Breaking News

TUMFAFIYA 31

 

 

 

 


ZAINAB IDRIS MAKAWA [2/2, 10:57 PM] +234 813 274 8094: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH  ,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

  3️⃣1️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

 

 Jin yawan kudin motar yasa ya fara budan ido yasan dole gari  da nisa sosai da nan din don sai a lokacin yaga kasadanshi na kamo hanya shi kadai zuwa wanan waje.

  Yanzu yake daya sani ya sanarwa Dije zancen tafiyan shi din duk da yasan cewa ba yarda da hakan Dijen zatayi ba.

    Amma a wanan tafiyan haka mai nisa ya kamata ace ya sanarwa Dije din kafin yazo ba wai ya kamo hanya haka shi kadai yazo ba yadda yayi din a yanzu.

   Sai Ido yake faman rarabawa yana kallon gari da ikon Allah gashi tunda ya bargida baiga wani idon sani daya sani ba a nan hakan yasakashi fara daya sani da ya hakkura ya zauna inda yafi wayau.

   Saidai a take wani zuciya yace dashi haba kamar kai ba namiji ba dai Ahmed haka zaka zauna ana ma gorin iyayye a cikin gari alhalin kana dasu raye.

  Waya sani ko mahaifin nawa baya raye yaba kanshi tambaya to ko baya raye dai zanga wasu nasan su su nasani suka tabbatar da ya haifeni a duniya.

   Duk da gajiyan dake jikin shi bai hanashi sakawa da kullawa ba a lokacin yana zaune a karshen mazaunin passengers ya kama haban shi da hannu guda .

   Wana  fitowan ba gudu baja da baya gareshi ko ta halin kaka so yake yaiwa kanshi gata a idon mutanen da yake rayuwa a cikin su duk da mutane da yawa sun sha sheda shiba shege bane.

  Da ubansa sabani ra,ayi kawai aka samu yai fushin zuciya bai juyo ga danshi ire iren haka kowa ke tofa albarkacin bakin shi a kai suna fadin iya sanin su kan matsalan nashi dashi yake ganin shi kadai ya shafa.

  Don hakane ya yanke wanan shawaran a zuciyan shi cewa zai tafi har garin ya binciko mahaifin nasa ko yan uwanshi bisa taimakon wani mutum da akace tare sukazo dashi mahaifin Amadi din garin suna yara.

   Duk da mutumin ya nuna cewa shima baisan shi ba haduwa duniyace kawai sukayi a ibadan dashi har suka zama abokai har yakai sin sami ubangida dan zamfara da suke sana,an dabbobi tare har yakai sunji dadin mutumin sun biyoshi nan zamfara sun zama kamar yan uwa dashi.

   Amma shidai ainihin dan kanone kuma yasan shi mahaifin Amadi din yana fada mai cewa shi dan Mambila ne kuma ainihi iyayyenshi sanan nune a garin da kace gidan hardo Dume za a akai ka.

    Wanan zance Amadin ya rike a matsayin makami a gareshi yaji yana da karfin tafiya a zuciyar shi koba komai zaiyi kokarin kai kanshi garin ya binciko waye ainihin mahaifin nasa a nan.

    Haka yasa yai amfani da daman shi daya samu yanzu tunda ya gama karatun shi kafin ya fara wani abinda zai samu na dogaro da kanshi ya hada yan kudaden dake gareshi ya kulla wanan tafiyan a asirce ba tare da sanin kowa ba a cikin dangin shi.

   Tun yana kallon garuruwa har yayi barci ya falka driver sai faman sharara gudu yake dasu a mota saidai sun tsaya a wani gari sunyi sallah sunci abinci a garin.

   Dan samakon da akasarin passinger mutanen motan sukayi a lokacin yasa suka sauka akaci abinci suka kara daukan hanya kuma.

   Kwance nake ina barci ni kadai a dakin nawa sai faman juyi nakeyi a gado don mafalkin da naketayi marasa kyau daya shafeni gudu nake faman yi ina neman ceto.

