Breaking News

TUMFAFIYA 65


 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/4, 7:48 AM] +234 706 815 1331: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH  ,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

6️⃣5️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

 

Na gaji sosai dana dawo don haka na kwanta da wuri a ranan sai washegari dana tashi nayi dan gyara kafin in in fita na kwashi takardun nasa don ranan nake son in turo wa Brother Bisi dasu kada yaji shiru.

  Na fito da shirina zuwa cikin gida don in gaidasu kuma in sallamesu na samu Dije a waje tana cin kayan bukin a wanan lokacin ya kirani a waya na dauko na daga ina fadin bari mu gaisa da Dije da tana hangoni tace yau kina shiga makaranta ke nan nace eh kwana biyu banje ba kada a wuceni da karatu sai na manta wayan a kunne take.

    Nayi mata inna kwana kana na nufi wurin inna da itama tana zaune daga kofansu tana cin nata kayan bukin nayi mata inna kwana cikin ladabi.

   Ta amsa min yadda ta saba ba yabo ba fallasa na juya muna gaisawa dasu Aisha daga cab Asmau ta leko ta daki tana fadin wai matar yaya wanan dayan mai cikin din da muka gani itama yar uwankuce ?

   Nace eh itace akai muna aure rana guda mu uku kai amma duk kin fisu kyau nisa ba kusa saidai su gwada maki jin dadi yanzu kawai don suna da sallo sosai wallahi.

    Kai ji yar nan da wani zancen banza su ba diyan masu kudi bane kuma yanzu suna aure me kudi in akwai kudi ina ruwan mutum da muninka ?

    Wani kallon takaici na watsowa inna din lokaci guda nace amma kada ki manta asalinmu daya duk abinda suke takama dashi dashi nake takama nima ai kudin mazansu wasuke ba ?

    Don nawa mijin baida kudi a cikon mu bashi ke nufin na koma baya ba Allah bai bashi ba yanzu in Allah ya nufa zaiyi nan gaba sai muyi harma kila mufisu arzikin da suke takaman dashi a yanzu.

    Wanan shine maganan gaskiya Dije ta fada daga kofanta ni kuma ina fadin haka na juyo zan bar wurin naji inna tace yanzu dawa kika wanga magana cikin mu ?

   Kemana Dije ta bata amsa yara na maganan su mikaiki saka masu bakinki ciki don wanga maganan ma sam bada wagga diya kikayin shiba danki kika hwadawa magana shida hannunshi bai kai ba.

    Sam na mace wayan yana kunne har lokacin saina dawo na fada a daidai lokacin da inna ke babatun fadin don na saka bakina ba gaskiya na fada ba ai banki mijin nata yai arzikin ba nima.

  Dije duk ake magana sai kiyi kokarin juyawa mutum maganan shi yanzu meya kawo zancen dan dije cikin maganan nan ?

  Nidai na fita ina jan tsoki ashe yanata magana a wayan banji shiba karshema dana fita na jefa wayan a cikin jakata jin nafice daga gidan yasa ya kashe wayan tasa a lokacin.

   Na isa makaranta daidai malamin zai shiga don haka kusan a tare muka shiga dashi lokacin bayan mun fitone muke hiran da hannatu dataga yadda nake rai bace a ranan.

   Sam har ya kwana biyu ya koma basu yarda sunyi zancen Ahmed dashi ba kamar yadda malamin ya fada masu iya lokacin da zasu kai kafin su tunkareshi .

  Hakan yasa suke kyale har ya tafi baisan komai ba gashi har Ahmed din ya kira Alh jauro kamar yadda ya saba kiransu lokaci lokaci daya bayan daya yana gaisawa dasu a matsayinsu na iyayyensa da suka tsaya mai a yanzu din cikin lamarinshi.

  Suma hakan sukan kirashi suji lafiyab mu don hakanema nake dauka da mahaifinasa yake waya wani lokaci sai daga baya na gane ba haka bane ashe.

   Koda ya koma komai bai canza ba tsakanin shi da hjy Yabi har yanzu zaman nasu suna dai yinshi a takurene da juna don sam yanzu baya shiga tsabgansu.

   Ita dai ke kokarin taga sun gyara koshi don tacinwa manufartane akanshi yanzun din kuma yasan da hakan don akwai ranan data fita ya kira mai aikinsu ya tsureta akan in bata fada mai gaskiya ba zai koreta a gidan.

