Breaking News

TUMFAFIYA 32

 

 

 


 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[2/5, 3:35 PM] +234 816 362 6370: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH  ,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

 3️⃣2️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

 

Baka jin komai a motar sai kidan gurmi da irin wasu dirobobin nan kan saka a mota idan wanan ya kare wani kalan zai dauka su ukune a cikin motan daga driver sai tsohon nan guda sai ko kayan daya dauko a bayan motan nasa.

    Don haka motan yayi shiru sai kida ke tashi a ciki kawai yayin da Amadi ke faman sauraron fatawan malam daurawa ta hanyar saka earpiece dinshi a kunne a yar karaman wayan shi a lokacin .

   Idan malam din yaba da wani adduan da bai gane ba zaiyi ta faman nanata adduan yana bi a haka har barci ya dan daukeshi na dan lokaci.

   Mafalki yayi da har ya manta da cewa a mota yake lokacin ba a gida ba komai yake mafalki a kai ba sai farin cikin rayuwan shi watau zahra.

    Zahra din ya gani zaune a cikin damuwa ya karaso inda take zaune yana tambayanta ko lafiya ya ganta haka a cikin damuwa.

    Kai ta dago ta kalleshi da fararen idanunta ta dan yi murmushin yake gareshi tana fadin sun sakani a gaba brother sai kace ni kadaine diya a gidan mu.

  Why zasuce saini ni kadai why da suke min hakan zasu rabani dakai su waye zahra ya tambaya bakin shi na rawa ta dago kai cikin yanayin kuka ga hawaye ya bata mata fuska ta ko ina ta nuna tana fadin sune sune suke son ganin bayan mu.

   Juyawan da yayi yaga inda take nuna mashi din ne ya falka ya ganshi a cikin mota ana faman sharara gudu sai tsohon nan abokin tafiyan shi daga gefen shi zaune sai daya  mutumin dake tare da driver a gaba.

    Dan gyara zama yayi yana fadin sannu baba jin haka yasa tsohon dan dagowa yana amsawa tare da fadin amma yaro kai daga nahiyan sokoto kake ko naji hausan ka ta mutanen wajajencan na sokoto.

    Eh baba amma ni daga zamfara nake ba sokoto ba zani neman mahaifina ne a nan garin ysohon ya amsa da na,am anan Manbila yake da zama yace eh to bandai sani ba amma yace shi mutumin mambila ne saidai kuma in anzo mambila din anfi sanin su da chedawa.

   Chedawa tsohon ya maimaita sunan yace anya kuwa a nan cikin mambilan zaka sameshi tunda naji kace chedawa sai wajajen tasanma su gurojje.

  Jin hakan yasa Amadin jin gaban shi ya fadi sai ya kasa daurewa yace baba ina ne hakan kuma ?

   Duk a cikin bangaren mambilawa yake saidai ba gari daya bane don akwai dan tafiya tsakanin shi da garin mambila din.

   Au bakone a wanan nan nahiyar namu ke nan drivern ya fadi daga gaban motan tsohon yace bakone bai taba zuwa wanan kasan ba.

  Yace wai ya fito yawon neman mahaifin shine daga zamfara dattijon ya fada jin hakan yasa drivern dan juyowa yana fadin daga zamfara fa kace kake yaro ?

   Wallahi daga can nake ya kara fadi yace kace kasha hanya da tafiya mai nisa ke nan, amma kayi kokori sosai wurin wanan tafiyan haka ?

  Drivern ya fada yana mamakin yaron kafin ya kara fadin da fatan kasan inda zaka sameshi dai ya tambayi Amadin ?

   Idan bai sani ba ai baya zuwa har nan da sunan neman shi duk yadda akayi yana da kwatancen inda zai sameshi dayan mutumin dake zaune tare da drivern gaban mota ya fada.

   Murmushi Ahmed ya sauke a fuskan shi yana girgiza kai cikin bacin rai yace ko sanin sa ban taba yi ba asalima dai tun ina goye ya tafi ya barni nida mahaifiyata.

    Na daizo ne ko Allah zaisa na gano inda zan sameshi amma bansan sunan garin da zan sameshi ba din a yanzu yaji drivern motan yana fadin.

   Kai mutanen mu akwai daukarwa kai nauyi zaka tafi kabar danka daka haifa da zufan ka babu ko waiwaye wanan ai yiwa kai zaluncine don duk abinda ya shafi jinin ka ya shafeka.

   Drivern motan nasu ke fadin haka yaci gaba da fadin kayi dabara yaro don haka shine gatan ka da cikar kimar ka a idon mutane don duk da mutane sunsan ta hanyar sunna akai haifeka wanan ba zai hana su soke dashi ba.

