Breaking News

TUMFAFIYA 25

 

 


 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH  ,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

2️⃣5️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

 

 Ki daure ki biya ba tare da shiga hakkin wasu ba yar uwa zaki karu na karu har wasuma su karu damu.

    Eh Dije ina son jin kudin mota zuwa can ne don naji idan nisa ko yawan kudin mota ya hana mahaifina zuwa ya dubani har wanan lokacin na kuma san shin yana raye ya watsar dani haka na zama mara gata a cikin garin mutane ko wani dalili zai ban nayin hakan dani.

   Amadi meye damuwan ka ga hakan yanzu don ibrahim ya tafi ya barmu da kai hakan ya hanaka rayuwane a duniya ba komai yasa yai muna hakan ba sai kawai don muki yarda da bukatanshi na rafiya da mahaifiyanka can kasar tasu.

       Yanzu Dije da kuka hanashi tafiya da inna a wancan lokacin yau ina innan take ?

   Amadi auren ta da dan gida yafi muna kwanciyan hankali don ko banza dai munajin labarinta ai jefi jefi kuma nan da can din inda take zamu iya yinshi a cikjn wuni daya mu isa gareta.

   Humm Dije ke nan yana fadin hakan ya girgiza kai kawai ya juya ya nufi dan dakin da yake kwana a cikinsa ya turo kofan bayan ya shiga da karfi ta tsaya tana kallon kofan dakin dake makwabtaka da kofan gidansu.

   Magana ta farayi ita kadai a bakin murhun da take aiki abinda kowa ya gujewa yarinyar nan ke nan tunfarko da auren bako.

   Amma dan uwan ubanta ya tsaya ya kafe cewa tunda shi din musulmine da uwan mu kuma tana so yana so gara kawai a hadasu ai matar mutum kabarisane.

    Yau me gari ya waya a hakan da yake mayaudarine yaso cuta bai tashi cewa zai koma gida ba gaban iyayyen shi saida yaga sun samu rabo a tsakanin su ya bijirowa mutane da zancen barin gari.

   Ina zan yarda ya tafi min da ya wani uwar duniya can me nisa da kowa ka tambaya yace ma bai taba zuwa ba yana dai jin sunan garin a bakin mutanene kawaishi.

   Wama ya sani ko shi din wani halin banza ke gareshi dama ya baro gida yazo nan ko kuma ya dauketa yaje ya sayar irin haka anyi sunfi goma muna ji a jakkar mogori ana fada.

   Har dije ta rarage aikin nata bata bar wanan jininin da takeyi ba ita kadai a tsakar gidan nata kamar tababa sai yankan fada takeyi.

   Yan dabbobinta na gefe tsaye sunyi shiru suna kallonta kamar mutane suna  saurarenta dan ko motsi basayi a lokacin sai gidan da yayi tsit lokaci guda.

     Kwana hudu ke nan da sallah amma gidan namu babu dadin zama ga iyayyen mu don haka fitama a lokacin baida dadi ga kowa dama can ni din ba ma,abociyar yin hakan bane.

   Dan dama lokacin da muka dawo sabo sabo garin muna dasawa da mama a lokacin idan na dawo daga school naci abinci zandan je part din ta mu danyi hira da ita.

  Sai na fahinci yin hakan wani hanyane da mama din kanyi amfani dashi wurin zolayana taji wani abu game da ummah na saina daina yawan shigan har haka yazo ya faru yanzu.

   Don yanzu saidai idan mun hadu zan gaida ita kota amsa min ko kuma ta kyaleni saidai hakan baisa na fasa gaida ita din ba .

   Wanka nayi na shirya don tun ranan sallah da nayi kwalliyan sallah din ban kara saka sabbin tufafina da ummah ta tura kudi har Abuja aka dinko min su ba ina kwance ina fama da dogayen riguna irin na shan iskan zaman gida.

   Abba ma dukda suna garin ban sakashi a idona ba tin ranan da yai min fada din nan tace kuma in turo mashi Ahmed idan nafita.