   Don wani iska mai kama da guguwa dake bina a guje ina gudun ceto kada ya lailayeni a lokacin wani gidane a gabana na gani aka miko min hannu kamar an fisgeni da karfi alaman wani ya ceceni na falka a tsorace.

    Da kyat na bude idona sai naganin a wani daki na daban sai daga baya na tuna da inda nake na dade a hakana kafin na mike zuwa bandaki na kewa na fito.

   Duk da ummah ta fada min na dinga kokarin yin sallah dare amma sai nakejin kasalan yin hakan a gareni saida kyat nake samun daren da nake rayewa ina tsayuwan daren .

   Hakana koma wani barcin ya kara daukana wani mafalkin nakeyi saidai wanan karon ganin kaina a wani waje dake da yawan tumfafiya gasu nan birjit a wurin ba iyaka.

   Na rasa me zanyi a lokacin in ceci kaina a wurin ina nan tsaye ina tunane sai na kai zaune ga wirin ba motsin komai ina nan zaune ne na kurawa wasu halita a jikin wani iccen tumfafiya dake kusa dani ido ina kallo gashi ni ban san me nake a wurin ba,  sai can naji motsin a bayana na juya .

  Wani mutum naga yana nufoni dattijone sosai mutumin yana cikin fararen kaya yana min murmushi tare da sallama.

   Kaman nin mutumin yayi min kama da wanda na taba sani ko naga fuskan a wani wuri kafin ya karaso nake faman tunanen hakan.

   Na amsa sallaman da sauri cikin damuwa yace zaman ki a nan shine alherin a rayuwan don zaki kubuta daga sherinsu har abada.

   Don kina tare dasu ta ko ina baiyanan ki a nan shine alheri a gareki ya zama hanyar kubutanki daga hannun makiyanki don suna son saka rayuwanki a ukuban su a yanzu na har abada.

Saidai kuma zasuyi ta wahalan cin maki amma ba zasu taba samun nasaran iya hakan ba gareki don ke din da tsari a jikin ki wanda ba kowa Allah kewa wanan irin baiwan ba a rayuwa.

  Don ke din kina tare da tsarin Allah ko yanzunma suna kan neman ki ba zasu hakkura dake ba sai sunga abinda zai faru ya faru dake zasu dauka sun gama da rayuwan ki gaba daya.

   Basu san cewa kin riga da kin masu nisa ba a hakan sai daga baya zasu gano hakan gareji lokacin da basu iya komai a kanki zasu san suyi sake har kinfi karfinsu.

  Kinga hanya nan ya nuna barin gabas da hannun shi yace ki bishi zai kaiki gidan ku ba abinda zai sameki in kin shiga gidan in sha Allahu.

 Nuna min hanyar da yayi yasa na dago kaina ina kallon hanyar daya nuna min din babu komai a wurin sai yawan tumfafiya gasu nan kore dasu sunyiwa wani irin luf luf a wurin gwanin ban sha,awa.

    Na dawo da kallona ga tsohon saidai babu kowa a wurin kamar ba wani mahalukin da ya taba tsayawa bayan ni har nayi magana dashi a wurin na yunkura na mike haka naja kafata da kyar na nufi wurin daya nuna min din.

  A cikin ganyayen tumfafiyan masu tsawo da tsayin duhu nake tafiya da sauri sauri gudu gudu ina sauri in bar wurin amma bancin ma iyakar wurin ba a lokacin.

    Ban kuma fasa kutsa kaina ciki  duhun ganyen tumfafiyan ba sai ganin kaina nayi a gidan kakan Ahmed tsaye ina dan waige waige a tsakar gidan su din daga haka.

  Har na falka daga barcin don alam din wayana dake kara a lokacin alaman shidda na safe yayi ke nan a gurguje na mike na shige bandaki na dauro alwala don na gama makara ga sallah asuba ranan.