   Ai wasu mutanen suna yin abu a cikin duhun kai da jahilci ta yaya kasan kana da da a wani wajen zaka gudo ka barsu tsawon wanan shekarun mutumin dake zaune gaban mota tare da driver yake fadin haka.

    Wani lokaci kadara da nisan wuri ke jawo hakan saidai wasu suna irin haka da son ransune Allah ya kyauta tsohon dake tare dake tare da Ahmed din a bayan mota zaune ya fada.

   Duk Ahmed din yana jin zafin maganganun nasu a zuciyan shi saidai baida zabin hakan don bai sani ba ko ta sanadiyan hakan zai samu mafita ga tafiyan nasa.

    Haka sukai ta zancen su daya shafi irin matsalan nan yana sauraren duk abinda suke fadi duk yana jin zafin hakan amma bai saka masu baki a zancen ba.

  Kasancewa tafiyan nasu yayi yamma da yawa don haka duhun dare ya riskesu sosai a hanyan baida wani zabi sai wasiwasin yadda zaiyi idan sun sauka wani gari.

    Wayan drivern ne yayi kara ya dauka hakan ya saka motan yin shiru lokaci guda da alaman tambayan shi ake ko yana ina a lokacin don cewa yayi munashiga taraba yanzu.

    Nan Ahmed din yasan inda suke ya gyara zamanshi yana bin hanyar da kallo ba tare da ya furta komai nan zaka gane irin misikilancin shi na rashin son yin magana sosai da baiyi.

   Ina zaune falo tare da mommy data dawo tasa Tabitha ta kirani a dakina tana tambayana abinda ke damuna nace ba komai kaina kawaine yake dan min ciwo nasha magani kuma ya daina yanzu.

   Idan bai daina ba muje asibiti zaifi su duba idan wani abune yake damun ki na danyi murmushi ina fadin ba komai mommy naji sauki.

   Fada min dai idan kewa hjy kika farayi tun yanzu na sani nace a a mommy ba gaki ba tace nasani amma tun zuwan ki nima nasan ban samu lokacin zama dake ba gidan nan daughter.

   Kiyi hakkuri wallahi aiyukane sukai min yawa ga zancen bukin auren autan hamisu ga kuma aiki daya taso muna a office wanan duk ya dauke min hankalina.

   Wallahi har fita nake sonyi dake muje ki dan zabo wasu abubuwan bukatan ki a nan don kada ki takura don naga bakizo da wasu kaya masu yawa ba don kada ki dade ko ?

   Murmushi nayi ina fadin lah mommy wallahi ba hakana bane naga dai ba inda zanine yasa ban dauko kaya masu yawa ba dama ban fada maki har kano zamu tafi buki tare dake ba.

   Za,ayi bukin autan mu namiji zaiyi aure kinsan maman mu mu bakwai ta haifa mu uku mata da wanan da kika ga dayan maman mu daya da ita itace yar wanda zaiyi auren a yanzu ita kuma dayan yar kanwar maman muce ita.

  Dukkan su a wurina suke tuntasowan su danayi auren farko nake zaune tare dasu mijina na farko mun rabune dashi yarana suna can hannun shi biyu maza sai mace daya.

   Saidai nan gidan ku kuma idan na samu indada karawa ta fada tana dariya nace Allah yasa mommy muma mu samu kani ko kanwa don  Affarace karama har yanzu su ummah da mama basu kara bamu baby ba kuma .

   Da alama taji dadin zancen  nawa don yadda naga ta lumshe idanun ta tace watau zahra kin gane wanan halin naku yasa nake son ku keda mahaifiyar ku.

  Don idan kuna zama da mutum da zuciya daya kuke zama da kowa ba tare da wata manufa ba kinsan maman ku maimuna ido da ido ta kalleni tace dani ba daina haihu da daddyn ku ba saidai na saka a masai ?

    Wanan yasa nake son haihuwa yanzu sosai zahra ko don in nuna mata iyakarta ta gane ba aiwa Allah shishigi ga lamarin shi da sam banda ra,ayin kara haihuwa a rayuwata .

   Amma yanzu naji ina son na haihu a gidan ku nima na saka nawa irin a cikin ku naga yadda zatayi damu din a gidan lokaci daya duk muka juya don jin kamshin turaren Abba da mukayi alama  ya shigo gidan ke nan ya dawo lokacin.

    Fuskan Abba a kanta yake fadin wai zama kikayi da yarki haka kuna hira kamar kin samu wata babba sa,arki  kuna hira.

   Daddy ke nan idan uwa bata zauna da yarta tayi hiraba a yanzu dawa zaka zauna hirana da zahra naji dadinshi sosai don yarinyace mai hangen nisa sosai.

  Ni ki tashi da wana  shirmen naki ki bani abinci Abba ya fada kamar wani yaro mai jin yunwa ita kuma tana kokarin janshi da wasa har dai ta mike ta wuce zuwa kitchen wurin masu aiki.

