Breaking News

TUMFAFIYA 48

 

 


ZAINAB IDRIS MAKAWA [3/11, 11:10 PM] +234 706 815 1331: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH  ,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

4️⃣8️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

 

Kai yadauki zafi kowani part na gidan mu ana sha,anin buki amma hakan bai hana a saka ido aka  ummah ba don ganin abinda take gudanarwa a nata bangaren.

   Don mutane da yawa suna kokarin son zuwa suba idanun su abinci don su samu abin fada gaba idan magana ya taso wurin yinshi duk da ansan tallaka zan aura amma bai hana mutane kwadayin son zuwa gidan nawa ba su ganewa idon su abinda ake fadi game da auren nawa.

   Yan fammanin mahaifina sun tafi sunyi min jere da kayan da Abba yasa hjy karima ta saya min washe gari kuma kayan ummah suka iso suma aka kaimun su gidan aka jera min su sai aka fitar da nasu Abban aka mayar a dayan dakin a take part din nawa ya koma abin kallo  .

   Duk sunyi wanan abin ne ba tare da sanin kowa ba sai gwaggo shafa da gwaggo Ai da suka tausaya muna kan irin abinda Abba yake nuna muna a bukin.

   Dawowan sune har wasu daga cikin dangi sukaji irin dukiyan da ummah ta kashe min wanda al,adan uwan kasan hausane ta fitar da duk wani tanadin a bukin auren yarta idan ya taso.

   Haka mutane zasuyi ta sintiri wurin zuwa ganin daki da abinda aka kaiwa yarinya a dakinta koda kuwa zuwa nisan inane garin sai an samu wanda yaje ya gano ya dawo ya fada.

   Hakan ne ya faru dani don su gwaggo na dawowa suka fara fadin hidiman da suka gani a dan gidan nawa da mutane suka raina saiga labarin abinda ummah da yan uwanta sukayi min ya karade kunnuwan mutune lokaci guda har yakai kunnen mama da hjy karima har zuwa wurin Abba din.

    A gaskiya Abban yaji mamaki yadda za ace wai kudin daya bayar har ummah tafishi yimin kayan kwarai sai jikinshi yai sanyi da jin hakan kamar wanda aka tunatar da wani abu daya manta a baya.

    Munyi walima gidan baffa Abubakar na mazon Allah an dauki waliman na yaku bayi da farko amma ganin yadda yan uwa da abokan arziki suka tsaya suka tsara abin da yadda akai kwaliyan titin unguwar gabaki daya da malaman da akaji an gayato sai mutane sukai ta tururuwa zuwa wurin waliman har ma da wanda ba a gaiyata ba lokacin don sauraron wa,azin.

    Ga kawayen ummah sunzo da sebeniya masu kyau na rabo sai hakan ya kara daukan hankalin mutane har yaja kowa zuwa wurin waliman don komu bamu zaci hakan ba gaskiya.

    Har an fara taron lokacin da mukazo tare da yar ummah wace ta tayar da ita a kaduna har Abba ya ganta ya aureta da kawar ummah da wata gwaggon su ummah din a cikon dirkekiyar motan da tazo dashi.

   Nayi adon lafaya mai shegen tsada takalman kafana kwaliyansu daya da lafayan jikina hakama jakkar dana rika shima kala daya da lafayan jikin nawa.

   Sam bansan cewa an gaiyato Ahmed ba wurin sai ganinsa mukayi yazo da tawagarshi nan dai aka nuna masu inda zasu zauna shi kuma suka sa muka shigo filin a tare dashi.

   Anan kowa ke dage yana son yaga mijin dana aura din da ake shati fadi a kansa din babu inda za a rainawa Ahmed wurin halitta saidai a kirashi da fakiri wanda baida halin ko zarafi something dai hakan.

    Wa,azi akayi akan hakkin aure daya kamata namiji ya sauke da wanda ya haukan mace itama sai kula da hakkin makwabtaka da malama ta karshe ta fadakar   damu lokacin.

   Inda akasa nayi karatu a cikin suratul maryam shima yayi a cikin suratul yusuf ikon Allah malamin ya fada yace kafin nazo wurin taron nan nayi ta tsuntan maganganu a cikin wani unguwa dana sauka akan auren nan.

    A gaskiya ni a ganina wanan hadin shine hadi irin wanda ya dace ayi a musulnce nan dai yayi bayanin yada ya dace ya wayar dakai yaja hankalin mutane akan hakkin aure.