   Jin hakan yasa fa kwashe komai data sani ta fada mai game da hjy saida hankalinshi ya tashi sosai bayan ya gama jine ya sallameta da jan kunnenta kada ta yarda ta nuna mata yasan da hakan don hakan zai jawo ta iya rasa aikinta idan ta shine tunda ta taimaka ta fada mashi ba wani mahaluki da zaisan wanan zancen.

   Tayi maigodiya shima yace ya gode amma duk lokacin da taga wani abin cutarwa a gareshi don Allah ta taimaka ta fadamai tayi alkawarin hakan.

   Haka yasa ya kara jan jikinshi da ita sosai dan dama dama diyanshi yana mu,amula dasu yadda ya kamata ko wani mahaifi yayi da dansa.

  Ya dawo da kamar sati uku tana dawowa unguwa ta hango yan aikina aikin gyaran dayan part din dake rufe a gidan da mamaki ta fito daga dakin tana tana binsu da kallo har zuwa wurin su.

  Basu dakatar da aikin da sukeyi ba sukaci gaba dayansu take tambaya yace maigidanne ya kirasu suyi aikin yana fadin haka yaci gaba da aikinshi ya barta nan tsaye tana ci gaba da kallonsu.

    Ciki  mamaki da samun daurewan kai ta taka zuwa part dinsu yarta ta sama a dakinta ta shiga a rude yarinyar na kwance tana waya dakin duk ya turare da hayakin shi-sha a lokacin.

    Shigowar uwar ta dan dago tana fadin mummy lafiya kuwa na ganki a haka kamar a rude salima wanan uban hayakin da kika turara a daki haka anya kuwa zai baki lafiya karshe ?.

   Mum wanan ba komai bane fa kin sani yarta fada ta mere baki uwar tace daddyn ku ya fada maki za ai gyaran wancan part dinne kafin ya fita ganin yakan dan zauna da yaran yayi fira wani lokaci yasata tambaya haka.

   Haba mum bai fada maki ba ni zan sani kawai dai kila yaga kayan cikin sun dadene yasa a gyara diyar ta fada cikin ko in kula sanin suna yawan gyaran gida akai akai.

   Salima ki dawo cikin hankalinki ki natsu ki fahinceni maganan abinda ke shirin faruwa a gidan nan nake maki kina karanto min hauka ke kuma.

  To ki sani idan ba aure zai kara a yanzu ba akwai wani plain da yake shirin yi dolene akwai abinda yake shiryawa bada sanina ba a yanzu ya zama dole in sani meye manufanshi da hakan idan ya shigo.

    Amma mummy daddy baya gari ya fada min da safe nan  kafin ya fita zai tafi South Africa shida Alh badaru zasu wani business a can nima naji hakan ne lokacin da Alh Badarun ya bugo mai waya suna magana.

    Mamakinta kara ya fito a fuskanta har tana watsawa diyar wani irin kallo kamar itace tayi laifin a lokacin yarinyar ta gand meke zuciyar uwan da sauri tace.

  No mum nimafa da suka gama wayanne ya fada min cewa Alh badarune zasu tafi South Africa tare da shine a yau din.

 Amma salima ya kamata tun lokacin ki sanar dani ba yanzu ba don fadin baida rana tace sorry mum na dauka aikin sanine ?

  Bata iya yin magana ba lokacin sai dagawa da tayi ta dan kure yar nata da idanu na dan lokaci kafin ta juya ta bar dakin zuwa nata dakin.

  Gado ta fada hankali tashe a hankali ta mayar da idanunta rufe ta rasa ta ina zata fara tunane ma don yadda take daukan zancen yafida nan a gidan nan yanzu.

  Tana nan kwance tunanen ta ya tsaya akan danta yasir lokaci guda don shine kadai zai iya takawa mahaifin nasu burki a yanzu kafin ya idda nufinshi dake cikin zuciyarshi akansu.

   Don ita salima da ita da babu a yanzu duk dayane kamar ba mace ba bata ko gwada kishin abinda mahaifin nasu ke mata a yanzu.

   Bayan tunanenta ya tsaya a yasir din ta samu zuciyanta ya dan rage zafi lokacin ne ta jawo waya don labartawa yarta abinda ake ciki game da mijinta.

