Breaking News

TUMFAFIYA 63


 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/1, 11:07 AM] +234 903 973 1553: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH  ,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

6️⃣3️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

 

Na samu taji dama tana zaune ta idar da sallah nagaida ita tare da tambayanta karfin jikin nata tare da kokatin nemanshi a layin wayan shi.

    Yana dauka na mika mata ta karba suka fara gaisawa dashi yake tambayanta karfin jiki naji tace dashi naji sauki ai  dama bata fadama ba jikin nawa ai kullunne ni.

    Banji me yace mata ba sai tace zan mata magana idan jikin ya matsa min tayi mai godiya tare da adduan neman tsari agareshi ta miko min wayan na karba.

   Na mayar a kunnena yake fada min na fada mata idan jikin yakiya tayi maki magana kuje asibiti don Allah da ita ko ki kaita chemist abata magani nasan baki rasa kudi har in dawo ai ?

   Zamu anjima idan na gama girki su bata maganin daya dace yace shine daidai don haka zatayi ta fadin taji sauki amma jikin na nan.

    Sai kuma ya koma tambayan badai matsala komai ko bayan tafiyana nace ba komai wallahi saidai wani brother dina dake zaune USA yayi waya dazun yake fadin na hadoma shi civic din ka akwai wani aiki da zasu dauka na tsunci bakina yana fadin haka.

   Yaya Musa ko ya Jafar ya tambaya da sauri nace a,a brother Bisi na lagos dake can zaune makwabtan mune inda muka zauna a lagos muka zama kamar yan uwa dasu lokacin har yanzu kuma ana zumunci dasu sosai.

   Shine ya kira dazun yana fadin na turo takardun ka ko nawa saidai ni ban gama karatu ba a yanzu sai a fara turo naka idan suna complet   sai naji yayi shiru na dan lokaci.

  Itako Dije dake gefen mu sai faman fadin take madallah madallah Allah abin godiya Allah maji rokon bawansa Allah mungodema.

    Kina dakin Dije har yanzu ke nan na amsa maida eh ok idan kin koma part din mu zamuyi magana sai ya kashe wayan nabi wayan da kallo don dama na zaci hakam tunda ban taba bashi labarin Bisi a cikin yan uwan mu ba.

     Dijeko sai fadi takeyi madallah wanan dan uwa naki Allah ya saka mai da alheri abinda yake nema na alheri Allah ya bashi na amsa da amin tare da fadin tuwo zan maki kici ko Dije ?

   Tace to tuwon naso tunda rana amma wa yanan makiyautan sunki girka min sai hanjin bature da suka sulala wai shine abincin gayanan na kasaci tundazun ma.

  Na kalli roban da suka zubo mata taliyan a ciki har ya fara bushewa gashi hankade da dan jajage kadan a sama nace zakisha shayi mai zafi yanzu in fara hada maki ?

   Tace idan na samu zansha tun kunun safene a cikina sai naji ta bani tausayi sosai naga harda sakacina a cikin barinta da yunwa tunda ina gidan nima ai da sauri na mike na hado mata shayi mai zafi da kauri da guntun bread din da mukai amfani dashi da safe.

   Na kawo mata nadan zauna na fifita mata saiga Asmau ta leko tana gani take fadin a a a yar tsohuwa dama ciwon kwadai kikeyi ashe shayi kika samu haka da kauri Dije.

  Shayi na samu wurin yar arzikin data san ciwona ba irin ku masu nema su kwace min ba sukayi ta musayan baki ina masu dariya.

   Ta tafi na bata tasha saiga zufa ya karyo mata a raina nace kila harda yunwa ke damun tsohuwarma lokacin nan na mike na fito ina mata sannu ina saka takalmana a kofa naji muryan inna na fadin.

    Mu ina zamu samu muna yar dangote a gida duk wani nema nasa yanzu ai can yake karewa wurinta yaushe zai tsaya bamu wani kayan shayi can yanzun ma kafin ya tafi da yaya ya hada muna abincin da zamuci ?

