Breaking News

TUMFAFIYA 13

 


 

   Don Allah kada kiyi ko kayi gangancin karata wana  novel din a audoo don na sayar dashi already ga wasu yin hakan shari,ace tsakanin mu.

    Zaman dai ba dadi amma hakan baisa mun bar gidan ba muna dakin ta sai shabiyu muka fito zuwa gida don zamu shiga islamiya lokacin.

    Sai dare na samu zama da ummah mu a falo naji ta tambayeni wai meya hadaku da hjy yau ibrahim ke fada min tayi ta maku fada tana zagina da baban ku ?

    Ummah zancen motar nan daine aka kai mata don mun samu su mama gidan wurinta nasan kara suka kai wai ashe Abbane ya saya min sai gwaggo uwanice ke dan tsawata mata har ta daina zancen amma taki sakin fuska damu.

   Sai cewa take ai Abban zaizo zataji dalilinshi nayin fifiko a tsakanin diyan shi don ita ba zata lamunci hakan ba tun tana raye ya fara yin haka ina ga ta kawu bata duniya saidai idan ansa abinda akai mai a karkashin kasa.

   Murmushi naga ummah ta sauke a fuskanta tana fadin Allah sarki yanzun ne zanwa Alh asiri kuma dacan baya ashe suma asirin sukai mashi ke nan ko ?

   Little sister dinace ke min nuni da abinci na diba na bata wanan ya dauke min hankali ga maganan da mukeyi da ummah din.

    Monday mun shiga school sam na mance da zancen karatu dan break din da muka samu sai ga mutum uku da mace daya sai wanan kawar dana samu tunda ita ke aje min wurin zama kafin nazo dana shigo zata daga min hannu nazo na zauna.

  Oya muje muga guy din nan don muji ya za ayi tunda  yau yace damu za,afara wa ke nan na tambayeshi cikin mamaki au har kin manta da zancen ke nan ?

    Keko zancen karatun mana da zamu fara ta fada haka suka sani gaba dole na tashi mukaje muka sameshi yana gyara kayan gwanjon shi a bayan aji.

  Gaisuwa suka fara mai muna tsaye daga baya kafin ya dago yana fadin yanzun ya kuke son ayi don gaskiya zaku takura min ga sana,ata kunsan tallaka baiga zama ba naso fita in zaga da kayan nan nawa cikin hostel ku kuma gaku.

   Hakkuri zakayi master don kyau alkawari cikawa manir ya fada ok ya fada yana dan kalle kalle kafin yace mu karasa daga can zaifi wurin ba yawan gittaya sosai don haka sai yai muna dadin zama.

   Bayani ya soma muna tun daga farkon yadda zamu gane kan topic din da Munir ya gabatar mai zaka rantse shi din wani baturene ko babban lectura ke bayani.

    Abinda ya dakatar damu yan class din nasu ne sukazo mai da wata tambaya hakan yasa muka barshi a lokacin muka koma namu building din.

    Tallan gwanjo na maimaita a fili why ga karatu ga kuma sana,a lokaci guda haka au kina mamakin guy din nan ne ko nima a gaskiya naji mamaki sosai wallahi.

  Gashi Allah ya bashi amma baiyi girman kai da hakan ba ke da ganin shima kin san yana bukatan taimako sosai a rayuwanshi ko suturan jikin shi ka kalla.

  Kune yayan manya irin su ya kamata ku dinga taimako inda halin hakan tunda muma yana taimakon mu da nasa baiwan da Allah yai masa ai yanzu.

    Ba wanan ba ai da alaman wahala sosai z tare dashi idan kin dubs ya fada muna zamu takurawa rayuwan shi amma yanzu kina nufin da wanan sana,an zai rike rayuwan shi ?

    Wata kilama hardana wasu a karkashin shi yanzu haka idan kin bincika ko yana da aurema a kansa ai kinsan yadda yake a kasan nan tamu yiwa yara auren wuri su dawo suna wahala daga baya.

   Kai gaskiya shiyasa aka bar arewa baya sosai saboda irin wanan matsalan  na tara iyali da wuri kaiba shekaruba ba wani aiki ba amma an cika gida da iyali.

   Munyi hira sosai akan matsalan daya shafi nahiyar mu da dalila  dake kawosu har lokacin sallah yayi muka mike zuwa masalaci kafin mu dawo wani malami har yashiga ko saidai munyi sa,a bai koremu ba don yasan sallah aka tafiyi.

    Da yamma lis muka fito sai ban tsaya komai ba na nufi wurin motana ina kokarin budewa na hangoshi yana fitowa da kumshin kayan shi ta bayan block din mu duk da kayan sun dan rijayeshi nake gani amma haka ya daukosu ya nufo hanyar da zai fitar dashi haraban wajen.

    Sai naji zuciyana nason na taimaka mashi duk da bai kalli inda motana yake ajiye ba lpkacin haka yasa na tayar da motan na mike hanyar da zai sadani da inda naga ya bi..

   Horn nayi mai haka  baisa ya juyoba sai tafiya yake da sauri da kumshin kayan shi a kai lokacin da gani sauri yake sosai zuwa get inda zai samu abin hawa.

