Breaking News

TUMFAFIYA 64


 

 ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/2, 9:15 AM] +234 703 080 4044: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH  ,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

6️⃣4️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

 

Daga school gidan muna na nufa tare da hannatu muka shiga saidai mun fara zuwa wurin ummah mun gaida ita mukaci abinci bata fada muna komai ba sai bayan munyi sallah muka shirya zuwa part din mama don mu gaishesu.

   Tun kan mushiga muke jin  dan hayaniya a part din tunda nasan an haihu don haka na dauka ai yan barkane suka cika wurin ake hira mukai sallama muka shiga.

   Mama gwaggo Rakiya yar dakin mama Rukkaiyan mu da yan uwan mama guda biyune a falon suke wanan cacan bakin ashe nashiga na gaidasu a cikin fara,ana.

    Ba laifin sun karba min akai gaisuwan mutunci nace ina maijegon mama tana ciki ta fada cikin wani irin murya mai sanyi da rashin fara,a.

   Sauran ko sai bina da kallo sukeyi na kwakwakwan na mike zuwa cikin hannatu ma ta biyoni a baya tunkan mu shiga dakin nake jin muryansu ita da hjy hakan yasa nagane hjy na dakin a lokacin don na dauka ta tafi gidane.

   In bako Aisha ba wa hjy zatazo ta zauna dashi a gida don ya haihu saisu yan gaban goshinta da basu laifi a wurinta komai sukayi daidaine ko yanzun ma ganinta baisa naji komai ba irin da danakan dan tsargu don nasan sai ta saka min tsarguwa kafin mu rabu.

  Idon Aisha din yayi hulu hulu ga hawaye dake gangara a fuskanta tana shara lokacin ba bata lokaci nace subbahanallahi maijego kuma yaya hakan da kuka ?

   Haba dai meyayi zafi kike kuka waya taba muna ke kuma barta da tsiyanta an bata hakkuri tayi shiru kada tajawa kanta wani ciwo taki ya barta mana in iyayyenta sun sa ya rabu da ita sai me kantane farau irin hakan ko itace karshe.

  Shi kaddara ai yana kan kowa waye baisan kaddaraba kuma hjy ke fada tana miko muna yar da aka hana mu dauketa lokacin.

     Na karbi yarinyar na dan dubata na rasa dawa tayi kama tsakanin uwan da uban na mikata gun Hannatu ta karba tana bin yarinyar da kallo naga har tana gyara mata hannu.

   Sheshekan Aishan ne yasani dago kaina na kalleta ina fadin wai meya farune kike wanan kukan naji hjy na maganan nan.

    Barta wai don iyayyen mijin sunzo jiya barka sunce basu yarda da yarinyar nan jininsu bace don haka ba zasuyi suna ba shine take wanan irin kukan kamar ranta zai fita.

   Ashar na lailayo na sake nace da kazan uba ba yarsu bace dawa yarinyar tayi kama bada shi jamil din ba don iskaci fadi kedai yar albarka kema ai kya fada.

  Don ga abu a zahiri kowa nagani amma haka yarshi jiya ta rufe ido tayi muna cin mutunci a gidan nan kamar ba gobe gareta.

    Muryan hannatu danajime ya katse min magana tana fadin yar nan fa kamar bata da lafiya nake gani asibiti mai sukace game da ita ?

    Da sauri najuyo ina kallon yarinyar gaskiyane nima naga hakan don nufashinta bai sauka sosai a lokacin hjy tace dannewan cikine yake saka hakan sai hannatun ke fadin a a hjy gaskiya da kunkaita asibiti zaifi.

    Haka takeyi tunda aka haifeta nayi magana sunce ba komai bane idan dare yayi ma abin yafi worse bata ma numfashin wani lokaci kamar ta mutu.

   Anya ba free matual bace yarinyar nan kuwa hannatun ta kara fada don gaskiya ba normal take sauke numfashinta ba abinda nake gani ke nan uwarta fada duk shi ya kawo matsalan nan ai tunda bamu cika Nine months ba.

   Da sauri hannatu ta kalleni nace ke nan sun sani suke son dorawa mutane laifi akai gaskiya sai an nemawa yarinya hakkinta kada su batawa mutane suna a banza.

   Ai mahaifinku yana tafe yace yau din nan idan yazo duk yadda za ayi sai ayita amma basu isa su taka mutane irin haka a kyalesu  inbanda ma ita Aishan data nace wa wayan nan mutanen banza aitun farko sun nuna suba mutanen arziki bane dama.

