Breaking News

TUMFAFIYA 14

 

 


  Na sayar da wanan labarin don Allah kada wani ko wata yayi audiovisual din labarin nan don Allah yin hakan taka dokane.

   Duk da akwai matsala a tsakani  mama da ummah sai nayi mamakin ganin ai ummahce mai dawainiya da bakin mama din kuma da duk wani abinda zasici zasu sha daga wirin umma yake fitowa .

   Naso nayi wanan tambaya  saida ba fuskan yin hakan gareni naja bakina nayi shiru  ina kallon su a fakaice don nikan washe gari tun safe na fita zuwa school ban dawo ba sai shidda na yamma na iso gida.

   A wajen gidan mu na samu su Dele sun fito shan iska har na karaso cikin gidan na aje mota idonsu yana kaina gashi naki jin hakan a rayuwana mutum ya kura min ido ba daukewa.

    Naso sharesu amma ganin hakan ba zai yuyu gareni ba yasa dana fito na nufi inda suke zaune din don na gaidasu.

   Tun kan na karaso kabir kanin Dele ke fadin wow what a beautiful car is this sister kunyi kyau dake da motar taki baki daya so wanan ce motar da mami jafar ke fadin an saya maki dama ba a saiwa su Aisha ba gaskiya motar nada kyau sosai wallahi.

    Nagode na fada kafin na dago kai wurin Dele ina gaidashi ya amsa min cikin dan nisawa yana gyara zaman shi tare da fadin kin dawo ashe nace eh ya sabon yanayi.

 Sai lokacin ya danyi murmushin gefe a fuskanshi yace ba matsala ina enjoyed din garin ai don weather din ku na da kyau sosai.

   Gaskiya yarinya daddy ku ya fito dake gari dole mamin jafar tace ojuju ku kaiwa daddy ku har ya sawo maki wanan mota haka mai tsada no warder ta kira mamin mu hankaki tashe tana kuka wai mamanki dake zaku karbe mata miji a hannun ta .

   Kabir dan uwan nasa ya fada a dake ya hade hannayen shi wuri daya bai motsa a yadda na sameshi ba sai idon daya zuba min kawai yana kallona kamar yaga photo.

   Kabir din ya juyo yana fadin is what they said, now aiba karya na fada ba brother ayi mata magana su gyara idan sun san sufada don kada suje su kaisu wurim babalawo ya halakasu a banza.

    Shit kasan sin din da kake aikatawa kuwa kabir kasan wanan yana iya jawo fitina kai meyasa kake shiga shirmen matane wai don Allah?

   Na fada maka idan kaji suna shirmen su ka daina kula balle ka dauka wani abu zai iya faruwa kawai dai shirmene na mata kawai suke fadin hakan.

  Nisawa nayi na gaida su suke tambayana daga ina nake nace school kabir bau dadara ba ya sake fadin lalai mami jafar saida dai tasa kikayi karatu a garin nan ke nan duk da daddy ku baiso hakaba.

   I don no why  wasu mata suke irin haka kan yayan mijin su meye laifin dan mijiki gareki ne wai da sukeyin wickedness akan yayan mazajen sune wai ?

   Murmushi na kakaro a fuskana tare da fadin har yanzu dai kana nan yadda kake ashe daba mutum dariya shima murmushin yayi tare da fadin.

   Kina ban tausayine a cikin su da kawai kizo mu koma lagos muyi zaman mu can ki kyalw kowa a nan zaifi amma idan that mumu Rukkaiya and Aisha suna ganin ki nan ba zasu bari a zauna lafiya ba And you know what ?

  Na girgiza kai yace don kifisu da komaine fa yasa sukejin haushin ki har mami Jafar din Zahar ya fada daga inda yake zaune na dago ido na kalleshi yace go inside.

    Cikin daure fuska nasan halinshi shiru shirune sosai shi baya da yawan magana sosai gashi bai iya bacin rai ba don dukkan su nasan halinsu tun ina karama dama kabir abokin wasanane idan mun hadu dashi.

   Saidai yanzu dana girma na rage irin sakewan da nakeyi dasu a baya can don yanzu hankali yazo min na gane cewa su din ba muharamina bane yanzu.

   Don hakane ban iya sakin jikina dasu a yanzu jin hakan danayi daga bakin Dele yasa na juya kawai na shige ciki abina na barsu wurin.