   Ga wasu kayan rataye a hannayenshi glass na sauke a hankali ina fadin yayana muje in sauke ka mana don bansan sunan shi ba har lokacin.

   Bai jiyo ba yasa na kara danna mai horn jin hakan yasa ya dan juyo mukai arba na danyi gaba na tsaya ya zagayo nake fadin .

   Na bude booth already na fada yace for what zan saukekane inda zaka dan murmushi ya sake yana fadin nida zan yawata da kayana ina ni ina shiga mota nagode kwarai da taimakon ki ya juya yana kokarin cigaba da tafiya a wahalce.

  Binshi nayi da kallo cikin tausayi na dan ja motan na cin mai hannuna yana cikin jakkata ina lalube naji kudin a inda na ajesu na jawo tare da fadin.

   Ga wanan sakon don Allah  ya juyo na mika mai da sauri ina fadin idan ka bude zaka ga takardane ya amsa yana mamaki na figi mota na na barshi wurin tsaye yana kallon envelope din dana mika mai din.

   Bai budeba naga yaci gaba da tafiya yana turowa aljihun shi na halba saman titi bansan yadda ya karasa va don ni kaina bansan nawa bane ya musa ya ban ba gaba daya na mika mashi su wanan lokacin.

    Tun daga get din gidan mu nagane anyi baki a gida saidai yanayin bakin maza ya nuna ba daga nan arewa suke ba ashe kawar mamace tazowa mama a bazata ita da yaranta daga lagos.

      Saida na shiga gidane ummah ke fada min zuwan hjy Rafat din nasanta sosai farin sani duk wani iya shegen bariki itace ta koyawa mamashi zaman su a legas tare.

   Don daya bai wanka ya bushe yana gidan daya mama ta iya shige shigen yarbawa kamar me haka al,adun su duk ta iya sosai don haka yaren lagos radau a bakunan mama da yaranta kaf.

   Akwai wani dan hjy Rafat din daya samin ido sosai idan naje hutu yana cewa wai sona yakeyi wanan yasa  dana fara girma na daina zuwa legos wurin su hutu kamar yadda na saba ina karama saina fake ga karatu a lokacin.

    Kai tsaye na nufi dakina na soma cire kayan jikina sai nayi wani tunane hakan yasa na juya na fito falo na zauna naci abinci babu kowa daga cikin kannena a lokacin don hakane gidan yai shiru a lokacin.

   Saidan motsin Tani dake aiki a kitchen lokacin kadai ke tashi a falon da sallaman zamani Rukkaiya ta shigo ta hangoni zaune saman dining table din mu ina cin abinci tace min ke mama na kiranki .

   Nima juyowa nayi jin yadda tayi min magana na mayar mata da fadin wa,ni ina nuna kaina da hannuna tace ke mana ok idan na g

hada zanzo na bata amsa nima.

   Kamar zata sake magana sai tayi shiru ta wani irin juyawa kamar a hasale lokacin ne tace ina zakizo kizo don ba mama bace ke son ganin mami Dele ne tazo dama akace akiraki ta hada da tsuki ta tafi.

 A daidai lokacin umma tana fitowa daga kingun shiga dakunan kwanan mu na part din ta bita da kallo saida ta karaso take tambayan meya kawo wanan nan ?

   Wai inzo inji hjyn Lagos ta fada ai dama zaki kigaida ita tunda batai maki komai ba koda tayi kuma ai bata fitar a fili ba angani.

  Saiki tashi kije kada kuma taje ta fada masu wani abin daba  don karamin aikin Rukkaiyane hadin fada kindai san halinsu ba sai na fada maki ba.

    Dole na mike nabi bayan ta na shiga da sallamana falo suke zaune gaba dayan su jin sallaman nawa yasa suka juyo suna kallona banda mama da yan uwana da suka hade rai a wurin.

   Hjy Rafat da diyan ta uku suka fara sake min murmushi tare da fadin see u you na your face be dis kowan su fuskan shi dauke da fara,a a gareni.

   Da dan sarsarfa na karasa gun mami din saidai na dungumeta kadan na saketa nakai kasa tare da fadin your welcome mah ta shafo kaina tana fadin ji yadda kika koma wata babba dake haka Zarah?

   Na danyi murmushi kadan tare da tambayanta ya hanya na dago kai ina gaida yaya nata da duk suka zubo min idanuwan su a kaina lokaci guda.

   Bayan na gaidasu mama data mike tun shigowana ta dawo ta zauna kusa da mami din na dago a cikin fargaba ina gaida ita ta amsa min da fadin lafiya kalau kun dawo ke nan ?

   Eh na fada na dukar da kaina kasa muryan mami Dele dince ke fadin u no see you man Dele, he de worry me asking you yanzu kuma ya ganki ya noke kamar bashi ba.

    Nayi murmushi sai kanin nasa yace shima yaji mamakin girman tane haka ta koma wata babban mace da ita shekaran ki nawa yanzu a jami, a ?

    Bai samu kanshi wanan yinin ba balle ya tuna da zancen envelope din ba don haka har yamma bai san meke cikin envelope din nan don bai koma ta kanshi bama alokacin.