   Kafin aka fara raba abubuwan ci dana sha da kyaututuka na ban mamaki bamu tashi ba sai gab da magariba taron ya watse kowa na sam barka ga taron.

    Mun dawo mun samu masu shirin zuwa dinner suna ta shiryawa masu bada labarin walima suna bayarwa abin mamaki saiga sako daga hjy mama cewa wai ummah ta shirya da mutanenta angaiyacesu zuwa wurin dinner su Aisha.

    Tadai amsa amma ba wanda ya leka a namu bangaren saida safe muke jin cewa wai walimana yafi dinner nasu kyau sosai don ba a tsara abin yadda ya dace ba karshema fadane ya watse taron da yan gidan angon Aisha da tawagan mama a wurin.

   Har mazan na fadin cewa sun fasa tunda mutanen banzane su inbashi da ya mayar da kanshi baya ba dama har Aisha macen aurene bayan kowa yasan irin watsewan su.

   Shima angon yai fushi dama a buge yake ya nuna mama yace ta kwashi yarta ya fasa auren gobema barin zaiyi da safe dama ita ta matsa mai akan ya auri yarta.

   Nan dai sukayiwa juna tonon asiri sosai itama da borin kunya tace ta fasa bashi yar nata mashayin banza da wofi kawai ai dama taimaka mashi tayi har ta dauki yarta ta bashi.

   Zance dai har wurin maza da safe haka falon Abba ya cika da mutane kowa da kalan zancen da yake zuwa dashi itama Rukkaiya dai an samu matsala wai gidan da zai ajeta yayi masu kadan su kuma sukace idan bai masu ba sai a fasa.

   Anan Abba ke jin cewa wai mijin Rukkaiya din ashe dan damfarane yana sayar da filayene a garuruwa da haka ya tara arziki yake karya dashi a gari.

    Kai rikici dai gashi nan da tonon asiri kala kala kowa yazo ya fadi nasa gashi da karfe biyu za a daura auren mu ga abubuwa sun dagulewa mama sai jiki yayi sanyi a lokacin.

  Dole Abba ya kira taron gagawa don samun mafita don abokan shi wasu na nisa harsun iso gusau lokacin gashi kuma rikici nata kara bulo kai.

    An samu an sasanta da iyayyen angon Aisha sun yarda an daura auren bayan Abba yaje har gidan da kanshi yaji ba,asin fada  nasu yaba da hakkuri kada yaji kunyan jama,an daya tara din.

 Karfe biyu da rabi aka daura aure har zuwa ranan ba a kawo lefena ba abinda ni kuma mutane ke gulma a kanshi ke nan kaina wai duk talauci ne haka ya hana mutanen Ahmed su kawo min laife ?

   Dangin mahaifinshi sukazo da kayan lefen nawa wurin daurin aure kamar yadda al,adansu yake sai bayan an tashi taron ne aka shigo dashi cikin gida aka gani nan gwaggo Shafa ta sake guda saida hankalin kowa ya dauku da hakan wajen.

  Tana fadin Alhamdullahi aure ya dauru tsakanin Aisha da manbo Rukaiya da sha,ibu gaye Zahra uwa bada mama don sunar uwan mu taci da angonta Ahmed.

   Alkawarin Allah bai tashi yau dai Allah ya nufa mun sheda wanan ranan kai ku shigo da abin arzikin nan a bajeshi tsakar gida kowa ya gani tana fadawa masu shigo da akwatinan acikin gida.

  Ta sake aza wani gudan tana fadin lalai a haifi da arzikin shi yafi a mutu a barmai gado daki auri mai arzikin ga mara arzikin na shirin fidda yarmu a kunya wana  kaya haka kamar matar dan gwauna fa.

    Kayan sunyi kyau sosai don ba zakace kaya daga hannun mutum irin Ahmed mara gata suka fito ba saida wata yar uwa  mu ta dakatar da gwaggo shafa ta daina sake magana.

    Ni dai ko a idona banga kayan lefen nawa ba sai sha,anin buki da mukeyi saiga sakon mama cewa na bada key din motana inji Abba.

   Wanan kuma wani irin zancene haka harda motan nata zai karbe saboda kiyayya wanan wani irin cin fuskane wai haka yayar ummahce ke wanan maganan ga gwaggo Sa,a datazo karban key din motana.

