Breaking News

TUMFAFIYA 27

 

 


 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[1/25, 10:32 PM] +234 815 085 0067: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH  ,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

2️⃣7️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

 

Zahra lafiya kike kuwa meke damun kine yau zaki bar school da wuri haka don naga kin fito daga aji ana karatu zaki gida ?

   Wani irin faduwan gaba naji ya ziyarceni lokaci guda ga kunya kuma haka yasa na dan dauki lokaci ban iya juyowa na fuskance shi ba lokaci guda.

    Kafin na tattaro karfin halina na juyo tare da fadin ina wuni bana jin dadine yasa zanje gida yanzu nasha magani indan kwanta nagode sai anjima na fada da sauri na fada motana ina kokarin tayar da motan.

   Hannuna dake rawa na kasa saka key din motar da kyau yasa shi matsowa zuwa window motan yana fadin kina ko cikin hankalin ki zaki iya tukin motan a haka.

   Murmushin dole na zakulo a fuskana kamar makaryaciya nace meka gani zan iya mana a daidai lokacin motan ta tashi ban kalli inda yake ba sai horn nayi mai na barshi wurin yana bina da kallo har na bace mashi.

    Ajiyan zuciya ya sauke ya juya a hankali ya koma wurin da yafi yawan zama wasu lokuta inda a nan ne kuma muke haduwa muyi karatun dashi.

    Bai dade da zama wurin ba su munir suka sameshi gaisawa sukayi dashi manir ke fadin yau master da kanka karigamu isowa ajin ?

    Dan murmushin gefen fuska ya sake ba tare da yai magana ba don inda sabo a yanzu sun saba da hakan nasa na rashin magana wanda kuma a hakan har muka shaku da juna dashi kowan mu ba mai son yawan magana ba cikin mu.

   Sunyi karatun su na dan lokaci duk da sun gane karatun nasu yanzu akwai sauyi a cikinshi sosai don bai yawan nacewa wurin maimaita masu.

   Bayan sun gama an fara watsewane a wurin tana batun wucewa ya hada kayanshi hannatu ce taki tashi tana zaune ya dago ya kalleta yana fadin .

   Hannatu lafiya dai ko yana kallonta ta dan gyara zama tana kalllon shi tace Master magana nake son yi dakai akan zahra.

   Zahra ya ambaci sunan a cikin mamaki kafin ya dan kada kai yana sauke murmushi tare da fadin wani abu ya farune sai hannatun tace a,a master.

   Kasan dai zahra bata da sata abokiyar data fini school din nan kaf don haka ta fada min duk abinda ya faru a sallah break din nan da Daddysu yazo.

   Muyi magana ta fahinta na bata shawara a jiya akan zamu ganka yau mu baka hakkuri kan hakan sai gashi yau din ta tashi bata da lafiya don haka ta tafi gida tun dazun.

   Eh na ganta da zata tafi din nake tambayan ta ko lafiya zata koma gida wanan lokacin take fada min bata jin dadin jikintane.

   Ok ka ganta ke nan nasan  duk akan matsalan takune bata jin dadin jikinta amma master sai nake ganin kamar zakuyiwa kanku sakacin da zai dameku a baya.

  Akan me fa ya tambaya yana kallonta a cikin mamaki murmushi ta sauke a fuskanta tace haba master na dauka ai in kun boyewa kowa hakan ni ba zaku boye min ba don nasan abinda ke tsakanin ku yanzu dai.

   Meke tsakanin mu din banda abinda ke tsakanina dake shine karatu nan da mukeyi sun kuma ce ta daina yanzu shike nan kowa ya tsaya a matsayin shi ai.

   Nasan ni din ba ajinta bane don bankai matsayin tsayawa da yarinya irin zahra ba kema kin sani abinda kowa ya sani ne kuma don haka kada yanzu kema ki shiga cikin masu ma alakata da zahra din wani fassara na daban.

    Murmushi Hannatun ta sauke mekama da yake a fuskanta tace nawa akayi muka gani a garin nan matsala dai ko wani mahaifi da nasa kalan fahintane .

  Shi mahaifin zahra a nawa fahintar an kai masa zancen nakune ta baibai yasa ya hau haka ba tare da bincike ba a kai har ya yanke hukunci irin hakan a tsakanin ku.

   Hannatu na kula kina son jan zancen da nisa yanzu bayan an rigada an wuce wanan wurin ko nake gani yace na bar ko wani irin halaka da yarshi na kuma bari.

  Itama din ta bar hakan ba sai kowa ya tsaya matsayin shi ba yanzu kuma ke kanki kinsan hakan ban kai matsayin da zan zauna da zahra ba gaskiya kema kin sanda hakan.

  Ita zahran ai bata dauki haka  ba idan ka duba irin rayuwan ta na saukin kai a cikin mu sam bata nuna cewa mu din ba ajinta bane take tare damu.