   Ina shiga ina jiyo hayaniyar su mama a part din su da alama dai akwai bakin da sukazo masu don gaida mami din da zuwa ke nan lokacin.

   Part din mu nashiga ummah tana zaune ita kadai a falon nayi sallama ta amsa na karasa ina gaida ita da tayi min ya karatun nace alhamdullahi.

   Har na juya zan shige naji tana fadin kinga su kabir kuwa da dan uwanshi a nan yau suka wuni zaune tun zuwan su gaidani basu

 sameki ba suka zauna na  basu dade da fita ba ai.

   Suna waje zaune na juyo ina bata amsa na shige ciki don zuciyana tayi nisa ga tsoron abinda naji a bakin kabir din kan zancen motana idan nayi tunane dakyau mami Dele tazone kan kiran gagawan da mama tayi mata ke nan a yanzu.

   Dama nasani ko a baya idan sun samu wani matsala da Abban mu idan naje hutu wanda a yanzu na tuno da hakan bai wuce kan zancena zasu samu baraka dashi sai mami Dele din tazo zasu shige daki su dade a ciki karshe ma su gice gidan tare sai dare sosai mama take dawowa.

    Don akwai wani zuwa da nayi hutu lagos din datun wanan lokacin zuwa hutun ya fara fita raina abinda ya faru shine da lokacin komawana yayi ranan muna cin abinci Abba ke fadin .

    Maamah tunda zaki koma

 sai yayan ki musa ya kaiki shopping ki zabi duk abinda ranki keso ke na  ko kai musa gobe ka fita da ita sai ka sayo mata duk abinda take so a nan.

   Ai kafin Abba ya rufe baki mama tayi cikin shi tana fadin na fadama banson hakana wani sayayya za ai mata kome ta rasa yanzu da za aje kashe mata kudi kuma?

   Can inda suke zaune da uwarta ba a sai masu abune halan tunda duk zuwa ina ganinta da sabbin kaya ai kai haba maimuna yanzu yarinya tazo maki hutu tayi wata daya amma ki bari ta koma haka ba komai daga nan.

   Mikewa nayi na bar wurin don ganin kaina ana son samun matsala ga ya musa ya fara fadin haba mama su wa yan nan da ake sayawa fa da cewa su Aisha.

   Sai ita datazo maku hutu dan sayayyan da za ai mata kuma shine zai zama matsala yanzu kuma haba dai mama idan hakane ai sai ta bar zuwa hutun tunda zuwan ta duk zata tafi sai an samu matsala irin haka.

    Fada sosai mama ta fara yiwa ya musa din yasa na tashi daga wurin cin abincin zuwa sakin kwanan amma ina jin muryoyin su cikin fada sosai daga dakin.

   Karshe shine naga mami Dele tazo gidan sun dade da mama kuma suka fita saya  tsaraban da Abba bai mun ba ke nan haka na dawo tun wanan karon naji zancen mama ya fara fita min zuciya.

   Na shiga part din mu da sallama ummah tana zaune ita kadai a afalo nayi sallama na shigo ina gaida ita da gida ta amsa min kamar a cikin damuwa.

   Yadda nake mata kallon tuhuma yasa tace dani ki shiga ki cire kayan nan kifito kici abinci na amsa da to ummah na nufi hanyar shiga dakunan kwanan mu.

   Muryan umma din ya

 dakatar dani na tsaya tana fadin kinga su Kabir a waje ne nace eh umma suna waje tace ai tun karfe daya suna nan sun shigo su gaidani suke tambayanki nace kin tafi school.

   Shine suka zauna nan din abincin safema a nan suka karya saidai na ranane gashi nan na aje masu basu dawoba ko sunci a can ne ban sani ba  ?

    Suna waje ummah yanzun muka gaisa dasu na fada nasa kai na shige dakina dogon riga na saka baka a jikina sai dan kwalinshi dana daura a kaina nasaka plat shoes dina na zaman gida wanda iya cikin part din mu nake yawo dashi na fito zuwa falo.

    Dining na nufa don ban samu ummah inda na barta ba da zan shiga abinci na bude naga sallon girkin na bakine wanan ke nan ko yau din ummah ce ta girka masu abincin na fada a raina.