   Don ita da mama aminan junane sosai a yadda naji ance itace kawar mama duk da suna da zumunci amma ta sanadin ta Abba ya auri mama kuma har yanzu suna tare duk da kowa ya girma.

   No ku basu don Allah Allah ya horewa mijinta wata rana ya saya mata motan da kudin shi badai za a karbi rayuwanta ba ai iya mota zancen zai tsaya ai.

   Motan da banje gidan Ahmed dashi ba ke nan kuma su ummah basu tayar da zancen ga kowa ba suka bada key din salin alin zancen ya wuce duk da hakan ya tabawa ummah zuciya sosai.

   Motar yan uwan ummah dana  kawayenta akai amfani dashi abindai kawai in fada a dunkule don zakace nidin ko yar rikoce a gidan ko wata yar rikon tafini samun gata a lokacin  .

   Don abinda mamaki yadda aka nuna min lokacin ko an kawo tsegumi wanan yayan ummah din ita ke daga hannu tace a kyalesu su fatansu Allah yaiwa aurena albarka.

  Don hakane suka sani zama a sakin tare dasu wai gudun wani ya hure min kunne a can dakina nazo na tubure masu daga baya.

  Gashi duk da banyi gaiyata ba amm hannatu ta gaiyato yan course mate din mu dama wasu da muke shiri dasu a school din namu dakin nawa ya cika fam da kawayen mu.

    Magariban farko gwagwanin  mu suka shigo dakin waina fito za a kaimu wurin Abba daga can za a wuce damu gidan hjyn su Abba sai gidajen mu.

    Tunda na sallame sallah nake daman kuka don irin nasihan da ake min a dakin da jan hankalina na tsaya na rike aurena da hannu biyu don shirun da mukayi nida ummah harsu yana sakasu wasi wasin din mu.

   Nikan kuka nake da daya da biyu har zuwa uku sau uku amma nabar komai a cikin zuciyana ina addua ashe banji abin kuka bama tukun sai lokacin da mukaje sallaman Abban mu.

   Inda ya kara jaddada muna musanman ni kamar yadda yace don a gareni yake hango matsalan farko a gidan shi na ba yaji ba kuma zuwa gida neman wani abu don ya riga ya gama damu ko a cewan shi.

   Kai har dai yar ummah data biyomu zuwa falon tare da babban aminiyar ummah din suka kai ga tankawa a lokacin inda tace kamar yadda akewa kowa fatan zama  lafiya a dakin shi insha Allahu ko ita haka zata zauna a dakin ta lafiya da yardan ubangiji.

    In har ana gason hakkuri a duniya ai Zahara ta gaji hakkuri a wurin uwarta meya rage na hakkuri yanzun wanda bata sani ba kuma ai saidai wanda ba,ayiba a duniyan nan.

    Kowa yayi shiru sai cewan da gwaggon mu daya tayi ku tashi mu karasa gidan hjy kuyi mata sallama daga can zamu wuce daga can baya wata ke fadin su angwanan zahra sun kawo motan daukan amaryan sune.

   Aminiyar ummah hjy kubura ta bude baki tace ko basu kawo ba mota ba matsala bane ai shima angon yanzu ya zama dan mu da akwai motoci sai mu kaita fatan mu dai Allah ya basu zaman lafiya aka amsa da amin.

    Haka suka rikomu zuwa waje muka taka da kafa zuwa gidan hjy din nan ma irama tayi muna nata hudu ban mai kama da jurwaye tare da fatan lafiya gare mu aka kwasa akafito wajen gidan .

  Ina jin mommy kubura na waya cewa sauran su fito idan an shirya motocin tafiya ba afi yan mintuna ba sai gasu gidan sun samemu da motoci hudu muka shiga gwaggo shafa tana cikin mu  tare da wasu yan uwa da basu bamu baya ba marasa tsoro ke nan su.

    Tunda muka shiga motan muna tafe suna fada min naja Tawakhaltu illallah lahaula wallakuwatu ina billahi aliyal azeem sau uku sai na dinga jan,  Hasbunallahu wani imal wakil har zuwa shigan mu gidan shi na dinga ja a bakina ina hawaye.

   Ba zan iya fadan ko hawayen me nake sakewa ba har wanan lokacin asalima ba bace ina cikin hayacina ba gaskiya don sai yadda aka juyani kawai nasan dai ina dan picking din wasu abubuwa dake gudana dani lokacin.