   Sai yau da korafin ummah dake yawan min fada kan rashin zuwa nagaida mutane yasa na shirya tunda safe na fito dakinta na fara zuwa nagaida ita da kwana.

  Kafin na dago na fita zuwa part din mama da nayi sa,a tana falo zaune da yaranta yanayin su kawai zaka kalla kasan wani abu mai muhinmanci suke tataunawa a tsakaninsu.

   Dagani fitowan dole tayi lokacin zuwa falon nata ta zauna tana saye da hijjab mai ruwan makuba har kasa suma yaran da hijjaban su sun dunkule sama  kujera.

   Nayi sallama a kofa suka kalloni na karaso har inda mama din take zaune na dan rage tsawo na gaida ita ta amsa a cikin irin izzanta na manyan mata.

  Tare da fadin yau an tuna da gaisuwan ke nan ko dan kuya ya kamani nace kiyi hakkuri mama kwana biyu ina daki bana jin dadine sosai.

  Na juya wirin yan uwana da suka kyaleni nace ina kwanan ku lafiya kawai suka amsa min dashi suna kawar dakai ga kallona lokaci guda.

   Na juya zan fita muryan mamane ya dakatar dani tana fadin Zahra kuna dai ganin irin cin fuskan da mahaifin ku ke muna a gidan nan yanzu don yayi sabon aure ko ?

   Mamah Aisha ta fada daga inda take zaune tana jan tsuki ta kawar da kanta gefe daya ta nuna bata so uwar ta fito min da zancen ba a lokacin .

    Dan dawowa nayi ina fadin mama kuyi hakkuri ku barshi kome yayi shida Allah don Abba ba yaro bane yasan abinda ya kamata da wanda bai kamata ba.

   Ita kuma idan tazo maku da wata manufane donta musguna maku kanta hakan zai koma watarana don Allah bai yafe hakkin wani kan wani.

    Shiru tayi nasan don diyanta da suka nuna basu so tafito min da zancen ba wanda ni kuma nasan damuwa ne ya saka mama yin wanan zancen dani a ranan .

   Na dan tsaya nayi jim don narasa abinda zan fada bayan hakan don ban saba irin maganganun nan tsakanina da ummah na ba yasa naji abin bambarakwai sai wanan amsan Allah yaban ikon in bata a lokacin.

 Allah ya sauwaka na fada naja kafata zan fita koda ban waigo na dubaba nasan cewa tsukin Aishace mama waida wanan banzan zakiyi wanan maganan kome ?

    Ni dai na fice na basu wuri dakin mommy na nufa yana rufe na kwankwasa sai wanan matarce a ciki muka gaisa take fada min cewa tana part din Abban mu na nufi can din don mu gaisa dasu da kwana.

    Suna zaune suna karyawa a dining nayi sallama suka amsa min na shigo suka kalloni nakai gurfane Abba na fara gayarwa sai ita saidai Abban tunda ya amsa min bai kara kallon inda nake ba sai ita ke fadin.

   Dama kina gidan nan na daina ganin ki ko part din ku na shiga nadan murmusa kadan tare da fadin ina nan mommy yanzu na fito part dinki akace kina nan.

   Daughter ke nan ko fushi kikeyi da kowa a gidan a, a nace da sauri lokaci guda don tsoron Abba dake wurin kuma banso ta furta hakan ba gareni.

    Yaushe zakuyi hutune nace nan da one month in sha Allah OK zan turo a daukeki zuwa Abuja daga can zamu tafi buki gidan mu autan mu zaiyi aure.

   Kallon Abba nayi da sauri don sanin ba zai yarda da hakan ba shima sai ta juya tana fadin Alh kaji na rokawa daughter tare da ita zamuyi wanan tafiyan idan lokaci yayi.

   Ba ruwana da zancen ta yanzu tunda bata jin magana ta a yanzu har zahra ce zata fara soyayya da wanan yaron da baida asali baida sana,an yi takamaimai ko wani jigo mai karfi don kawai ta bata min sunan iyalina a gari gaba daya kallon Abban mukayi lokaci guda.