   Abincin na fara zubawa a cikin plate a daidai lokacin kuma naji sallaman Dele cikin muryan nan nasa mai sanyi haka yasani dagowa ina amsawa.

  Yana gaba kabir yana bayan shi kai tsaye dining din suka nufo yaja kujera daya ya zauna a sanyaye shima dan uwan nasa yaja yakai zaune kamar wanda ke a galabance dashi.

  Kallo juna mukayi nida kabir din muka sakewa juna murmushi lokaci guda yace miko masa wanan ya fara cin wanan da kika zuba sai ki zubo muci tareni .

   Ido na fito dashi nace naci abinci da kai kato da kai ai sai kasa a dakeni yau ya dago fuska a daure yana fadin nine kato ko wanan yana nuna dan uwanshi gareni.

   Kaidaine kato amma ai shi yayanane don haka nake girmamashi ko yaushe saboda ya dauki girma na kuma sayar mai oh really nace yes ina aje plate din abincin dana sa komai a gaban Dele din.

    Na juya na fara zubawa a cikkn wani inda nakesa komai a wadace don nasan yana da ci sosai a baya ina ajewa yace oya zauna tare zamuci ba wasa nakeyi ba.

   Dole na zauna muka soma ci tare sai santi yake zubawa wai gaskiya ummah ta iya girki sosai yayin da nake kara lodamai abinci dana sha sai fira yake zuba muna dan uwan nasa na shiru.

   A haka Rukkaiya ta shigo ta sameni dasu take fadin wai ana kiransu Dele din gasu nan zuwa idan sun gama cin abinci ta juya ta koma part din su.

  Tana fita kabir yace kinsan me na tsani wanan yarinyar wallahi sjn faye gulma da sa ido yanzu wanan fita da tayi zataje tayi amebo akanshine.

    Dariya nayi yace gaskiya nake fada nace yan uwana ba haka suke ba kaima ka sani kawai dai baka ra,ayjnsune kawai yasa ka fadi hakan.

  Mikewa Dele yayi wanda shima yasa shi mikewan yana bin bayan dan uwan nasa a kofa suka hade da Aisha data biyosu ranta bace.

    Duk yadda yaso ranan  mu hadu bai samu hakan ba don bubuwa gaba daya sun rikemai a ranan saboda test din da suka shiga mai zafi kodaya fito ya samu motana baya wajen yasa shi komawa ciki.

   Zuciyar shi ta bashi shawaran ya nemi number na ya kirani haka kawai zaiyi ya samuyin magana dani yadda yake so son so yake yaja min kunnem yin hakan saidai yasan a fili ba zai iya yin hakan ba gareni don yana kallon narkankun idanuna yasan zasu rikitar dashine lokaci guda.

    Zai iya cewa yana hanin mata kyawawa da zarra irina mata amma bai taba haduwa da macen data rikitashi ba lokaci daya irin hakan.

   Yasan dai bai isa ya nuna so ko shakuwa a inda Allah bai kaishi ba haka kuma shi bai isa yakai ko matsayin drivern gidan su ba ko mai ban ruwa gidansu ba yadda yaji mutane suna fadan irin arzikin gidan mayana din a gari.

   Shawaran zuwa department din mu yayi ko zai ga abokan karatuna hakan yasa ya juya da sauri zuwa hanyar shiga building din suka hade da hannatu a kofan wace ke fitowa don zuwa gidan lokacin.

   Tana ganin shi ta fara sake murmushi a fuskanta lokaci guda tare da fara gaidashi tana fadin master kayi wuyan gani fa ashe ka shigo yau bamu sani ba gashi harsu zarah sun wuce gida tunda muka fito dazun tace yau suna da baki a gidansu don haka ta koma gida da wuri yau din.

   Don Allah ko kina da lambata ki kira min ita akwai sakon da zan batane eh to nima dai na dauki lambatane a wayan ta bata sani ba amma dai gashi tasa hannu tana ciro wayan nata daga cikin jakkarta na hannu ta fara duba wayan can ta miko mai tana fadin ga layin nata akwai kudi a ciki dazun ta saya min kati.

   Kai wanan ta faye surutun tsiya wallahi haka ya nasa a zuciyar shi yana karban wayan a hannunta sunan ZARAH MAYANA yagani da manyan harufa.

