Breaking News

TUMFAFIYA 49

 


 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[3/13, 7:33 AM] +234 803 800 7509: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH  ,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

4️⃣9️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

 

Irina ne shima ba wani tarin abokaine dashi ba sai mutum biyune suka rakoshi zuwa dakin suga angonai adole sun saka babban riga a jikinsu.

    Ina dan jiyo muryan su daga can ciki inda nake kwance a makure kaina yana wani irin sara min lokacin naji muryan hanne tana fadin babu inda zata fito yanzu don tunda aka kawota kanta yana ciwone.

   Naji Ahmed din na fadin subbahanallahi Hanne shine baki fada min ba tun dazun na sayo mata magani ta hade aika san ciwon kan zahra ba irin normal ciwon kan nan bane.

   Ta dai shaka wanan abin inaga ta samu barci don tun dazun banji motsinta ba haba dai hannatu kika barmin mata ita kadai a daki kwance.

   Au laifina zaka gani yanzu Master duk kokarin zama  kula maka da ita da nayi a,a ai bamu yar haka dake amma dai kin kusa laifi kan a nan da baki zauna kin tsare mun itaba a ciki.

   Taufa abu yazo ga masuyi ke nan ashe zamu daina ganin ka yanzu waje kana gida kana gadin gimbiyar bai basu amsa ba sai jin sallaman shi da nayi a ciki yana kiran sunana da Zahra ?

    Barci kikeyine ko idon ki biyu yanzun hannatu ke fada min bakiji dadi ba haka haba aida kinsa ta kirani a waya gashi yanzu dare yayi koda yake barin fita yanzu kila na sameshi bai shige gida ba.

   A lokacin nace cikin karfin hali ga murya duk ya dushe min gurin kukan da nasha a wanan wunin ko wace amarya na farin ciki da walwala a wanan ranan ni kuwa sai bakin ciki da takaicin da muka gani akaina nida mahaifiyata.

    No ka barshi kawai yana fada min ai na fada cikin karfin hali dariyan su mukaji daga falon ko ba a fada ba musan shi sukewa dariyan lokacin.

   Yace baifa tafi ba har yanzun kike nufi bari kawai na samo maki ki gwada a gani muryan dayan abokin nasa mukaji daga falo yana fadin .

   Kai mutumina wai mikakawa zimudi hakana zahra Allah ya nufa yau a gidan ka zata kwan ka shige kamar wanda ankacewa za a kwacema ita.

  Ka barsu suyi abinsu Allah ne ya nufa suga wanan ranan don sun zama iccen tumfafiya mai tohurwar kasa ko an sareka a sannu zata dawowa tsaye.

    Yau ba gashi bayan wuya sai dadi ba hakkurinsu yakaisu ga zama ma,aurata ga jjuna ai Master ya zan zakaran gwajin dafi a cikin dubu.

    Hannatuce ke fadawa abokan nasa haka sai naji Ahmed din ya fito yana fadin  hannatu dare ya soma na sallameku zuwa gida kada aga kun dade a nan.

    Can naji muryanta tana fadin kai haba dai Master wanan kudin basuyi yawa ba kada fa mu cikama ido kai muna kyautan da baka shirya yinsa ba.

    Hannatu ke nan kada kiji komai konfi haka a wurina idan ina da hali dayafi hakan don ke kawace ta arzikin da akeson mutum ya samu ai bari wanan ya sauke ku a gida idan zai tafi yanzu.

   Kai Master kake kowa koran mu kake sonyi mun rakoka dakin amaryan ka ko da badon yan matan nan ba babu inda zan tafi yanzu amma kaci bashin hakan gareni.

   Allah dai ya nuna muna lokaci lafiya naji Ahmed din yana fadawa maishi suka kwashe da dariya hannatu ta leko daga kofa tana fadin zahra zamu tafi insha Allah da safe zan taho in dubaki.

    Ki taho ina da safe wanan mai rawan kan zai barki ki shiga gidanai da safe sai ko kinyi zaman jiranai a waje indai  Amadina.

    Daga nan naji fitan su suna mika min gaisuwa suka fice daga dakin can naji shiru harshi falon yayi tsit can sai naji dawowan shi yana rufe kofan shigowa part din mu alaman ya gama fita ke nan a ranan.