   Idona ne ya kawo hawaye lokaci guda don jin abinda Abba ya fada game dani din sai naji tace daga inda take zaune ina wanan zancen anyishi ya wuce ko, Alh bai kamata kana kara tayar da zancen ba a yanzu kuma.

  Ya juyo da kyau yana fuskantana tare da min kallon ido da ido yafara fadin kuma ki sani duk na kara jin cewa kin kara kula wanan yaron nan saina saba maki a gidan nan  .

   Kasa nayi da kaina kafin na iya budan baki da kyar ina fadin kayi hakkuri Abba niba soyayya nakeyi dashi ba dama muna mutuncine dashi kawai a makaranta don taimakona da yayi ranan da kowa ya gudu a wurina da ciwona ya tashi sai ya kawo min taimako tun wanan ranan muke gaisuwan mutuci dashi.

   A zatona kamar jikin Abba din ne yayi sanyi a lokacin amma sai naji yace koma meye na fada maki bana son in kara ganin kuna hurda dashi  again don yaron bakma kwanta min a raina ba.

   Jeki daughter zamuyi maganan dake daga baya zan shigo part din ku in sameki hjy karima din ta fada da sauri na mike zuwa waje kafin nakai part din mu kukan da nake rikewa yaki tsaya min dole da kuka na shigo part din namu.

    Kallona umma da kannena da sukai cirko cirko suna min kallon mamaki dakina na nufa ban tsaya gun ummah ba don nasan hakan kara min wani laifin zaiyi kuma.

   Gado na fada na fara kuka ina hadiyan zuciya kafin can na mike zuwa bandaki na wanko fuskana na dawo na kara hayewa saman gadon na zauna ina faman tunanen abubuwa da dama a zuciyana.

  Kofa aka turo azatona ummace  ta shigo dakin don ban dago kai na duba wanda ke shigowa dakin ba lokacin muryan Tani naji a kaina tana fadin .

   Haba uwar dakina meyayi zafi haka zaki kulle kanki a daki kina kuka haka kome yayi zafi hakkurine maganin shi kibi umurnin iyayye a zauna lafiya yadda suke son .

  Don jayayya dasu baida amfani wani lokacin don abinda babba ya hango yaro baya hango hakan don haka shawaran da zan baki shine kibi umurninsu a yanzu kiyi yadda suka amince maki dayi sai komai ya wuce a tsakanin ku.

   Yanzu share hawayen ki barin kawo maki abin karyawa ki karya saiki sake jiki ki nuna komai ya wuce a wurin ki koma kamar kowa a gidan nan.

    Don kinsan dama hakan akeso aga kin samu matsala da mahaufin ki shine farin cikin wasu gidan nan ki nuna masu cewa ke din mai tarbiyace da bin umurnin iyayyenki.

    Maza ki mike ki saki jikin ki kada ki yarda mahaifinki ya wuce da fushin ki a zuciyarki nan zan kawo maki ko falo zan kai maki abincin naki ?

   Da kyat na iya budan bakina da yai nauyi lokacin nace a barshi zan fito falo in karya a nan na fada mata ta juya zata fita nace nagode tace kai ba komai uwardakina ai muna tare ina bayan ki har kullun don mu hjy tayi muna komai wallahi dolene mugani ko mu maganta a zancen.

    Ta fita na sauke ajiyan zuciya ina tunane don a gaskiya ba zance ga dalilin kukana ba saidai abinda nasani shine yin hakan da Abba yai min a yanzu zai iya jawo min matsala a karatuna nishi nake ganin dalilin damuwana a lokacin.

     Mikewa nayi daga zaune din na nufi falo kai tsaye wurin daning na nufa tun kan nakai zaune kannena suka rufa min da taimakon hiran da suke min har na samu na dan sake .

  A wurin Abban mu ya sameni zaune muna hira da yan uwana suna ganin shi suka nufeshi suna fadin yaushe za,a kawo muna keken mu.