    Jin mota ya tsaya lokaci guda ga guda da ihun yaran yana tashi lokaci guda yasa na lumshe idanuwana a hankali naji mommy kubura dake gefena zaune ta dan kwanto min tana fadin yawaita karfin zikirinki a wanan lokacin ki fara da ya Rabbi ya rabil ya rabil alamin ya Allah ina rokonka a ckkin kyawawan sunan ka daka baiyana suga bayin ka ya Allah ka suturani a dakin mijina har Abada ka kawar da duk wani shedan da shedaniya a tsakanin , , , , , , ,

    Nasan ina maimaita abinda mommy din tace in fada daga haka na rikice masu har zuwa cikin dakin nawa saisune suka san halin da nake ciki kan gadon dakin ta kaini ta zaunar dani da bissimillah tare da adduan koran shedan gareni.

    Anyi adduoi daya dace ayi a lokacin kafin manya su fara watsewa bisa umurnin mommy kubura dama suna sauri su koma suje kai sauran amaren gidajen su haka yasa bata samu wani matsalaba wurin sallaman mutanen.

    Muka rage daga mu sai su su hudu sai yan matan dake falo su hannatu sai zuwa can na fara gane inda nake zaune duk da ban sheda a dakin da nake zaune ba lokacin.

    Kai gaskiya idan Allah ya hadaka da mutanen arziki a rayuwanka ka godewa Allah don sai ka daukama sunfi wani dan uwanka na jini wani lokacin.

   Don ko ni naga hakan a wurin uwata don ko yan uwa da abokai sun nuna mata gata sun fitar da ita kunyan kishiyoyi dana mutanen gari tare da bakin cikin mahaifin mu.

   Yan kawo amarya sun koma cike da mamaki tare da labarin abinda idonsu ya gane masu a gidan kowa saidai ashe mu munbar baya da kura don Aisha dai ba a samu kaita nata gidan mijin ba.

  Saboda mijin nata yana nan aka  bakan shi naya fasa auren nata tunda har tai sanadin data tozartashi a gaban mutane ya baiyana halinshi a cikin rashin sanin kanshi lokacin.

   Wanan yasa ya rufe gidan shi ya juya zuwa portakut inda yake aiki ya fita zancen su ya kumabar sakon cewa ya fasa sai ya dawo suzo su kwashe kayan su.

   Mamakan da yarta ranan sun kwana da bakin ciki ita kuka yarta kuka ga zagi da Abba ya dinga surfan su dashi na tozarci a bainan jama,a kowana jinsu.

    Tsab hannatu ta gyara dakin ko ina duk hjy kubura na tsaye har aka saka kamshi kafin ta kara lekani inda nake kwance mukayi sallama ta fito tabar su hannatu su uku a dakin tare dani.

    Tana jin daga dayan lungun da akace na  iyayyenshine ana fadin wai Dije mutanen nan sun tafine basu kawo muna amaryan nan dakin ba ko meye ?

   Ato ina muke da kimar da zasu kawo muna yarsu nan ai bai nuna masu cewa muna da wanan matsayin ba gareshi aiko zanga yadda zaiyi  yau yace zai shiga lungun nan.

   A,a ki barshi ai yana da hankali koma meye dalilinsu nayin hakan zamuji ai daga gareshi suna hakan sukaji sallaman hjy kubura duk sukaja bakin su sukai shiru.

    Su biyune suka shigo ta gaisa dasu take fadin kun jimu shiru ko wallahi mun kawo yarmu sai ya kasance bata da lafiya tana can kwance kafin mu fito saida akai mata allura amma kuyi hakkuri idan Allah ya kaimu gobe zamu kawota gareku.

   Yanzun ma na shigone in fada maku don kada kuga kamar an raina makune anki kawota nan wurin kune ayi hakkuri don Allah lalura ya kawo hakan.

  Nan take su Dije aka shiga fadin jam Allah ya bata lafiya daga jigilan buki sai kuma ciwo haka Allah ya sauwaka.

    Tayi masu sallama ta tafi mahaifiyar Ahmed dake tsaye tana jiran kaucewan ta tace aiko ba gidan nan ba dama nasa  badon Allah aka aura mashi yar nan dole da wani dalili a kasa da yaron nan yake boye muna.

 

No comments