   Mamace ta shigo yar mama tayi muna tsaye tana signal kada a fada muna caraf a idanun Hannatu sai hannatun tayi saurin fadin yanzun dai ayi gagawan kai yarinyar nan asibiti aji meke damunta shiyafi.

    Wanan yar ne za akai asibiti yayan mama din ta tambaya cikin mamaki da sauri Aisha din tace ba rayuwa gareta ba mama itama mama ?

    Ni gaskiya idan ba zaku   kaita ba naje na kaita a dubata don hankalina yana tashi gaskiya da yadda yarinyar nan takeyi da dare Aishan ta fada cikin tashin kunya.

  Ke arrr uwayen ma naki baki barsu ba shiyasa yar mijin naki keson ta karantawa mutane hauka don tana yar iska kin nuna kina mutuwan son dan uwansu, kamar mai bakin uwa a kai.

   Nan dai ta bushe ido tana ba hjy amsa har yar mama din taje ta kira mama a falo tazo ta duba hjy sai cewa tayi mune da iyayin mu kazo da zancen akai ya asibiti.

   Mama din tace eh gaskiya hjy yar nan na bukatan ganin likita don yadda take numfashin nan baya sauka abin a dubane sai hjy din da yar uwan mama suka mere baki waisu basu taba ganin an kai da asibiti ba haka .

   Mudai bamu fito ba saida muka tabbatar sun tafi asibitin wai ashe wani cleanic ta haihu dama suna zuwa asibitin aka hausu da fada kanme suka zauna gida da yarinya haka tana jin jiki aka dora mata oxygen nan take irin na yara.

   Bayan na koma part din ummah nake tambaya ashe rikici akeyi tsakanin su mama da dangin mijin Aisha sunce basu yarda da yar nan ta dansu bane ?

    Fitar da bakinki cikin zancen nan kada sunan ki ya fito a zancen nan ki saka masu ido suyi abinsu iyakan ki dasu gaisuwa shine ya dace a tsakanin mu.

   Mutanen da ko barka na shiga gaidasu suke nuna min wani hali har boyon yar sukeyi suna zaton zan mata wani mugun abune shiyasa na bar zuwa na gaidasu yanzu tun da naje sau biyu.

  Shiru nayi ina dan tunane kafin nace munyi karanbanin fadin yar na bukatan zuwa asibiti don bata da lafiya kafin ummah tayi magana sai hannatu tace in sun boyeta ai ba zasu boyewa Allah ba shidaya halicceta.

  Ummah kiyi hakkuri don mun rigada mun maganta hakan garesu sai ummah din batace damu komai ba ta dauko wani hiran munayi akabar zancensu.

   Hakan yasa ban dawo gida ba sai dare karfe tara da wani abu na shigo gidan part dina na nufa kai tsaye na bude na shiga saidana kwabe kayan jikina na watsa ruwa na fito zuwa cikin gida don in duba Dije.

    Na shiga da sallamana suka amsa min na gaidasu don inna bata gidan ta fita unguwa lokacin don na tambaya inna na dakine sukace ta fita dazun nan saidai Dije.

   Na shiga na gaida Dije din nayi mata ya jiki tare da tambayanta kota sha maganinta tace tasha dazun da yamman nan ina zaune muna hiran jaririyan da Dije innan ta dawo tana fadin har yanzu wanan bata dawo ba ke nan.

    Ta dawo tun fitan ki gata nan dakin Dije ma zaune suna fira jin hakan yasa na fito na samu inna din ina gaida ita nace na samu jaririyan bata da lafiya ankaita asibiti yanzu hakama an bata gadone suna can.

    Ikon Allah jaririyan aka kwantar to Allah ya sauwaka ta fada tana shiga dakinta ban koma dakin Dije din ba na nufi part dina har na fara tafiya naji Asmau na fadin kada ki rufe muna nan shigowa fa.

   Na amsa mata da to na wuce abina nadai jin muryan inna a lokacin amma ban tsaya sauren abinda take fadi ba don kona tsaya rainane zai baci a banza.

    Kamar yadda suka aje goma na safe suna kofan gidan abokin nasu suna jiranshi bai bata lokaci ba ya fito tare suka zagaya dashi dukkan gidan dan uwa daya kamata yana zumunci tare da alheri garesu.

   Hakan yana iya jawo mantuwa ga dan Adam shine hikimarshi na ziyarta wanan karon yana masu alherin daya dace dasu sai biyu ya dawo gida a gajiye cikinma baije wasu wuraren ba ke nan don yawa garesu sosai a garin.