    Daga inda nake zaune nake fadin welcome Abba ya amsa min yake fadawa yaran cewa yau idan na koma zan sayo maku na aiko maku dashi.

    Hakan yasa na fahinci cewa a rana  zasu koma ke nan ashe bedroom din ummah ya nufa yaran suka dare don ba mai shiga idan Abba din ya shiga nan din.

   Muna zaune tare dasu suna murna ya dan jima sai gashi ya fito daga dakin a tsakiyan falo ya tsaya yace maamah zo nan na taso da sauri daga inda nake din zaune nazo na sameshi tare da dan rage tsayina gareshi .

   Hannuna ya riko ya dagoni ya fara fadin ki kula da kanki  mamana bana son yawan shiririta ki natsu kiyi karatu yadda ya dace kamar kowa ni da kaina zan zaba maki abinda ya dace dake in sha Allahu.

    Na amsa da to Abba na gode in sha Allahu zan kiyayye ka yafe min abinda kake zaton inayi a bayan ka wallahi Abba hakan ba gaskiya bane.

  Is OK ya fada yasa hannu a aljihunshi ya ciro kudi masu yawa ya miko min yana fadin ki kula na fada maki ga wanan ki mayar da hankalin ki sosai abinda baki dashi ki kirani ko ki fadawa Hjy salma ta fada min.

    Nagode Abba na fada yace wa kannena suzo suka taho yake binsu yana sallama haka muka rako shi har kofan part din mu don ya nufi part din mama yasa muka tsaya a nan muna masa Allah ya tsare.

    Koda muka juyo zuwa ciki ummah ta fito falo a lokacin nan yaran suka rufeta da fadin Abba ya bamu kudi ummah tace kun gode ai na  muka fara mika mata kudin an kawo kaina tace ki rike naki a hannun ki tunda ba tambayana kudi kikeyi ba.

   Sallaman mommy ce hjy karima ta shigo da fara,a a fuskanta tasha kwaliya sosai a jikinta tana fadin to uwargida rangida mu zamuyi maku ta baki fa don Allah a gafarce mu.

    Tare suka shigo da wanan matar suna sallama ummah din kafin ummah ta kakaro murmushi a fuskanta tana fadin muma ai ku gafarce mu zaku juya ke nan yau ashe ?

  To ba dole ba tunda kun hana mu zama  lafiya a nan din kunce bamuyi daidai ba ai dole mu juya kada azo rayuka suna baci a banza ni wanan matar da ace garin nan nake zaune tare da ita da mun kwashi yan kallo a tsakanin mu kullun.

  Mace haka ba tsoron Allah sam a zuciyarta sai son kai da son zuciya kamar kowa ba mutane bane sai ita ai bata cika yar sheri ba tunda harta kasa hanashi kara aure takuma zauna da kishiyoyi aishe bata isa ba ke nan ?

  Murmushi ummah ta kara sakewa tare da kallon matar da suke tare tana fadin baabba zaku koma ke nan ashe yaune tafiyan naku ?

   Gashi dan tsaraba ba a hada maki ba zaki tafi hannu sake babu komai wallahi ko wanan fuskan da muka samu ai kin bamu komai sai kuma wani lokacin idan Allah ya kaimu.

   Aita hakkuri kiji yar nan me hakkuri shike da riba wata rana in sha Allahu wata rana sai labari haka rayuwa take wani lokaci ga bawa mai tawakkali da Allah.

   Nagode baabba ummah ta fada ta mika hannu ta dauko wani leda da tun shigowan mu yake aje a gefenta tana fadin hjy karima ga wanan a rikawa baabba ba yawa bamu sanda tafiyan ku ba yau ban hada mata komai ba.

    Kai haba dai ba zamu karbi komai naki ba gaskiya haba dai bafa ke nabawa ba baabban mu nabawa don haka ki bar zancen nan don Allah.