    Ya shigo dakin da sallama naji ya rufo kofan falon lokaci guda ina danjin motsin shi a falon can na yayi sallama ya shigo ya aje abu yana fadin .

   Zahra ki tashi ki danci wani abu sai kisha magani gashi na karbo maki a chemist saidana muskuta nake fadin ba zan iya cin komai ba a yanzu murya can ciki nake magana.

    Ruwan zafine sai madara da kaza ko kadan ne don Allah ki tashi ki taba zaifi ki kwanta a haka da yunwa a cikin ki ai ya fada yana zama kusa dani daidai kafana.

    Na dan jaye kafan tunda ban zama irin haka da maza dan dama ya musa da mukayi sabo sosai dashi ko ina kwance ne zai zauna a bakin gadona idan ya shigo dakina muyi magana.

  Saiko yau dashi Ahmed din yayi hakan gareni sai naji abin wani bambarakwai gareni gashi dai ina son in daga don hadani da Allah da yayi kuma yayi zaune inda zan tashi din lokacin.

    Ko yagane me nake tunanene sai naga ya mike ya nufi bandakin ya dan leka kamar ruwan dake ciki ya duba a lokacin ya fito daidai lokacin na mike ina dai ganin juwa a idona.

    Sannu yai min daga kofan bayin inda yake tsaye yana bina da kallo kamar ranan ya fara ganina a duniya nasan lokacin da da hali dayace zai daukeni ya kaini bayin saidai babu fuskan hakan gareni.

   Har nakai bayin yana min sannu ya rufo kofan da kanshi na dan jima a ciki don har brush nayi ko zanji dadin bakina lokacin sai dana gama na fito.

  Kallo daya nayi mai na kawar da kaina gefe na dan rabashi na wuce zuwa gado na zauna a bakin gadon ina mayar da brush din a cikin jakata na samu ya bude kayana ya ciro min rigan barcina ya dora saman gado.

   Shi kuma yana tsaye daga shi sai boxer irin na maza da farin singlet a jikin shi abinda yasa jikina bari ke nan don ban taba ganin wani mahaluki hakan gabana a fili ba .

   Sannun dai ya kara min yana fadin ga kayan barcin ki nan na fito maki dashi ko wanan din zaiyi maki ban sani ba nagode kawai nace ba tare dana dago kaina kalleshi ba.

    Ya juya zuwa bandakin ya jima a ciki don ban debe tsamani idan ba wanka yayi ba a lokacin sai gashi ya fito yana saye da jallabiya mara hannu brown a jiki  shi da ganin rigar sabuwace a ranan ya fara sakata a jikin shi.

    Na dan kai kishingide don yadda yanayin jikina nake jinshi lokacin kallon inda kayan makulashen daya aje yayi sai naga ya nufi hanyar waje ina jinshi ya bude kofa can ya dawo ya rufe ya shigo hannun shi yana dauke da plate da cups biyu.

   Ya aje ya bude ledan ya juye naman da har lokacin yana da sauran zafin shi sai kamshi suya ke tashi wanda ni kuma a lokacin nake jin kamshin na hawa min kai.

    Ina zaune a inda nake ina kallon shi ya gama ya kalloni yana fadin bissimillah kona kawo maki a nan da sauri na tareshi da fadin No ka barshi na taso ruwan zafin kawai zansha.

    Wani kallon mamaki ya watso min kafin yace ruwan zafi kawai naman fa ba zakici bane don kifa na sayoshi kuma gashi bakici komai ba ?

   Bana jin cin komai ne a yanzu don tun safe dana karya ban iyacin komai har yanzu da sauri naji yace dani what kina jiran me har yanzu oya tashi na baki a baki idan cin yake maki wahala.

   No ba haka bane kawai dai bana jin dadin komai ne a bakina yanzu ruwan zafin is OK idan nasha sai naga ya mike ya dauko cup din ruwan zafin  ya nufoni dashi.

    Yana zuwa yakai zaune a kusa dani har turarensa na maza daya shafa yana shiga hancina a lokacin ba kuya naga yana kokarin mika min kofin shayin a baki da sauri na dakatar dashi daga hakan da yake shitjn yi cikin kunyanshi nace.

   Haba dai zan iya sha dakaina ai bakya son na baki da kainane kefa yanzu sauraniyatace ke dan murmushin ciki na sake dkn ni mamakinshi ma ya hanani kara sakewa.