    Danna kira yayi sunan ya shiga saiga wayan na ringing a daidai lokacin ina kwashe kayan da mukaci abincin dashi da sauri na aje tarim plates din dana dauka zankai kitchen.

   Bakon number nagani na tsaya ina mamaki ciki  tsoro nakai kunnena a lokacin naji muryan namiji yana kwada min sallama.

   Daga wayan nayi ina mamaki naji muryan hannatu na fadin zarah nice coursemate din ki master ke son magana dake na kiraki master na fada cikin mamaki sai naji sallaman namiji.

    Amsawa nayi yace OK dama naso ganjn ki yau ashe kin shigo har kin fita ban sani ba muna ciki munayin test bamu fito da wuri ba.

  Saisai dama akan wanan sakon da kika ban jiyane a cikin envelope naso muyi magana dake don ban san ko kudin meye haka kika bani ba ?

   No kayi amfani dashi kawai na bakane kawai nagode sai anjima zaiyi magana nace kaba hannatu na fada a karshe na hana dama  yin magana a gaban hannutu din ko godiya.

    Hello Zarah kina lafiya kalau na fada a gajerce har yanzu kina school ke nan ashe tace yanzun nan fitowana daga class ke nan zantafi.

  Ok saida safe na fada na kashe wayan lokaci guda na mika hannuna na kwashi plates din abincin zuwa kitchen daga nan na koma dakina.

   Ba matsala ko Hannatu dake kallon shi ta tambayeshi ganin yadda yanayin fuskanshi ya sauya lokaci daya a wurin duk da bataji ko akan me mukai magana ba a lokacin.

    Hostel din maza ya nufa bayan sun rabu da Hannatu din don ya yawata ko kayan zasu shiga nan aka kewayeshi sai gashi kayan sun samu shiga har wasu basu samu ba a wurin.

   Haka yasa yai masu alkawarin zai kawo masu in sha Allah,  kudin shi mina mina ya kirga sai bakin titi ya hau mashin zuwa kasuwa  inda zai kara saro wasu ya kuma cika alkawarin daya dauka din wa mai kaya .

    Tun kan ya sauka mai kayan ya hangoshi ya fara washe baki don lokacin daya bashi ma bai karasa cika ba ya dawo suka gaisa dashi yace har sun shiga ke nan yace kaya sunyi kasuwa sosai wallahi.

    Nan ya mike ya jawo wanda ya boye mai da farko yana fadin kaga wasu yau aka kawosu sai ka hada dasu zasu shiga sosai wanan  mata da maza duk  zasuyi saya sosai idan sin gani.

   Zuciyar shice ta bashi shawara yayi amfani da wanan kudin kawai tunda nace na bashi su koda daga baya zai zauna dani muyi magana a kansu.

    A take ya biya kudin kayan gabaki daya yana gyaran kayan mutumin ke fadin daukan kayan nan yayima yawa da zaka daure ka samu tsohuwar mashin ka saya sai kaji dadin yawatawa da kayan nan zaifima sauki sosai.

    In,sha Allahu ina da niyar yin hakan nan gaba amma ba yanzu ba sai kudin sun kara kauri nan zuwa gaba dai sai nasa cigiya in saye don kayan sun fara min nauyi a kai haka.

    Ya baro kasuwa zuwa gida da kayansa niki niki yana hanyane ya tuna da alkawarin da tayi na sayowa dabbobin su abinci kaya kawai ya aje daga kofan yace mai mashi din ya koma dashi .

   Jin motsin shi da uwargarke tayine yasa ta mike ta fara kuka sosai lokaci guda kuna na tashin hankali har saida Dije dake daki ta fito hankali a tashe zuwa wurim garken nasu tana duban su.

   Kofan shigowa gidan uwar garke ke kallo tana kuka sosai sai hakan ya dagawa Dije hankali ta nufi hanyar fita wajen gidan sai kuma taci karo da kumshin kayan shi a ta cikim gidan .

   Mamakine ya kama Dijen lokaci guda ita daya take magana dama Amadi ya dawone ashe ko kuwa kayan a nan ya barsu ya tafi ?

     Lekawa tayi ba kowa wajen gidan sai yan mutanen dake gittaya jefi jefi a layin can ta hangoshi tafe ya sayowa dabbobin haki da dusa yana sauka saman mashin yana tambayanta ko lafiya ?

No comments