    Raina ya baci ranan na bayar da amsa nace ba diyar dangote nake ba amma yar babana nake shayi kuma ba a gidan nan na koyi shanshi ba da abina ya ganeni bama na wahala irin wanan ba.

  Don ko yaushe kaje gida  mu zaka samu kayan shayi zube saman dining table don babu mai kula dashi ban karban kudin daki ko na hanashi ya sai maku abu amma inna kin dauka nice ke hanashi baki abinda kikeso gareshi.

    An fada ko bakiso na fada auren kine yake kokarin juya min baya a yanzu bani gane kan dana amma ke gidan ku ai yana kai masu don a yabeshi.

   Kadin nayi magana naji muryan Dije na fadin ke kan Rashida kinji kunya tun yar nan bata baki amsa har yau an wayi gari ta gaji da halinki takai ga baki amsa daidai dake.

   Dama ke zaton ki shi dan naki yana iya daukan duk lalurantane kome ki rabu da So sone kawai ke aikinsa nan amma ko kallon yar nan kikayi kinsa ba kalan danki bane ita.

  Sai kuma ta juyo gareni tana fadin yi tafiyan ki ki kyalesu da ita mara tausayin wace taje ta fada masu din dan kin tausaya min kin hado min ruwan zafi nasha naji karfin jikina Allah ne maganin su.

  Marasa godiyan Allah kawai in kina da kunya ke har kyayi wanan maganan don ta taimaki uwarki ina zaki san ta taimakeni kina daki da diyan ki tun safe kuma shewa zan mutu ku kwashi ganima.

    Nikan ganin abin zai rikice masu naja kafana na koma part dina cike da bacin rai na barsu ina jin hayaniyarsu daga part dina ina mamakin hali na inna da zata tsaya tana sa,insa da mahaifiyarta haka.

   Yanzu nagane da danta be kula al,amarinta ashe yasan halin abinshi har ina ganin laifin farkon shigowana gidan sai yanzu na fahinci inna irin mutanen nan ne da basu danne zuciyarsu subar abu a cikin su komai kankantanshi.

    Hakan yasa na manta da wayana dake kuryan daki ashe yayi ta kirana ban sani ba saidana gama aiki na dauko waya naga six misscall din shi a wayan.

   Ban kirashi ba don raina yana bace sai gashi ya kira banyi saurin daukan wayan ba saida ya kusa katsewa na daga murya ciki ciki nake amsa mashi.

   Naji yana tambayana kina inane waya nata rinngin baki daga ba ina kitchen na bashi amsa a dakile yace banace inkin dawo part din mu zamuyi magana ba na sake fadin aigani yanzu.

   Jin hakan yasashi fadin wai meke damunkine princess ina magana kina bani amsa wani iri ba yadda kika sababa sai naki yin magana a lokacin.

  Da sauri yace min ko wani abu ya farune kuma nace gaskiya nagaji da irin yadda inna ke min don kawai na hadawa Dije tea shine zai zama wani magana har tace aurena dakai yasa yanzun baka kulawa kana kwasan kudin ka kana kashewa a kaina ni har, , , , ,

   Cool down my dear ba sai kin kai karshe ba don nasan kina hakkuri da zancen inna dama yau daine tayi maki fiye da kullun don Allah zahra ki kara hakkuri da inna tunda kinsan halinta.

    Naji nace amma kawai don Asmau ta fada mata magana sai ta dinga zuba min arashi kamar sa,anta nake mahaifiyarta fa na taimakawa.

   Kin gani ba nan zaki gane abinda nake fadi da farko kina fada kina ganin laifina nace kai dantane ai dole ka bita ko yaya halinta yake .

   Wai Asmau bari yar kam uban nan da nadawo zasu koma gidan dagin ubansu su zauna na gaji nagaji wallahi da yan iskan yaran nan dako sharan gida basu iyawa saici da tsegumi.

    Ka hada takardun ne na katseshi da fadi naji yaja tsuki yace barin loda kudi na sake kiranki ya kashe wayan a cikin takaici.