  Saboda abubuwan da yake min a yanzu zakace munyi irin sabon hakane dashi tun farko don gaba daya ya juye min ya koma wani Ahmed din na daban ba wanda na sani a baya mai alkunya ba.

    Hannu na mika ya sakarmin cup din na dan kai bakina ba laifi don da dan zafi kuma naji dadin hadin sosai saboda kamshin kayan yajin dake tashi a ciki.

   Na kurba yakai sau uku yana zaune ya kura min ido yana kallkn yadda nake kurban ruwan tea din sai nayi kokarin ajewa saboda naji ya isheni a lokacin.

   No shanyeshi fa zakiyi sai ki dan ci naman nan na baki magani sai ki kwanta nace don  Allah ka barshi wanan din ma is Ok ai basai naci nama  ba.

   To ki kara ruwan zafin ga maganin a hannuna sai kisha don dole naci gaba da kurban ruwan shayin har saida na kusa shanyewa na miko mashi cup din a lokacin ya miko min maganin daya bare dole na karba nasha da kyar don banson magani a rayuwata.

    Karban cup din yayi ya shanye sauran wanda na rage din a ciki sai mamakin hakan da yayi ya kamani bayan yashane ya mike daga inda yake zaune yana fadin .

    Bari na saka wa yancan a cikin fridge kada su lalace da safe sai ayi amfani dasu ya kwasa ya fita ya dan jima bai shigo dakin ba don koda ya dawo har barci ya daukeni lokacin.

   Ya gama abinda zaiyi ya kashe wutan dakin tare da hawowa gadon daga can barin gefen da nake ya kwanta ya fara karanto muna adduan kwanciya don yasan yadda nake din nan karfin hali kawai nakeyi ba lalai bane na iya yin addua a lokacin.

   Ban tashi farkawa ba don maganin ciwon kan da nasha sai wajajen  karfe uku da rabi na dare koshi fitsari ne ya falkar dani lokacin na tashi.

    Dakin da duhu sosai sai gabana ya fadi don sam lokacin na manta da inda nake a ranan ga nauyin mutum da nake ji a kusa dani lokacin.

  Nan na fara dan lalaben wayata dana aje a gefen gado na jawo na haska a hankali tare da tuno a inda nake a lokacin ne naga yadda muka kwanta a gado daya tare dashi.

   Don kusan jikin mu yana hade da juna dama nayi tunanen hakan don dana falka naji nauyin mutum a kusa dani saina fara kyarma.

    Muryan shi naji daga gefena yana fadin lafiya dai ko da kyar na iya bude baki nace dashi ina son in shiga bandaki na kewayane.

   Mikewa yayi zaune kafin na tashi ya jawo wayan shi ya kunna touchlight din shi yana fadin na rakaki bayin ne zan iya na bashi amsa da sauru na samu na mike zuwa ban dakin ga wani irin barci a idona lokacin.

    Ban jima ba na fito na kwanta can kafin barcin ya daukeni naji mikewan shi ya shiga bandakin bandai san fitowan shi ba ashe alwala yayi yazo ya tayar da sallah.

    Yana nan zaune akai kiran sallah farki ba a jima da kira ba yaji ana kwankwasa kofan dakin namu daga waje bai daga ba kuma baiyi magana ba.

   Can kuma kamar bayan wasu yan mintu ya kara jin a kara dukan kofan a lokacin ta mike yayi gyaran murya yana mamakin hakan yau gareshi.

  Shida zai bugawa mutane kofa su tashi shine akazo aka bugawa kofa ya tashi waye da wanan aikin garwshi haka sai yaji ranshi ya baci da hakan da akai muna din.

    Ban dakin ya koma ya shiga ya sake dauro wani alwala ya fito ya dan shafawa jikinshi turare kana ya nufi kofan ya bude ya rufo daga baya ya barni a ciki.

    Jin fitan shi yasa nima na mike na shiga nayi alwalana na fito na zo na tayarda sallah daidai da lokacin an fara sallah bayan na idar na dan dade a zaune wurin ina adduan samun zaman lafiya a tsakanin dama sauran mutanen gidan.

   Na shafa ban koma na kwanta ba saida na gyaro dakin ko ina na saka kamshi nayi wanka har lokacin bai dawo part din namu ba na samu wuri na kwanta again sai barci.