  Yadda take a rude hakan ta labartawa yar uwan nata komai hankali tashe itama yar uwan ta rude ta kwaso ashar ta dura masa tana fadin me yake nufi da gyarab daki a yanzu.

   Shin aure yake nufin zai kara ko kuma dai shine zai koma ciki a yanzu ya barku nan haba dai yayata yaya za ayi shidake tsakiya ya koma gefe ko kin manta yadda tsarin gidab namu yakene wai ?

    Tsarin dama na mutum biyune nasa a tsakiyan mu ba sai wani yaga dan uwa a cikin mu ba inyaso hakan da sauri yar ta dakatar da ita da fadin kedawa ?

  A, a musali nake maki ai gara dai ki gyara don bani fatan ace za a kawo maki wata a cikin gidan nan yanzu da sunan kishiya kila kuma wanan kucakar ta nan zai dauka ya kai can yarta fada.

    Ita kuma ta amsa da sauri tana fadin tazo ina aiko da komai ya lalace min a yanzu da gaske in har Naito tazo garin nan da sunan zama ko kin manta da cewa ya auretane da yardana wai ?

  Maganan da ke nan ba yanzu ba don yanzu komai da mukayi a baya da alaman abubuwan sun badamu a yanzu gaskiya nima hakan dai nake gani amma ai idan yasan wata ai baisan wata ba.

    Tundai zancen shigowan yaron nan da kika fada karkiji yanzu yadda nake jin zafin wanan zancen don irin masu shigowan nan tsakiya sai suzo su zama wani abu a gida naka na zaune.

   Don Allah bar zancen nan aiko zan tafi hutuwace sam ba zan taba yarda da wanan shegen yaron ya shigo cikin mu yanzu dai gobe in Allah ya kaimu gobe zan tafi Nasarawa an fada muna wani boka a can wani kauye zamuyi tafiyan tare da hjy liyyatu zuwa can.

    Duk wanan wayan a kunnen mai aikintane dake duke tana jera mata abincin don taba da umurnin a kawo mata abincin a dakinta lokacin tagama jerawa ta fita tana sheda mata angama komai.

    Muna zaune aka gama tura koma zuwa ga e-mail din Bisi din duk wani takardan daya dace saida muka tura mai a lokacin bandai fadawa kowa komeye ba balle zancen ya yadu kafin hakan ya tabbata.

   Wayanane ya dauki kara lokaci guda na lalubo daga cikin jakkata shine a Latin na dauka ina mashi sallama ya amsa na dora da ina wuni ya amsa da lafiya lau kun fito break ke nan ?

  Nace eh amma yanzu gida zan tafi don ba zamu zauna karatun yamma ba yau yace test zamuyi OK idan kika koma don Allah kada ki kula duk wani abinda inna zatayi maki don Allah nasan har yanzu tana jin zafin zancen daya faru da safe tsakanin Ku.

  Kai Waya fadama hakan sai naji yayi murmushi kafin yace au had kin manta na kiraki a ways lokacin kika bar wayan kunne da sunan zaki gaisa da Dije a lokacin don haka ban kashe wayan ba ai lokacin.

   Naji koma naji duk abinda ya faru had amsa da kika bata dan haka banson wani zance kuma ya kara tasowa son run dazun nake son kiranki nasan kina class lokacin.

   Ni ya wuce ai a wuri dama kawai don ta gane na bata amsa ai kuma shike nan ai yace na sani don Allah ki bar tankawa daga yau don tana sane take komai ai.

   Kayi hakkuri idan hakan ya bata min yayi murmushi yace is OK mashin zaku hau yanzu ke nan ko nace eh don yau Nabila bata shigo ba nake gani motarta baya nan.

    OK ki kulamin da kanki nace nagode harga Allah banji dadin da yaji wanan zance ba don ba komai nake son ya dinga jiba tsakanin mu muna gama waya dashi na mayar ke nan a jakka sai naji wani kiran ya shigo again

   Na dauka shine kuma a lokacin ya sake kira said naji ummahce ashe dana dauko na dauka da sallama ta amsa ina kokarin gaida ita naji tana fadin.

   Kina school din be had yanzu nace eh ummah amma yanzu make son in koma gida min tashi ke nan race to ki kira Aisha da mamaku kiyi masu gaisuwa .