   Gaskiya ni banda bakin magana don ko hakan ai mun gode da karamcin ki garemu Allah ya kara bamu hakkurin zama tsohuwar ta amsa da amin.

    Hjy kariman tace to ni ina skn naje nayiwa wanan sallama bansan da wani ido kuma zata tarbeni ba a yau don idan tayi min ba kyaleta zanyi ba.

  A,a a rabu a gana alherine kada ki biyewa wanan aikin zama tare ne hakan don wanan zance ai ba kyaki zuwa kuyi sallama ba musanman ma ba da zata tafi.

   Ke ke nan kika san wanan din bari dai din muje sai munyi waya in sha Allahu kuma suka fara tafiya don barin falon kafin ta juyo tana fadin daughter sai na aiko ke nan ko nidai nayi murmushi kawai na mike na dan rakasu zuwa fita part din mu dagani har ummah muka juyo muka dawo.

    Hankalina na mayar ga tv da ake wani film din yara a cikin sa tani ce ta shigo tana fadin ashe yau zasu koma shike nan har sun tafi ?

    To meye a ciki yanzu bagashi sun juya sun tafi tare ba kuma ba a isa a hana hakan ba don kwanan ni wallahi suyi ta kwana bashine a gabana ba.

 Mazan nan da zaka mutu a kansu su kasa suma maka su wanan hauka hjy maimuna keyi tace wai bata yarda don sunzo nan din tare ta amshi girki ba tunda a can tare suke dashi.

   Yanzu kinga ya barta da kunya kuma girma ya zube kan abinda baikai bai kawo ba an tafi an barta da bacin rai da takaici ga banza.

    Ta dauka irin kine ai data saba takawa tana hawa yadda takeso a kullun tani ta fada yoni ina ruwana da wanan bakin haukan ?

   Hjy ke wake daka ta taki keda ke barin mutum da wutar shi ta konashi ai zama da irin ku yana da wuyan sha,ani sosai idan mutum bai gama ganeku ba.

    Ina zaune ina jin abinda suke fada gaba daya dana tattara sai na gane cewa abinda mama take son fada min ke nan da safe dana shiga wurinta yaranta suka hanata fada min komai.

  Koma meye matsalansu ce ta manya hakan don su hakan ya shafa ba zancen mu bane mu yara wanan maganan tasu.

  Mikewa nayi da niyar barin falon Tani ta kalleni tace dani uwar dakina komai ya wuce ke nan da alaman haka ?

   In ma bai wuce ba ai itabta sani yanzu da muka kyaleta da shirinta ba gashi abin ya koma a kanta ba an watse a baram baram tsakanin su sheri ai dan aikene dama.

   Nayi mamaki matuka da wanan zancen har yazamo hakan wani irin abune yaran nan basayi a garin nan amma saina wanan kawai aka gani a gidan nan har ya zamo min abin fade.

   Yanzun dai ai intana da hankali tagani ke nan  sai ta shiga hankalinta idan zata shiga don abin kulin sheri yanzu baida kadan ta dai rabu da yaron nan shima tunda har Alh ya iya kiranshi yayi mai warning nasan zai rabu da itane .

   Haba hjy ki rabu da aikin so yana da wuya ace an rabasu haka farat daya yadda kuke nufi din nan sai dai ku bisu da addua shine mafita don uwardakina tana da saukin kai sosai don gashi dan maganan da nayi mata dazun yasa ta sake harta fito yau din waje.

   Kuma fitowan ai ya zama mata alheri tunda uban ya shigo ya samu ra sake naga aisun shirya kafin su tafi hakan itama bai mata dadi ba yanzu ?

    Darene gabanin asubahi lokacin sanyi ya sauko kowa najin dadin sanyin masu ibada a lokacin suna jin dadin yanayin dije dake kwance tana barci a cikin yanayin da kowa keji ta fara mafalki.

    Sai dan juyi takeyi tana dan mutsutsuka kamar yarinya kafin ta mike zubur daga kwancen tana sakin salati lokaci guda tare da fadin Amadi ?

No comments