shekara ashirin da takwas amma har yanzu ba wanda ya waiwayi juna da yana raye yasan malam ladan nada wayayyen kai dolene zai nemishi akan yaron don ko lokacin bawai iyayyen Rashidan na ainihi suka bijirewa zuwanshi da itaba nan yan uwan haihuwan iyayyen ne suka kawo wanan matsalan.

  Duk da yasan yana son Rashidan a lokacin yadda yake ji a jikinshi don kiran da akaimai gida na asiri ba zai iya dakatar da tafiyan nasa ba a lokacin.

   Don kirane na gagauce a duk inda yake a lokacin dole sai ya dawo gida ko babu shiri kamar yadda lokaci guda suka turashi cikin duniya ba wanda yasan inda yake hakama wanan karon aka kirashi ya dawo gida ba shiri.

   Idonshi ya runtse a cikin takaici yana maijin zafin faruwan hakan a rayuwanshi why da abubuwa suke zo mashi a hakane cikin rayuwanshi kadai.

   Yasan ya dawo gida da niyar komawa ya dauko iyalinshi a lokacin amma sai abubuwa suka faru da yawa bayan dawowan nasa har yakai ya manta da zancensu a zuciyar shi.

  Oh lord ya fada a fili tareda furta Astangafurallah Allah na tuba ka yafemin kada ka kamani da wanan babban laifin dana aikata a rayuwana.

  Yasani iyayyen Rashida da yan uwanta ba wasu masu karfi bane a garin tallakawane tilis inba Allah yai masu wani budi daga baya bane irin haka dole ke nan yaron a yanzu yana can cikin wahalan rayuwa.

   Bayanshi yana nan da nasa iyalin a cikin daulan duniya da jin dadin rayuwan da bai musaltuwa a lokacin son shidin ba mutum bane mai tauye iyalinshi.

   Yanzu ina zai fara bullowa wanan matsalan da wani ido yanzu zai baiyana garesu yace yana neman dansa dan da baisan cinshi da shansa ba har ya rayu yakai wanan shekarun masu yawa haka ?

   Dolesu jauro zai nema a asirce kamar yadda yanzun ma suka tunatar dashi hakan asan yadda za a bullowa maganan da wuri kada ya mutu ya bar baya da kura kuma don yasan halin matarshi ba yarda zatayi da hakan ba shi yanzu ina zaikai wanan alhakin a rayuwan shi.

  Godiya da tasbihi ya shiga yi a zuciyan shi yana mai lumshe idanuwan shi kadai yasan yadda yake ji a zuciyanshi yasan alhakin hakan dole ya kamashi a wani bangaren rayuwa.

    Hjy Yabi ce ta shigo part din a lokacin jin motsin mutum yasashi dago kai ya kalli mai shigowa dakin a lokacin matarshi ya gani hakan yasa ya sauke kanshi kasa daga kallonta.

   Barka da hutawa yaji bakinta na fadi yau karo na farko azamansu kunuwanshi ya jiyo mai hakan a bakinta a ciki ya amsa mata ta samu wuri ta zauna tana mai kallon fuskanshi dake daure lokaci guda.

   Alh wai da wani matsalane ka canza gabadaya cikin yan kwanakin nan mu bamuji dadin kaba kai kanka bakaji dadin kanka ba kuma kaki fada muna abindake faruwa mu sani ?

  Lafiya nake haka dai naga shine daidai yanzu don naga kina kokari dake da diyanki ku maidani mace ke ki zamo miji a gareni yasa na daukarwa kaina matakin hakan shine kawai ya fada yana dago kai tare da kallonta.

    May ya kawo wanan zance kuma ana zaune kalau zaka fadi haka a cikin mu waya nuna maka cewa baka a matsayin ka na ubangidan nan yamzu ?

   Nina gani na fahinci hakan don haka nake shirin daukam matakin daya dace dani a yanzu wanda shine daidai gareni gako wani magidanci kuma.

  Gaban hjy yabine yake wani irin faduwa don abinda take tunane shidin take ganin ya faru a lokacin hakan na nufi duk wani shiri na sihiri da kulli da sukai mai suka daureshi abin ya karye a yanzu haka ke nufi.

  Cikin karfin hali irin na hamshakan mata tace dashi kai Alh wanan zance ai bai kamata a bakin ka wani power naka zan dauka ko yaran nan su bani bayan kowa yasan a karkashim innuwan ka muke rayuwa a gidan nan.

    Idan ma Baku sank ba said Ku fara sank son Abubakar din da kuka sank a baya bashi bane yanzu kuke kallo wanda kuka mayar dashi da banza duk days a wurin Ku.

   Shiru tayi tana Dan kakaro murmushin dole a fuskanta don tunanen ta ya wuce abinda takeji a gareshi yanzu dole wani aikinsu na baya ya samu matsala a wani bangaren .

  Inko haka tasan akwai aiki a gareta babba yanzu don't yaushe zata iya tuna wani abinda akai mashi a baya ga kuma hjy Korau uwar rikon nasu sun samu matsala yanzu da ita akan yayanta.

    Zakace ba haihuwa akayi ba a lokacin don't yadda naji gidan shiru koda yake darene a lokacin watakila kowa ya nufi gidansa sai kuma gone su dawo ga yadda nasan aal,adan yan uwan my ko garin mu

   In an haihu kai maigida ka shiga uku don yawancin yan uwa a nan suke tarewa kullun suna gidan sai dare za a watse said bayan suna kafa ya dauke.