  Duk lokacin gari bai gama haskawa ba ya dawo gidan ya shigo a zaton shi zai samu banyi sallah ba har lokacin  sai ya samu nayi sallah don idonshi ya fara tozali da gyaran dakin da nayi ga kuma kamshi na tashi tun daga falon.

   Ya karasa ciki ya ganni a kwance na dunkule da alaman barci nakeyi a lokacin don haka baiyi wani dogon motsi ba ya koma falo ya kwanta shima.

   Dije kega mutumin ki ko yau ko lekomu baiyi ba kuma naji dawowan shi tun dazun gashi matar nashi har gari yayi haske haka bata fito ta gaida mutane ba.

   Haba haba yar nunu yaushe gari ya waye da kika hwadin wagga maganan  indai Amadina yasan abinda yakai ba sai an koya mashi ba.

    Wane har yaushe yake ni gudu nake yazo ya saba da hakan daga baya kuma yazo ya damai keki rabani da wagga maganan don Allah har yaushe muka fara tantance haline akan matatai yanzu.

    Shiru tayi don bata so jin hakan ba daga bakin mahaifiyar nata so tayi ta mara mata baya suyiwa tufkan hanci don kada ya zarce da hakan saboda yaran masu kudi sai suyi kokarin mayar da miji bawa garesu.

    Balle wanan da ubanta yake hamshaki kowa ya sanda hakan dole ta dinga sashi a hanya don in tabi ra dije biye mashi zatayi suyi abinda ransu keso ana kallon su.

    Shara ta farayi na gidan kafin can taji bundan kofan part din yaran bata dago ba don taga ko waye saboda tasan kowaye ma zata ganshi yanzu ai tunda taji motsin mutum zai fito.

   Inna ina kwana ta dago tana amsawa kafin ya katseta da fadin su hauwa suna inane suka barki kina shara da kanki haka ?

   Kwana sukai basu tashi ba na kuma wurin duk yayi ba dadin gani kada a shigo a samu wurin ba gyara amma ai inna ya kamata a tashesu hakana tunda gari ya waye ko ?

    Ai tashin su zanyi suyi sallah yañzu idan na gama yasa kai ya wuce ba tare da yayi wani magana ba sai jin muryanshi tayi yana tayar da yaran nata.

    Haka sunka saba dashi tun can kamar yaran nan ace ayi sallah suna kwance suna kwana sai lokacin da sunkaga dama sunka tashi don kansu.

   Dijece tsaye daga kofan ta take fadin hakan shi kuma yace gasu hauwa a gida ance sai inna tayi shara da safen nan .

    Haka tagga dama dauri ta koya masu komai amma yanzu haka gozai gozai yaushe zasu iya hakan nan dai yayi masu fada ya fice daga gidan can andan jima sai gashi ya shigo da leda biyu a hannun shi ya shiga ya aje masu guda ya fito ya shige part din mu da dayan a hannun su.

    Inna keji kamshin kwai a ledan da yaya yya hita dashiya karamar nanwar shi ke fadin hakan sai uwar nasu tace kona jiya a a zanyi ?

   Tunda mu kauyawana bami iya shan shayi da kwaina sai bussashen burodi tunda anga na kawai ta fada tana wani yatsunan fuska lokacin.

    Inna a dauko kofi a raba muna ko diyar ta sake fada kai kawai ta gyadawa yar nata don takai cin da ya kume mata zuciya lokacin .

  Kafin ma tayi magana yar nata ta mike zuwa dauko kofin ta sai ganinta tayi ta dauko tace su bude su fara zubawa tana bude kofan saiga kumshin kwai suma a cikkn nasu.

  Lah inna ke gani ashe muma yasa a faso muna kwanan yarinyar ta fada tana rawan jiki zata bude ledan daga inda dije take zaune a kofanta ta fara fadin waga diya akwai bakin kwadai gareki.

    Uwar garke dake gefe can ta baya yanzu don sai idan kamar zaka bayin su Dije a nan zaka gansu an dan sakayasu a wurin.

   Kuka akuyan keyi sosai har suka mayar da hankalinsu garesu suna fadin dabbobinga kukan mi sukai da safe haka.

    A can cikin barcina kamar a dakin akuya ta shigo sai zabura nayi na mike don kukan akuyan daya daki kunnena lokaci guda na mike ina waige waige a tsorace daidai nan yayi sallama ya shigo dakin.

 

No comments