   Lokacin Abba ya kalleni yace maamah ya labarin karatun kine da fatan kina mayar da hankali sosai dai kuma ina fatan kin fita zancen wanan yaron mara asali ?

    Gabana ya fadi amma haka na daure nace Abba lafiya kalau Alhamdullahi bana wasa da karatu in sha Allahu shine amsan dana iya ba Abba din lokacin.

   Zanji dadi idan hakan ya kasance gareki don ina da hope maikyau a gareki don hakane bana son ki tsaya yin wasa ko kulawasu can idan kinyi hakan zamu shirya dake.

  A zuciya na bashi amsa da sabanin hakan matsalane ke nan ko amma fili cewa nayi ban wasa Abba kuma ban kula kowa yanzu duk ina da labarin komai Abba ya ban amsa.

   Shiru nayi na dan lokaci kaina yana duke kasa kafin naji fitowan mommy daga kitchen hakan yasa na daga daga wurin na nufi dakina don kada in tsaya idona ya gane min irin soyayyan da sukeyi kamar yara ko a gaban kowa.

   Daki na nufa zuciyana cike da maganganu kan zancen mu da Abba dana mommy din da mukayi watau dai Abba har yanzu ya dauki zancen Ahmed da zafi a ranshi ?

    Ni banga wani illa dake ga Ahmed din ba da ko yaushe Abba ke kiranshi da kaskantance kawai dai rashin fahinta ne wani tambaya ne yazo min to ko Ahmed din baida ubane shegene da Abba ke fadin baida asali ?

    Gabana ne ya fadin yin wa kaina wanan tambayan to ko shegene meye laifin shi tunda shi yana da natsuwa bashi ya aikata hakan ba ai.

   A take wani sashi na zuciyana ya bani amsa da fadin inko hakan ya tabbata ko ummah ba zata yarda ba balle Abba da yake na miji nima kaina duk da nasan za,aita aibantani kan hakan ba yarda zanyi da hakan ba.

   Ke nan taraiyana da Ahmed din dai akwai matsala ke nan don haka dole in tambayeshi inji gaskiyan abin daga bakin shi don ban taba kawo wanan tunane a kwakwalwana ba.

   Haka na ajewa raina zan tambayeshi labarin mahaifinshi dana yan uwanshi inji daga bakin shi don komai nason tambaya asan gaskiya tunda Abba ya nace da maimaita kalma daya haka a gareshi .

   Nasan talauci ba zai hana auren mutum ba tunda Allah shikeyin mai arziki jikin matalauci haka yayo matsiyaci jikin mai arziki don ba a san mai gobe zata zamawa mutum ba ai a rayuwa.

    Ni kadai a daki nake faman kullawa in warware  don banda abokin magana a gidan daga mommy sai yan aikin ta da mukan dayi hira kuma akan abinda ya shafi girkine haka.

    Don kanen mommy dake gidan zan iya kirga ganina dasu a gidan don basu zama  gida ko suna gidan ma ba ruwan su dani nima haka ba ruwana dasu don naga suna da gadara da jin kai sosai a yanayin su.

    Sallah nayi na koma gado don sam ban jin yunwa a ranan na kwanta a lokacin zancena da mommy ya fado min a raina nace watau ita mommy haihuwa take so a hakan da girman ta gashi ummah ma data haifi Affara mama tana fadin ta tsufa tana haihuwa balle mommy da zata girmewa ummah din nake gani.

   Ina nan ina mirgina saman gadon naji mommy ta shigo dakina wuta dake kashe ta kunna ta ganni kwance take fadin badai yarinyar nan barci tayi bataci abincin dare ba ?

   Kara lafewa naji kamar ina barcin gaske naji ta gyara min rufin bargo ta kawar min da rigana dana aje a gefen gadon ta kashe wutan dakin taja kofa ta fita.

   Ajiyan zuciya na sauke ina bude idona kallon lokaci nayi a wayana karfe goma sha daya na dare saura naga lokacin yayi saurin yi a ranan duk ban sani ba.

    Wayata din na kalla naji kawai in kira Ahmed mu danyi hira na danna kiran layin shi ya shiga yana ta ringing bai daga da wuri yadda ya saba dagawa ba idan na kirashi din.

   Sai can wayan na batun tsikewa naji ya daga yana sallama yanayin da nake jin muryan shi din yasa nake jin kamar a mota yake tafiya don karan iska da nake ji a lokacin.

   Ina kake haka nake jin wata kara kamar kana cikin mota yace muryan shi da nake ji can kamar yana yawo a iska yana fadin gani taraba zahra zanje wurin mahaifina ne.