    Shine abinda ya bani mamaki a was a wanan karon data kofa muka tsaya muna sallama kusa sau ukku ba a amsa muna ba kallonshi nayi ganin haka yasashi daga muryanshi da karfi ya kwada sallama a daidai lokacin aka bude kofa.

   Mama hafsice zata fito tsci karo damu tsaye a kofan dakin cikin mamaki ta amsa muna sallaman tana fadin ashe bakine daga can ciki naji mur I an mama tana tambayanta da su wayene a kofan ?

   Nice mama nayi saurin bata amsa kafin mama hafsi din ta bata amsa ta bude muka shiga au Zahrace ashe yanzu like tafe aina dauka bakiji haihuwa  ba ma son ban ganki ba ?

   Naji mama dazun nan ummah takirani tana fada min anty Aisha ta haihu barkan mu da arziki ubangiji Allah ya rays muna bisa kan sunna amin.

   Nafada freely da murmushi a fuskana tace amin gaba daya hankalinta na kaina tana kallona daga samana har zuwa kasana lokaci guda nikuma na fahinci hakan.

   Nasan ba komai take kallo ba sai shigana na lokacin duk da ba laifi amma ita taga kasawa a hakan dama shi take son gani a gareni don' komai daya shafeni baya burgeta ita.

   Ki shiga suna ciki tare da hjy tsohowa cewa kakan mu sai nace a cikin kunya tare muke dashi yana kofa yazo yai maku barka shima OK tare da mijin naki kike ashe ?

   To kije ki shigo dashi ciki mana ta fada a cikin izza da isa iron nata na mike na fita ta bini da wani kallo mai kama da harara tana jan tsoki tare da kawar da kai gefe daya.

   Nayi masa iso da mu shiga daga ciki na juya zan shige naji ya dan jawoni na juyo kudi ya danka min bansan ko san ko nawa bane nayi godiya yace No da sauri.

   Ina gaba yana biye dani a bayana zuwa ciki yayi sallama suka amsa mai su ukune zaune a falon lokacin har kasa yakai ya gaidasu kafin ya fara masu barka da karuwan da aka samu din.

    Rakiya kira masu hjy nan su gaisa ta fada a gadarance don mama badai magana a gadara ba kan balle ta samu wurin yi a yanzu.

   Jin hakan yasa nasan ba sai mun shiga ciki ba kenan a nan zasu zo mu gaisa dasu son azato har maijegon din amma sai naga hjy ta fito ita kadai dakin itama saida ta jima ta ja muna rai tabarmu a zaune shiru a falon  kafin can ta fito tana Dan dingisawa irin na manyanta.

   Su waye ke neman ta fada a gyatsire tana kaiwa saman kujeran farko dake falon bayanta kalle mu gata nan takwarankice ita da mijinta sukazo barka mama ta fada har lokacin tana mike a saman dogon kujera da waya a hannunta.

   Waye takwaran nawa ta fada kamar bata shedani ba tana wani gimtse fuska a cikin daurewa mama tace gata maisunan kicefa ta nan gidan.

    Yanzun taga daman zuwa ita issasa duk yan uwa dake nuna farinciki sunzo sun tafi wani iri naji a lokacin,  bansan lokacin da nace muma ai farin cikin mukazo nunawa kedai hjy duk da kin dade bakiga mutum ba sai kin yaba masa magana son ranki.

   A,a makka kikaje karshen dadewa ina kina cikin garin nan dai karshen dadewa unguwar sullubawa  da kika zabi zama.

    Sai naga mama ta kalloni ban fasa maganan ba naci gaba da fadin yanzu da naji din bagashi munzo tun ba,a kwana ba ?

   Ke kada ki shiga min ido ana magana kinayi har wani aure kikayi na gwadawa tsara da kike ganin wuyan ki yakai yanzu da zaki fadawa mutane magana yadda kike so .

   Tashi muje ya fada a hankali daga bayana inda yake zaune din itako taci gaba da fadin masu manda da uhumm basu  rawan kan aure.

    Naji zafi naji ciwo a raina amma saina dake INA fadin in auren banzane kije kiyi mana ai naggidan ai zawarawan fake sonki had yanzu na mike da zuman shiga dakin naji mama Rakiya na fadin Aishan ko ta samu barci fa.

    OK in ta tashi a gaida mun ita muna mata barka da sauka lafiya ya mike yace mama zamu tafi Allah ya raya muna na mikawa mama rakiya kudin daya bayar abawa jaririya nace ga wanan inji shi asaiwa jaririya kwali.

   Kai haba dai kana fama da kanka da iyali cikin Dan kunya yace ba komai mama ayi hakkuri dashi son Allah to an gode ta fada nayi mask saida safe muka fito zuwa part din mu.

  Nan ma bamu dade ba min gaida ummah ta tambayemu mutanen gida na barsu tana kara mashi nasiha na shiga wurin kannena har sunyi barci a lokacin.

   Mukai mata sallah muka fito bar muka hau mashin din my banji yayi magana ba a lokacin zuwa gida don haka nasan ranshine ya baci sosai nima nayi shiru.

No comments