  Wanan mafalkin yasa ni jin wani yanayi na daban a jikina don tun tashina nake jin kasala a jikina ko ina yana min ciwo zakice a fili nayi wanan gudun ba a cikin mafalkina ba.

   Ranan ban iya fitowa ko falo ba har su mommy suka fice wurin aikinsu ni kuma ina kwance a dakina a galabaice sai wajajen sha biyun ranane Tabitha ta leko dakina tana fadin.

   Anty Anty yau lafiya kuwa baki fito ba barci nake sosai a lokacin a galabaice nake jin muryanta sama sama a kunnuwa na hakan yasa ni bude idona da sukai min nauyi a lokacin ina kallon ta bushi bushi tsaye dan nesa kadan dani.

    A cikon murya mara sauti nake fadin yau bana jin dadin jikinane nake kwamce ina kokarin son in juya itakuma tana tsaye a inda take  idon ta yana kaina tana kallon yanayina tare da fadin ayyah sannu ko .

  Na hado maki ruwan zafi ki sha shayi ta fada cikin tausayawa nace barin yi wanka na fito kitchen din tace Allah baki lafiya nagode na fada a daidai lokacin dana samu na mike zaune.

   Ta juya ta fita na dan dade a zaune don sanin danayi cewa baida kyau daga rashin ka kace zaka sauko daga kan gado ba tare daka dan dade a zaune ba na wasu yan mintuna kadan.

  Don irin hakan yana jawa jikin bawa wani matsala a take attack zai iya kama mutum a wurin yasa na saba da idan na tashi zan danyi minti biyu ko uku zaune kafin na mike na sauko.

   Bandaki na nufa na watsa ruwan zafi ko zan samu dan karfi a jikina na fito na murje jikina da manshafina na fito bayan na shirya zuwa kitchen.

   Ina shiga Janet ta shiga yimun sannu itama na amsa Tabitha ta fara fadin madam yau ta fita ta kwashe kayan shayi muma ba a bamu shayin munsha ba.

    Na danyi murmushi karfin hali ina fadin zakusha shayin ke nan tace in mun samu zamusha mana anty nace barin zo na juya zuwa daki na dauko kudi na kawo masu dubu uku nace su karba su sayi duk abinda suke son suci.

   Gadiya suka fara min na dora idomie a wuta na dafa nan na fara jin gulman mommy da irin halinta na samu abubuwa da yawa da nake son ji game da mommy din a bakinsu.

   Zaune nake na kasa cin abinci don bakina da nake ji harshi babu test a lokacin wayana na jawo na fara neman layin Ahmed saidai computer na fada min not richarble ..

  Kira kusan hudu nayi mai ban sameshi ba yasa nayi mamakin haka  don yana ganin kirana yaka  dauka ko ya bari sai ya mutu ya kira da layin shi.

  Irin haka  yasa na kasa fahintar halin shi don shi mutum ne da sam baison aga gazawan shi a al,amari idan ya taso tsakanin shi da mutum din.

  Yau kwana biyu ke nan baya gidan ganin cewa yamma ya soma a rana ta biyun a daidai lokacin dashi yake can yana kokarin shiga garin yola Dije kuma a nan zamfara ta tayar da hankalin ta sosai.

   Har yakai ta fita ta samu malam tanimu da fitosanshi ke nan a lokacin take labarta mashi rashin dawowan Ahmed din gida da sunan zai shiga kauye ya sayo hatsi kamar yadda ya fada mata din.

     Dijeki kwatar da hankalinki duk inda yake in sha Allahu Amadi yana lafiya don ni jikina bai bani cewa wani abu ya sameshi a can ba kinsan tafiya yadda yake.

    Mai yuyuwa wanan karon yayi nisane da gida sosai don in kin kula abinci a yanzu yayi nisa sosai ba ako ina ake samun shi ba haka kai tsaye.