    Jin hakan da hjy Korau tayi cewa ai yau Dan gaske ziyara yake kaiwa yan uwanshi yana kuma masu alheri sai hassada da bakin ciki irin na kishiyar uwa mai mugun nufi ga dan kishiya ya darsu a zuciyanta.

   Abinda bata son ji ke nan ace shine ya zama tauraron gida yana tallafa masu harda diyanta da yan uwa duk dako wace uwa nason hakan a dakinta ai.

   Sai ranta ya baci sosai ta shiga daki tasa jikanta ta kira mata yarta hjy Yabi duk da a yanzu Yabi din ta dan bata baya amma hakan bai hana tana aiko mata da alheri irin na uwaye.

  Ba kuma wani abune ya hadasu ba sai yadda taso ta juya hjy yabi dinne da irin mulkinta taki yarda dashi shine ya kawo masu sabani a tsakaninsu suka bata baya suna abu tsakaninta da yan uwanta yanzu tunda sun bude ido da hakan dama.

    Tana daukan wayan take fadin bayan sun gaisa yau dai ga irin abinda nake fada maki nan yana faruwa da mijin ki dama ta yaro kyau yake baya karko.

   Na fada maki kada ki yarda ya rabi yan uwan nan nasu ko abokansa su Jauro amma kin nuna ban iya ba don komai da mukayi an fada muna har in hakan ya faru komai zai lalace muna tun farko.

    Hjy ban fahince kiba hjy yabin ta fada daga bangarenta nan dai ta koro mata irin hidiman da yayiwa yan uwa da abokan arzokinsa na baya yadda rahoto yazo mata daga bakin babban data da aka bashi ya raina abinda dan uwan yayi mai don haka yaji zafi yazo yana fadawa uwar nasa.

    Komai ma ina ganin yanzu ya lalace don ko wanan tafiyan bai sanar dani ba zaizo gida saida ya iso mukai waya yake fada min tun jiya hankalina a tashe yake don ina gudun yaje Gembo wurin wa yan nan yan uwan nasa.

  Yaushe kuma dan Amo ya fada min yaga sun dauki hanyar zuwa Gembo din nasan kuwa har Garba Chedi sai yakai a can ne komai zai karasa lalacewa kuwa kuma kinsani .

 Don suma ba zama zasuyi su zuba masa ido yana haka su fita batun shi ba tundai wanan malam Amadu da baya kaunan mu ko kadan.

     Sunyi waya sosai da tsohuwar don itama hankalinta a tashe yake lokacin suna neman mafita akan hakan kada abinsu ya koma masu daga baya.

    Karfe shida da wani abu na safe ya kira wayana na dauka muka gaisa yake fadin yaya zamuyi ki karbi sako a tasha don driver zai kawo maki kaya yau din nan.

   Kaya na tambaya cikin mamaki yace eh kayan da zakisaka wurin fita sunan yar uwanki na sayo maki tare da takarduna na hado don naga kamar ranki ya baci ranan.

    Bai baci ba tunda kaine maiyin aikin bani ba yace naji zaki bar wayan ki a gidane Aisha taje ta karbo maki ko yaya za ayi din nasan zaki shiga school yau.

    Zan dai zauna har drivern ya iso da sakon na karba da rana sai in shiga school kasan wayata bana ba kowa su halaka min  ita.

   Hakane kuma why note ki shiga school din idan ya kira ya iso sai ki fito ki karbo eh ko hannatu saita karbo min amma da baka wahal da kanka wurin saya min kaya ba tunda ina dana sakawa ai.

    Haka nayi ra,ayi saidai idan kin raina amma ba zanso su ganki da wasu kayan da suka sanki dashi ba a wurin ya fada cikin wani irin murya.

   Idon na lumshe tare da jin tausayin kanmu a lokaci guda a raina nace Allah sarki master yagama min korafin baida kudi yanzu kuma ko ina ya samu kudin da har ya saya min kayan fita suna oho ?

   Watau shidai master sam baya son yaga na kasa a cikin yan uwana ko yaushe yana dai iya bakin kokarinsa dani yadda kowa zai fito aganshi fes a wurin taron shima haka yake son a ganni ke nan ban bambanta da yan uwana ba.

   Na dade zaune ina tunanen zuci kafin na mike na fara shirin fita zuwa school ina kuma tunanen yadda zan samu in karbo sakon ba tare da an samu matsala daga gareni ba don saura kwana biyu sunan yar Anty Aisha.