    Don yarinyar nan jaririyar ta koma dazun aka kaita da sauri na furta innalillahi was inna alaihim raji,in yanzu yar nan ta rasu ummah ashe ?

   Have eh wallahi kamar dama jira take ayi suna taiwan uwarta bara yadda aka fada son jiyama basu kwana a gida ba saida suka koma asibiti da ita a can ta cika.

  Nayi mata adduan dacewa da Rahaman Allah ga musulmi nacewa ummah yanzu zan kira Aishan insha Allahu mukayi sallama ta kashe wayan nata.

  Jikina yayi sanyi sosai ina dago kai hannatu na fadin yar Aisha ce ta koma ko nace wallahi a cikin wani irin yanayi murya a raunane .

    Dama ai yana da wuya ta rayu irin hakan sai in yaro rabone zai zauna bayan ansha wahala karshe kuma ya taso a wahalce da ciwarwuta iri iri a jikinshi.

    A hankali muke takowa data cikin school din muna maganan sai ga motar motana na gani ta gitta muna nabi motan da kallon mamaki.

    Hannatuce ta rigani magana da fadin ikon Allah wancan kamar motarki zahra nace itace wallahi waye ke janta ciki nace naga kamar sanusi ne dan yayan mama dama dan dakintane shi sosai zakace shidin ma Dan gidan mune shi.

   Kai wanan mama din gaskiya ba mutumiyar arziki bace yanzun mortar naki zata dauka ta ba dan uwanta bayan kowa yasan nakice dama taje su hau hannatu meye duniya baki dayanshi ma balls mota da zai lalace.

    Wallahi ummah ta riga da tace koda andawo da motan ma bazan haushi ba ko hakan zai zama sanadin aurenta da Abba kuwa to kinga me zai dameni no yanzu da ita duk mai hawa ya hauta ba abinda ya dameni a yanzu.

    Shiru tayi kafin can kuma tace dani amma wuri ta samu ina ji a gari ana fadin ko wanan amaryan Abba din yanzu hjy mama ta shiga gabanta amma fa yadda mutane ke fadine fa.

   Murmushi nayi bance komai to waike zahra irin matan nan basu tuna cewa zasu mutu su koma ga Allahne wai mutum ya rungumi duniya yasa a gaba irin wanan halin me zataje ta fadawa Allah akan hakan ne wai ?

    Kofa bata mutu ba zata iya tsufa ko ta nakasa kinga duk abinda tayi din nan ya tashi a banza yanzu ai gara mu biya ta gida muyi masu gaisuwa ko ta fada jin tana ta magana ban bata amsa ba lokacin.

   Bari to na kira master in fada mashi na fada ina kokarin zaro wayana daga cikin jakata lokacin wanan Sanusin ya kara fitowa daga cikin makaranta ya kwaso wasu yan mata yan UG two a motan suna tafe suna shan kida sukazo suka wuce mu kamar farko.

   Ina jin hannatu tace wallahi Allah ya isa dan iska dakai da uwar dakin naka sai kunyi kunya tun a nan duniya in Allah ya yarda wani irin dariya ta bani lokaci guda har ya dauki wayan ban sani ba ina karawa naji yana fadin a ina kike kike wanan dariyan kamar an maki bushara ?

   Wallahi hannatuce take zagan min mama da sauri naji yace subbahanallahi wace maman naki ciki nace wallahi mama da mama ta gidan mu wai kawai don taga wanan sanusi din dan yayanta a cikin motana yana ja ya kwaso yan mata keja masu Allah ya isa.

  Sai naji yayi murmushi yace kai hannatu bata rabuwa da shirme wallahi ta bari idan nayi kudi in saya maku motar daba me karbe muna saidai Allah.

  Balle har wani gardi ya hauta wanan tamu dukane yanzu tunda na Abbane kowa yana da right din da zai hauta yanzu namu nan zuwa da yarda ubangiji.

   Murmushi nayi tare da fadin Allah ya nufa saidai kada ai kudin sayen motan aje a dauko min wace zata hanani zaman lafiya dakai kuma.

   What ya fada da karfi nayi murmushi tare da fadin nawa akayi muna gani dama tunanen ki ke nan zahra a kaina bari anji mu karasa mun samu dan mashin yanzu zamu shiga na bashi amsa na kashe wayan ina murmushi.

 

No comments