   Nima na jefa wayan gefena inna son zuwa in duba tsohuwar da jiki saidai kuma takaici ya hana inje part din nasu don nasan inna na nan sun baza tabarma da diyanta a lokacin.

  Sallama naji daga kofa na amsa Aishan shice ta shigo wurina a cikin rashin sakin fuska na amsa mata ta shigo tana fadin ashe baki barci ba na dauka harkin kwanta ai.

   Nace ban kwanta ba Aisha ta zauna tayi shiru na dan lokaci kafin tace Anty Zahra banji dadin abinda ya faru tsakanin ku da inna ba dazun.

    Duk Asmau ce ta kawo zancen nan duk dai bata dauka itama zancen zaiyi tsawo haka ba don ta shigone tanawa Dije sheri shine inna ta karbe maganan ta juyeshi ya zama haka.

  Don Allah kiyi hakkuri kin saba da halin inna ai yanzu kibar tankawa don Allah kada ajiku da ita nasan idan yaya yaji hakan ba zai masa dadi ba.

  Kinga ni yanzu na gane tana kallo ko yanzu na shigo nan din don ba zata rabamu ba muna gida daya kina muna alherin da zakiwa kannen ki don haka kika daukemu muma.

   Asmauce ta shigo itama tana fadin nikan na wuto wai innace ke kwala min kira na dawo naki matan yaya kallo zaki kuna muna a waya muyi dama don yaya na nan ne bamu zuwa.

    Mamakin halinsu naji nikan na jawo wayan na kuna masu wani film din tan Philippines da muke kallon season film tana fadin mun wuce nan ai yana kiran wayan.

    Hakan bai hanasu yin surutunsu ba yace keda suwaye a dakin nace su Aisha ne ya kunduma zaki dame sukazoyi yan kaza uba ?

    Kasa kudin ke nan na fada na kawar da zancen a lokacin yace eh yanzu na sayi a banki kin saka loudspeaker ne ko kuwa nace ban saka ba yace tambaya dama zanyi yaya akayi guy din nan zai bamu aiki.

    Kai tsaye nace idan zancen bai kwanta maka bane a barshi don Allah ni j  nagama zan nemeshi yabani tunda niya sani yace haka zakice min nace naga kana son fassaramin zancen ne da wani manufa banji yayi magana ba ya kashe wayan.

    Na kunna masu na mike ina fadin zan dubo Dije in gaida ita da jiki suka amsa da sai kin dawo nan na fita na barsu zaune suna kallo can na iske inna tayi bakin mata masu zuwa sayen kayanta.

   Na shiga wurin Dije muka gaisa na samu tana cin abinci lokacin yasa na dan jata da hira tanaci muna taba hira tana ban hakkuri kan abindaya faru nace ai ya wuce yanzun ma su Aisha na wurina na barsu suna kallo.

   Ban jima ba na mike zuwa part dina na kwanta ina fadin in sun gama su tayar dani in rufe kofa Asmauce tayi saurin fadin ni a nan zan kwana barin tashi in rufe gida dayani.

   Inna nada baki a cikin gida na fada tace zan fada mata ta rufe don yaya yaja muna kunne sosai kan rufe gida wai barayi ke yawo a unguwa.

   Ta mike zuwa cikin gida bata dade ba ta dawo tana guna guni ta fadin wai inna kada mu kwana nan yau don dama idan baya gari a yan kwanakin nan da muka fara shiri dasu sukan kwana a part dina saboda kallo.

    Ai basu koma a nan din suka kwana dukkan mu falo muka kwana tare dasu nayi sammakon tashi zuwa school inda daga can gidan mu zan tafi in duba maijego sai dana shirya na shiga sallaman su nake fada masu sai da yamma zan dawo zan tafi gidan mu daga can in duba mai haihuwa .

   Asmau tace dani aida daga nan zaki tafi da mun tafi tare ina son zuwa gidan ku wallahi mutum baj fitowa ba a bashi wani abin karuwa ba gashi kuma kaci ka koshi farat inna tace to yar mayunwata fada mata gidab ku gidan tallakawane.