  Ai akwai diyan attajirai irin ta masu jan aji cikin makarantan nan wasu ma basu ko kai matsayi irin nata ba amma suna ji da kansu cewa su din diyan wasu kusan garine su.

    Ni a ganina gaskiya ya kamata ku tsaya ku fahinci juna kai da Zahra tunda kuna son junan ku a yanzu kowa kuma yasan da hakan gareku.

    Haba hannutu ban zaci wannan zancen zaki zo min dashi ba a yanzu don da ban tsaya sauraren ki ba gaskiya mutumin nan yai min iyaka da yarshi fa tare da kakausan murya kan hakan.

   Itama yar nasa da alaman tabi umurnin mahaifin don haka kibar wanan zancen don Allah ta tafi hakana don gujewa matsala nan gaba kan hakan.

  Abu daya nasani shine idan naganta a cikin matsala zan iya taimaka mata final yana fadin hakan ya fara tafiya da niyar barin ta surin zaune yaji muryan ta na fadin.

   Saika shirya karban mumunan labari game da zahra don kuna kiris da jin abinda bashi ba a kanta nan da yan kwanaki kada  don hakan yanawa rayuwan zahra barazana a yanzu.

   Juyowa yayi da sauri yana kallon ta kafin ya bude baki yace me hakan ke nufi ke nan tace abinda idon ka ya gano maka dazun game da ita.

  Ban fahince ki ba hannatu kaje kayi tunane a kai ta bashi amsa ta mike ta bar wurin da sauri ya bita da kallon mamaki kafin shima yasamu ya daga kafanshi ya bar wurin cikin damuwa.

    Tunda na dawo na fadawa ummah banda lafiya ta ban magani tare da zaton ko ciwon kainane yake son tashi min har hayaki da shakawa duk saida ummah ta tsareni nayi.

  Kafin na shige dakina nayi sallah na kwanta sai barci mai nauyi ya daukeni ban falka ba sai karfe shidda da rabi da kyar na iya mikewa na shige ban daki na dauro alwala na fito.

   Ban daga ba saida nayi magariba da isha,i lokacin har ummah ta leko ta gani kona tashi daga barcin da nakeyi saita samu ina sallah.

    Abinci na fito naci tare da kannena na koma daki don jikina da ya danyi min nauyi a ranan wanka nayi nashirya kwanciya tareda karanto adduan kwanciya nakai kwance.

  Kamar ana jiran in kwanta a lokacin wayana ya danyi tsuwa alaman kira ya shigo saidai flashing ne kiran nayi mamakin hakan amma sai na zaci hannatu ce ke min hakan don itace me dabi,an flashing a kira.

   Bandaga inga mai mun kiran ba lokacin naci gaba da abinda nakeyi nakashe bedside lamp dina na lumshe idona a hankali.

   Amadi dake tsaye a kofan gidan su wanda dawowan shi ke nan unguwan tasu wuri  ujulanshi ya sake danna ma lambana kira karo na biyu gaban shi na faduwa sosai lokacin.

   Saidai kwarin gwiwan shine zancen su da hannatu don ya karkare wunin ranan da wanan zancen arashin da hannatu tace idan baison ya rasani yai wani abu don ina gab da salwanta rayuwana.

  Gashi basu samu tsayawa da ita yaji ma,anan fadin hakan ba tayi tafiyanta ta barshi da tunane a zuciyar shi wanan ya sakashi a cikin damuwa sosai a ranan .

  Don haka yaga dacewan ya kirani yaji meke faruwa saidaya danna kiran farkone yaga mezaice dani din bayan warning din da mahaifina yayi mai a kaina cikin kakausan murya da cin zarafi.

   Har ya juya zai shiga gidane wata zuciya tace dashi ya sake kirana ko zan dauka din zuciyan shi na bashi cewa anyi min kakausan warning a kanshi don yadda yagani a idona lokacin.

  Don hakane ya daure ya danna kira a wayan nawa yagani ko zan dauka in sauraren shi sai yaji kiran ya shiga saidai wayan yana ringing ban daga ba ga zuciyar shi sai bal bal yakeyi yana tsaye a cikin duhun unguwan shi kadai.

    Salamu Alaikum yaji daga bangarena cikin muryana mai sanyi ina mashi sallama hakan yasa ya gane banyi blocking din layin shi ba ashe kamar yadda ya zata.

    Ya amsa da wa,alaikis salam zahra ya jikin naki da sauki ko ya fada don bai san me zaice dani ba a lokacin sai yaji nace.

   Ohh master ne naji sauki wallahi nagode ya kake ya kaka a gaida ita kaka tana lafiya zataji ya fada a bangaren shi .

  Sai kuma mukai shiru na dan lokaci shi baiyi magana ba ni kuma ban kashe wayan tasa ba lokacin lokacin ina sauraren shi don ina gudun kashewa ya dauka wullakancine hakan .