   Duk da suna asibiti ummah ta fada min da mukai waya za ayi taron sunan mama tace ba a janyeshi ba yadda yake nasan mama da bidi,a kam.

   Don  hakane muke tashirin suna mukan da sauran yan uwa son naji ance su Abbama sunzo har da hjy karima da yanzu ta daina zuwa gusau din ban kuma san dalilin hakan ba tunda ba hurumina bane sanin halin da suke ciki.

    Gashi kuma washegari nake son in zauna gida inyi kitso da kumshi da badon hakan ba da ranan na zauna gida ban fita ba ko don sakon dake tafe mani din.

   Sakon ya iso lafiya kuma hannatuce taje ta karbo min din kakken atamface barauniyar super an mashi dinki half gown dinkin ya kwanta yayi kyau sosai dashi don yan zaria badai dinki ba kam sai in baka da kudin dinkin kwarai.

    Da wuri na dawo gida don Aisha ce zata tsafe min kaina na wanke washegari aimun kitso da kumshi a nan makwabtan mu wata mace ce muka samu yar maiduguri matar wani police take kitson da kumshi koshi yan gayun garin sun bata ta yanzu don sai anyi bucking dinta kafin ka samu .

  Don haka sammako zanyi zuwa gidan nata ta gyarani bamda niyar girki don haka na nufi part din nasu da kayan tsefe kan nawa.

   Wurin Dije na fara shiga muka gaisa ina fada mata nazo Aisha ta tsefe min kaine gobe ba zan fita ba zan tsaya gyaran jikine zuwa rana sai in leka gidan mu din.

   Muryan inna naji a kofan tana magana na fito ina gaida ita nace Aisha gani nazo zancen tsifan kai din tace a nan zamuyi ko a part dina lokacin naji inna tace Aisha.

    Ki dauko wanki ki fara min kafin ku zauna kuma ki dora girki idan kin gama jin haka kawai yasa na juya zuwa part na zauna na fara tsifan kan sai ga Asmau tace na kawo tayi min yanzu ta dawo Aisha ke fada mata abinda ya faru ita inna kome yasa take haka oho ?

 Ni dai ina jinta ta gama min a cikin lokaci na wanke na dunkule don yanzu ba zancen zuwa saloon bane gareni gaskiya don duk wasu abubuwan rayuwa na rage yinsu a yanzu din.

    Don kada yace sai ya matsawa kanshi yai min tunda nagane halinshi na kwatantawa ban faye yin abin da nakeyi a gida ba yanzu.

    Washegari sammako nayi zuwa gidan kitson yaran sun nuna min suma suna so saidai suna kame kame nasa akai muna tare dasu aka gama na biya karfe biyu muka dawo gida.

   Don mune na farkon zuwa munyi sa,a an gama muna cikin lokaci don inna bata da kunya sai gata tana jin dadi har tana nuna na diyan yafi kyau a gabana ni dai ban tsaya kulata ba.

   Washegari suna suka kuma nuna zasuzo gidan namu nikan goma na safe ina gida don ina son inga Abba ingaishi don mun dade bamu hadu ba.

   Nayi sa,a sai gashi ya shigo ina daki da kanne na nan na fito ina gsidashi da mamaki ya juyo yana amsawa tare da dan kura min ido kafin yace dani .

   Yaya maigidan naki nace yana lafiya yana can school zaria yace har yanzun bai karasa karatun ba ke nan na dan amsa da eh Abba.

  Badai kuna lafiya ba nace lafiya kalau muke Abba ya danyi shiru har ya bude baki kamar zaiyi magana sai kuma ya juya yana magana da ummah.

  Na daga daga inda nake zan wuce naji yace kina dai kula da karatub ki yadda ya kamata ko nace eh Abba to ki kula zai maki amfani wata rana koda koyarwa ne ki samu nace nagode Abba.

   Daga hakan shima ya fita wani iri naji a raina bayan fitan Abba din part din hjy karima naje muka gaisa da ita itama din dai wani kallo take min da har na tsargu.

   Daga wurinta na nufi part din mama ina gaida mutanen dana sama kowa dai idon shi akaina na rasa meyasa hakan sai kawai na tsargu na tashi na koma part din mu a nan su hannatu dasu Aisha da sukazo min suka sameni nadai kaisu sun gaisa da me haihuwa kafin yamma muka amshi abin sunan mu ummah ta kara min da wanda aka bata muka dawo gida.

No comments