  Don yana raragewa kasuwa ya koma don ya saro wasu kayan da zai fita dasu da safe yakoyi sa,a ya samu an bude a gaban shi.

   Don haka dilace mai kyau na kayan maza ya samu giredi kamar anzabo mashi sune daga can ya taki sa,a matuka don yana zuwa ana bude dila saidai kudin shi basu kai ya saye dilan duka ba lokacin.

   Don haka ya zaba  tare da rokan mai kayan ya aje mai zuwa safe ko yamma zai dawo ya saye sauran ga baki daya .

  Mutumin yai shiru na dan lokaci kafin ya duba sabo da kwazon yaron yace amma idan bakai bane banayin haka gaskiya tunda inada masaya.

  Ida  har bakazo ba zuwa biyar zan sayar dasu duka gaskiya yana magana yana hada sauran kayan a wuri daya don ya adana mashi kada wani yazo ya dauka bai sani ba.

   Ya bashi kudin tare da godiya kan karancin da yayi mai saboda sabo da juna da sukayi ya dauko kayan shi zuwa inda zai samu abin hawa da zai kaishi unguwarsu.

   Da kayan shi niki niki ya shigo bai tsaya ba sai kofan dakin Dije data riga ta tayar da sallah magariba a lokaci  shima buta ya dauka ya fara alwala kada ya rasa jam,i.

   Bai dawo gidan ba sai yamma lis ya dawo duk a gajiye yake sosai a lokacin hakan bai hana shi zuwa wurin uwar garke dake kwance ba ita da yayan ta..   

   Duban abin abincin su yayi babu komai a cikin kwanon haka yasa ya fita gidan ba tare da sanin Dije ba yaje gidan da ake sayar da abincin dabbobi unguwar don ya sayo masu.

   Dije wace taji shigowan shi gidan saidai bata karajin motsin shi ba a zatonta yana dakin shi yana hada kaya ta fito tana magana taji shiru.

   Yau ga ja,iri kafita ne koka kewaya ban dakine wai ita kadai take maganan a tsakar gida sai gashi ya bullo a cikin duhu har saida ta dan kadu dan ganin shi a lokacin.

   Tambaya yayi lafiya kike nan a tsaye cikin duhu wai kai na fito nema naji motsin ka kuma nazo naji shiru ashema kana waje.

   Naje nan gidan malu ce na karbowa dabbobin nan abinci don naga basu da abinci saidai dusan gwaunatice na samu na gargajiyan ya kare tace.

   Dadina dakai Amadi akwai kula duk da wanan gajiyan daka kwaso bai hana ka tuna da bayin Allah nan ba a ranka Dije dole mu kula dasu tunda mun turkesu a wuri daya idan bamu basu abinci ba sai Allah ya tambayemu hakkin su akan mu.

    Yana bata amsa ya duka yana zubawa dabbobin abinci kafin yakai hannu ga uwar garke yana fadin uwar garke tashi kiyi kiwo kada ki kwana da yunwa kinji kuci sai na sayo maku haki gobe insha Allahu.

    Zakace da mutane yake wanan maganan yadda dabbobin suka mike suka fara kiwo lokaci guda abin shan ruwan su ya dauka ya daure guntun jarkan da aka yanke ana zuba masu ruwan sha a ciki yaje har randan ruwan su ya debo ruwa lokacin ya farga da basu sa ruwa a gidan ashe.

    Yana gamawa da dabbobin ruwa ya fara diban masu yana cika kayan zuba ruwan Dije duk ya samu ya cika don ya samu ba mutane sosai wurin ruwan.

    Sai goma da wani abu ya samu kanshi ya sauya kayan jikinshi ya nufo dakin Dije wace ke shirin kwanciya hannu dauke da takardan da yarinyar nan da sunan gidan su ya sani na MAYANA.

    Zama yayi yana bude takardan don ganin meke ciki kudine suka zobo daga cikin takardan zuwa jikin shi sabi dasu kar saida ya dan kadu da ganin hakan.

    Kai din da yace yasa Dije juyowa inda yake tana kalloshi idonta ya sauka saman kudin da yake tattarawa a jikinshi.

   Amadi ina kafito da wanan kudin sabbi haka kar dasu tana tambaya take tsureshi da ido a cikin tsaro da son jin ina ya fito da wa yan nan kudin masu yawa.

  Bai dago kaiba don tsayawa da yayi kidaya kudin dubu darine cif din su a mike dinsu suna daukan ido tambaya ta jefo mai da ina kafito da wanan kudin Amadi ?

   Wallahi Dije ina wanan yarinyar da matar nan tazo gidan nan karbawa magani wurin malam tanimu ranan to itace dazun ta bani shi tace don Allah na karba kada in bude sai nazo gida.

  Nina dauka ma wani takardan wani abune a ciki ai ashe kudine ta saka haka a cikin takardan nan ta bani har tana fadim nayi hakkuri dashi don Allah.

   Amadi kudi lafiya mace ce zata baka kudi haka kuma yarinya karama kadafa ta jawo muna matsala muna zaune kalau a yanzu ?

 

No comments