   Saboda wanda ya kula da kai har yakira yaji lafiyan ka ya gama maka komai a rayuwa ai don hakane na jira naji har ya kashe ko kuma yana da abin fada min lokacin.

   Zahra!!! Duk da mahaifin ki yai min iyaka dake yace ni din da sana,ata da komai bankai matsayin koda sabulun wankanki banyi darajan shi ba balle nace zanyi soyayya dake a rayuwana ba.

  Duk da naso fadawa Alh cewa ni din ba wai soayya nake yi dake ba a lokacin zaman amana da mutunci mukeyi saidai daddy bai bani daman yin hakan ba gareshi.

   Yace ni din banda asali da arziki da zance zanyi mu,amula dake don matsayina baikai ga hakan ba saboda haka in rabu mashi da yarshi ko kuma yasa a wullakantani da kowa nawa a garin nan.

  Ido na runtse ina jin wani irin zafi a raina yayin da sautin muryan shi ke amayar min da zancen Abba na ranan gareshi don haka zahra kada ki dauka cewa na sherekine don son raina ko rashin damuwa da lamarin ki .

   Allah ya gani zahra ke haskene a cikin rayuwana don haduwa dake ya zamema rayuwana alheri a yanzu koda kon barni zahra ba zan taba mantawa da alherin ki gareni ba don kece kika haskawa rayuwana fitilan hanya madaidaiciya a yanzu haka.

   Enough Ahmed enough ka dauka cewa ba maiyiwa wani sai Allah a rayuwa  bayinshi anyi hakan ne don aga an hanani farin a rayuwana ko uwata tayi baki ciki kamar yadda akeson ganin mu kullun.

     Abu daya na sani na kuma rike har in ina son kane da gaske ba wanda ya isa ya hana wanan a tsakanin mu don kawai kai din baka nuna hakan bane na kuma san bashi mukeyi ba mutuncine kawai.

   Naja bayane kuma don nasan Abba ya saka muna ido don kada najawa rayuwan ka matsala kana gab da gama karatun ka a yanzu din don hakane banson najawo maka matsala.

    Murmushi naji yayi kafin ya sauke wani ajiyan zuciya da har nake jinshi yace zahra banda wani matsala indai a kankine duk abinda Abba zaisa amin idan har zan samu zuciyarki na dauki hakan a mukadarine a gareni kan samun ki.

    Idona na lumshe ina jin wani iri a zuciyana yaci gaba da fadin tsorana daya a yanzu shine kada na nace akan abinda zan dawo ina wahala daga baya kanshi ya kasance cewa ke baki min irin son da nake maki a zuciyana .

    Har yayi ya gama ban samu bakin fadan komai ba ina dai sauraren shi ga hawayen daya wanke min fuska ni kadai a daki ina tunane saida ya ji shirun yayi yawa yake fadin kina jina zahra ?

   Hello Zahra kina tare dani kuwa ko kin daukane na amsa da ina ji Ok kin fahinci me nake nufi kiyi hakkuri da hukuncin Abba a kan mu ba sai mun hadu bane alakan mu zai daure dake matukan waya yana aiki zamu iya gaisawa har zuwa lokacin da kika shirya hakan jin nayi shiru ba amsa yace

  Kina jina zahra nace naji idan mun hadu zamuyi maganan sai anjima na kashe wayan yabi wayan da kallo na dan lokaci kafin ya aje ajiyan da dan karfi ya fara kokarin tura wayan cikin aljihun shi.

   Daga kai yayi ya kalli hanyar daya ratsa ta gaban gidansu sai yan mutane dadaya ke wucewa a lokacin hakan yasa yasan dare ya fara dan nisa ya cire kafa ya daga da niyar shiga gida a lokacin Dije data gaji da zaman jiranshi ta leko daga cikin gida suka hade.

    Amadi lafiya yau kakai wanan lokacin baka dawo gida ba tana tambayan shi cikin nuna damuwanta gareshi a lokacin.

   Yanzun ba gani ba Dije, na dan tsaya yin wani abune a nan waje ai tundazun ina kofan gidan nan bandai shigo bane ciki ya bata amsa yana skn su shiga cikin gidan nasu.

   Amadi Dije ta ambaci sunanshi a sanyaye ya juyo yana kallonta tare da fahintar akwai wani abinda ke faruwa da tsohuwan zomu shiga ciki yace da ita ta fara takawa zuwa shiga cikin gidan nasu tabiyo bayan shi a baya.

    Kayan daya dauko ya fara ajewa kofan dakinshi kafin ya dago ya dan duba bayan shi har lokacin Dije tana biye dashi kamar jela.

  Muje daga ciki yunwa nake ji Dije banci komai yau tun wayewan gari sai kunun tsamiya danashi kafin na shiga makaranta.

No comments