  Ji inna meye yanzu matar yaya bata sani ba game damu saidai idan mutanen gidansune basu sani basu ni dai na fita na barsu da shirmen su.

   Ina mamakin yadda Ahmed ya fito cikin cikin wanan matar haka halinshi ya fito daban shi kodan bai tashi tare da ita bane oho don dana biye mata ko da safe da mun kwasa tana fada da yaranra kan sun kwana part dina tana fadin wai ana dauke masu hankali da kallon banza da zai lalata masu tarbiya

   Kai haba inna wani irin bata tarbiya mutanen dako yarensu bamuji kuma ba irin tufafin mu suke sakawa ba don Allah ya horewa yaran nan ta baki basu da kwabo ko kadan.

    Shiru yayi yana sauraren abokin nasa har yakai karshen magana kafin ya dago ya kalli sauran dake saurarensu sukace kwarai kuwa don ko gaskiya Alh jauro ya fada.

  Duk yadda mukaso muzo kusa dakai a lokacin matarka dama kai kanka baka yarda da hakan saidai aimu bamu kika ba don ko yaushe muna tare dakai don munsan hakan bayin kanka bane.

    Duk abinda kake yi alama ya nuna muna ba a cikin hankalinka kake muna mun so mu share zancen ka mu zauna a inda Allah ya ajemu saidai a yadda muka taso dakai mun kasa hakan gareka.

   Badon komai ba sai sanin cewan da mukayi cutar dakai zasuyi a karshe don badon Allah suke tare dakai ba kuma gashi duk yan uwanka sun kawo ido suma sun saka maka duk da sunsan gaskiyan zancen suma sunyi fushi dakai a yanzu subar zancen ka.

   Idanunshine ya ciko da hawaye lokaci guda don jin zantuntukan da abokan nasa suke fada a yanzu yaushine mace ta mayar hakan a cikin yan uwasa da abokanan sa lokaci guda.

   Yanzun dai mu godewa Allah dayasa ka gane hakan da wuri tun lokaci bai kure maka ba don da ka mutu a cikin halin gaskiya akwai matsala babba.

    Aishi mutum mai alheri Allah baya barinsa haka dama don ko sun hanaka komai basu hanaka alheri ga mutanen makwabtanka ba.

    Wanan ma ya isa ya taimaka maka ka fito daga kanginsu don ba haka sukaso gani a gareka ba sunso suga sun rabaka da kowa a garin nan.

   Yanzun dai ba wanan ba yaya zancen da muka fara dakai a waya na yaron nan don ya kamata ace zuwa yanzu kasan matsayin da yaron nan yake ciki.

   Fuskanshi ya shafo don maganganun nasu sunyi masa yawa a kai duk da dama yasan dasu abaya amma yanzun da yake kara jin hakan a bakunan su sai yake jin zancen kamar sabo a gareshi.

   Sun dauki lokaci a tare dashi har zuwa magariba kafin zuwa sallah bayan sun fito kowa ya nufi wurin iyalinshi akan da safe zasu fito su rakashi zuwa wajen yan uwan nasa na haihu.

    A cikin gida kuma itama hjy mariya mamakin abubuwan dake faruwa sai take ganin abin yau kamar a falki yake zuwa mata ba gaskiya bane yau mijin nasune yazo gareta shi kadai ba tare da matarshi wani lokacin da yaransu da basu da kwabo ko kadan.

  Zasuzo su mayar da ita kamar yar aiki agidan sai sun tafi take samun sa,ida a rayuwanta don hakanema bata kaunan zuwan nasu saboda cin fuskan da ake mata din idan sunzo.

   Ya shigo gidan bata saba idan yazo ta sameshi ba kamar yadda ko wace mace ke samun freedom da mijinta idan yazo sai gashi ta kasa zuwa gareshi.

   Sai shi din ne daya fahinci hakan ya taso zuwa gareta sai taga abin wani irin bambarakwai a gareta don haka lokaci guda ta rude da ganin shi kai duniya.

 

No comments