   Na ambata Taraba fa kace Brother yace eh ina cikin mota yanzu idan mun sauka zan kiraki idan baki barci ba Allah ya tsare hanya nayi mai ina lumshe idanuwana a hankali daga inda nake kwance din.

   Baya  mun gama wayan ne  na ambata Allah mai tsarki da daukaka na godewa Allah da banyiwa Ahmed wanan tambayan ba har na samu amsa a wurin shi haka a cikin sauki.

  Da nayi masa tambayan dani zan rage da kunyar hakan shiyasa ake cewa komai yana son tunane da nazari kafin mutum ya aikata shi a rayuwan shi ashe .

   Hakan yasa naji wani natsuwa da dadi a zuciyana kamar an cire min lakkan jikina a lokacin yadda nake jin kaina a lokacin har wani nauyayyen barci ya saceni lokaci daya ban sani ba.

   Ahmed kuwa yana kashe wayan ya nisa ya lumshe idanun shi yana sauke ajiyan zuciya zakace yasan abinda ke a ran zahra ne a lokacin muryan tsohon nan dake kusa dashi zaune yaji yana fadin ai yanzu mun dan fita taraba bakaji yanayin ya canza maka ba.

   Yanzun zamu shiga hawan Mambilane daga nan mun fara tasan ma nahiyar mu na mambila ke nan daga nan ya  zakaji yanayin garin ya sauya ma daga nan .

    Saidai tsohon bai gama rufe baki ba yaji driver na fadin banga mota nabi hanyar nan ba idan mun kai nan ga kadan mu tambaya muji lafiyan hanyan yaya yake.

     Nan yaga yan cikin motan a tsorace suna fadawa driver cewa ya dakata kawai su kwana a dan kauyen gaba zaifi da asuba sai mu kama hanya na gaban motan ya fada.

  Bari dai mugani malam idan hanyar zata biyu sai mu mike zaifi inji drivern shidai yana jin su yana zaune a bayan mota yayi shiru yana addua.

   Ummah ce zaune a falonta da safiya Tani maiyiwa ummah din aiki ta shigo ta sameta suka gaisa take tambayan ummah din ko anji mata motsin uwardakinta anyi waya ko da ita ?

    Ta kira jiya mun gaisa kin santa da shiririta ko sakarcine wai tayi mafalki ta falka da safe duk jikinta ya mutu ita tana jin tsoro ko waya fada mata mafalki gaskiyane oho ?

   Da sauri Tani din ta kalli ummah tace hjy kune dai baku daukan abu da muhinmanci a yanzu ai bai kamata ko kice haka ba da sau ki tambayeta kiji akan me tayi mafalkin aji ?

  Duk da dai ba duka mafalki yake zama gaskiya ba amma da haka dan karamin abu yake zama babba watarana saidai sakaci irin namu na mutanen yanzu ke hana mu dauki mataki kan abu sai yazo ya girma yadda bamu iya dauka muce muna neman sauki a kan abin.

    Yarki ta girma yanzu ba za,asata a sahun marasa wayau ba don tasan ciwon kanta yanzu kama yayi kiji irin mafalkin kinga in na sadakane sai ai mata sadaka a nan Allah ya tsare zaifi.

    Wanan ne kuma Allah bai ban ikon yi ba ko ince zan mata sadakan banyi ba gaskiya ummah ta fada a dan damuwan hakan don maganan Tani din yayi tasiri a zuciyar ta.

   Tasani cewa tun tana karama wani lokaci manya kance sunyi mafalki bari suyi sadaka don Allah ya mayar da abinda sukai mafalkin alheri garesu.

    Amma gashi ita bata bada daman hakan ba ga yarta sai binta da tayi da fada tana kira mata sakarci komai sai ta saka arai ya dameta don mafalki zatace tana jin ciwon jiki.

    Iyayye mu farga da wanan maganan a yanzu a kan yayan mu don a yanzu zamani na tafiya ne da nau,i biyu wayewa da jahilci don har yanzu akwai masu  jahilci dake sihiri akan mutum kuma Allah zai iya nunama a mafalki wanan baiwane da yawancin mutane da yawa kedashi a cikin rashin sanin hakan garesu.

  Mata mu farga da yawaita yin sadaka ga yayan mu don min sadaka riga kafin masifa ne ga bawa sadaka baya tafiya a banza inji masana addini komai kankanta abin sadakan zaiyi amfani ga maishi.

  Musan man sadakan abinci, kudi, tuffafi kosai sugar kuli,kuli alewa naira darin ki sai yai maki riga kafin rayuwan ki dana yayan ki duniya da lahira.

  Amma yanzu wata ana sati daya ko fiyema da hakan bata mika wani abin ba da sunan sadaka saboda Allah da Annabi Allah ya kare ya tsare ya bada ikon yin hakan Amin.

No comments