   Malam Tanimu Amadi bai tafiya irin  haka yakan danjene ya dawo gida don haka donle in damu da rashin dawoawan shi haka yaufa kwana biyu ake nema ga tafiyan nasa.

   Namiji nefa Dije don Allah kijeki ki kwantar da hankalinki insha Allahu yana nan lafiya ba abinda ya sameshi a can saidai muyi adduan Allah ya dawo dashi lafiya yanzu kan.

  Wanan  zancen nasu da malam tanimu yasa ta danji hankalinta ya dan kwanta ta ta koma gida da dan kwarin gwiwa ba kamar yadda ta fito ba da farko.

   Kowa ya fito a motan ga yamma da yayi sosai a lokacin don har wasu sun fara shirin alwala shima fita  yayi da dan jakkarshi na ratayawa kalan ta maza a kafadan shi.

    Wurin wani dan Union ya nufa da yake gani dattijone a   wurin yace don Allah malam tambaya nakeyi mutumin ya juyo don jin hausan shi yana kallon shi.

   Yake fadin mabila nake son zuwa don Allah ko za a samu motan da zata tashi a yanzu zuwa can ?

   Malam da yamman nan kuwa gaskiya yana da wuya a samu motan da zai tashi yanzu zuwa can don yanayi hanyan a yanzu.

   Amma ka dakata mu gani nan zuwa dan anjima amma da zaka bi shawarana ka bari sai zuwa safe kabi motan farko ka wuce kasan yanayin boko haram din nan da muke ciki ya fara kawo muna nan.

  Jin hakan yasa jikin Amadi din yai sanyi shi yanzu idan yace zai kwana a ina zai kwana ke nan don haka bashi da zabi in mota ta samu zai dauki kaddara hakana yabi hanya Allah ya tsaresu.

    Kaje can ka zauna mutumin ya fada yana nuna mashi wani benci a wurin Amadin yace bari nayi sallah a can na fito zan dawo yanzu in sha Allahu.

    Jeka Allah yasa mu samu motan mutumin ya kara fadi shi kuwa Amadin ya nufi wajen da yaga wasu na zuwa don yin ibada.

    Har ya idar ya fito ya dawo wurin ba alaman mota  har lokacin yaja ya zauna a nan inda mutumin ya nuna mashi da farko kafin yaje sallah.

    Bai dade da zama wurin ba wata mota ta shigo cikin  tashan yaji sunawa drivern kirari ana gaisawa dashi wanan dattijon yaje gurin shi shima suka gaisa.

  Daga can yaga mutumin yana masa hannu ya taso da sauri zuwa wurin su ya iso mutumin ke fadin kayi sa,a ga mota nan har gaba da mambila ya nufa shi sai su sauke ka su tafi.

    Kudin mota dubu biyu da dari biyar ne ka kawo a bashi dama mutum biyu yake nema ya cika kuma ya samu don ga wani dattijo can shima gembu zai tafi yace.

  Hannu ya saka a cikin aljihun shi ya ciro kudin ya mikawa mutumin saura dari biyu ya sake mika yace babba ga wanan kasha ruwa.

   Godiya sosai mutumin yai mashi don shi tausayi dattijon ya bashi a rayuwa yafi tsanan wanan aikin na Union din tasha sai yake ganin shi ga aikin malalatane.

   Sai kaga mutum har mutum.daya dace ace yana aikin karfi amma ya buge ga yin kamisho din mota ana bashi taro sisi zuciyarshi ta kara mutuwa .

   Wanan din ma ya ganshi ya dan tsufane yasa yaji tausayin shi haka kuma ya hango idon mutunci ga mutumin tun shigowan su cikin tashan dama shiyasa ya nufi wurin shi.

   Ba bata lokaci bayan shiganshi motar yana rugume da yar jakan shi motan ta tashi suna daga masu hannu da alama wanan drivern sananene sosai a cikkn tashan yola din.

No comments