Breaking News

TUMFAFIYA 67


 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/6, 11:08 PM] +234 816 310 0038: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH  ,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

6️⃣7️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

 

  Har na kwanta naji waya na ringing na dauka hannatuce cikin damuwa take fadin don Allah zahra kiyi hakkuri bansan cewa ranki zai baci haka dani ba.

   Na dauka yadda nayi zai taimaka maki gun mahaifinkine amma naga ranki ya baci da hakan kiyi hakkuri don Allah ta sake fada a sayaye.

    Bakomai amma gaskiya banji dadin hakan ba wallahi wanan matsalance ta cikin gida Hannatu bai kamata ki zake irin haka ba tunda nima kinji nayi shiru a lokacin gaskiya ban fatan irin hakan ya sake faru garemu.

   Na fahinta yanzu Zahra in Allah ya yarda hakan ba zai sake faruwa ba kuma na kirga kudin da Abba ya bani har dubu talatin nagode kwarai wallahi.

   Bakomai nina kwantane saida safe nace da ita ina hamma tace Allah ya bamu alheri amma barci da wuri haka ni dai na kashe wayan don ban iya surutu a lokacin.

  Sati daya kacal da hakan sai ga kiran wayan brother Bisi fitowana daga aji ina bakin masallacin mu zan shiga naji waya na ringing na tsaya na ciro da sauri ina dubawa naga sunan shi a rubuce a screen din wayan yadda nayi serving.

   Na dauka da sauri tare da sallama ya fara fadin takardun sun iso an kuma yaba da kwazon mijinki sosai a takardun nan.

    Saidai zai barki ya taho nan suyi interview yaya kika gani ya tambayeni cikin son jin amsan da zan bayar a lokacin da sauri nace haba brother koya kama ya zauna can ne aiba abin damuwa bane agareni yanzu .

   Muna maka godiya da wanan kokarin dakayi muna sosai saidai zuwa America yanzu gaskiya ba karamin abu bane a garemu gaskiya.

   No kubar komai a hannuna nine zan dauki duk wani nauyin tafiyan nasa har yaje ya dawo insha Allah fatana kawai ya yarda da hakan don mu cinwa manufar mu na taimaka mashi da nake sonyi ?

   Insha Allahu ba matsala don ya yarda dakai saboda na fada mai halakarmu dakai kana matsayin babban yaya a garenine sai naji yayi murmushi yace amma baki fada mai nine naso auren ki kamar in mutu ba ko ?

   Nima dan murmjshin nayi tare da fadin ba aure a tsakanin mune sai zumunci irin haka shiyasa Allah bai kaddara muyi aure ba na dora mai da gidiya bisa karamcin da yai muna din don a katse wanan zancen na tuna baya.

    Mukai sallama ya fada min na turo mashi da account dina dana mijina nace yayi hakkuri ya karbi na mijina kawai yakece min kona raina da abinda zai turo min din ne nayi min kadan ?

  Da sauri nace a,a ko bansan ko nawa bane nasan masu yawane kuma mai amfani a gareni yace to na turo zai kara kirana insha Allahu.

    Har na fito sallah ina tunanen zancen mu dashine haka kuma ban fadawa hannatu ba tun farko don na kula tana da yawan surutu Allah daine ya hadani da ita.

    Bayan na dawo gidane na danyi girki nakaiwa Dije don na kwana biyu banyi girki ba shiyasa na dora donta kawai dama tun a get din school na sayo danyen nama da kubewa da alaiyahu nazo dashi gida.

    Girkina a natse nakeyi yadda na saba har na hada tuwone Aisha data shigo ta karba ta tuka min shi muna hira muka saka a leda na bata ta mika min zuwa cikin gidan .

  Wanka nayi na fito na tayar da sallah don lokaci har ya dan shige muna kitchen din bayan na idar na zauna na dan jawo jakata ina duban  a lokacin idona yakai kan ledan da ummah ta bamu ranan bacin rai ya hana in duba tun ranan.

   Danbun kifine dana naman kaza sai sai yaji naci a ciki da wani kwalban tutare mai kyau itin na Dubai din nan da ganinshi zaiyi tsada sosai don har da armpit dinshi daga gefenshi an rubuta mai Noor haiyat a jikinshi da larabci da kuma boko.

    Bayan na gama duk sallolina na fito na dauko leda a kitchen na diban masu wanan dambun nashiga cikin gida dashi na kai masu.

   Na gaidasu da wuni dije ta karba min tana kiciniyar bude ledan dana mika mata din daga can naji inna na fadin wai wai wai yarinyar nan ina kika fito da kayan dadin nan haka ?

   Nace wallahi ya dade a dakina ummah tace tabani shi tun ranan da mukaje gida gaisuwan yar anty Aisha din nan ban bude ba sai yau shine na debo maku.

  Nidai naji Dije na munko gode Allah ya karawa arziki albarka nace amma Inna ko uffan batace min ba sai  zuwa can naji tace ai irin wanan abin haka bai kamata a fitar dashi a gidan nan ba tunda tayarwa mutum da kwadayi za ayi ga banza.

   Jinta fara sakin magana haka yasa na mike tsaye lokaci guda ina fadin to saida safe ku zanje in kwanta.

   Ban karasa fitaba naji Dije na fadin wanan rayuwa naki baiyi ba ke kan data cinye bata bamu ba shine nufin ki tunda bai isheki ba watau ta karo maki ko ?

    Kai umma zaki fara juya zancen ki ke nan duk akai maganan daya shafi yarinyar nan saiki mayar ya zama naki ni bansan abinda yasa kike haka ba wallahi.

   Banji amsan da Dije ta bata ba don nayi nisa a lokacin ba kwanciya nayi ba a lokacin don na samu wayata da miscalled dinshi don haka na sake kiranshi ya dauka yana fadin barin kiraki.

   Bayan na kashe ina gyara kwanciya naji ya sake kirana lokacin na dauka muka gaisa yake tambaya mutanen gida da karatu na amsa da lafiya.

    Kina cikin gida halan bakiga kirana ba ya tambaya na amsa da eh naje kawai Dije abune dama naso na kiraka tundazun sai aiki yai min yawa ban samu lokaci ba.

   Meya faru nace dama brother Bisi ne ya kira dazun wai ka shirya zakuje interview a can kuma, , ,  ban karasa ba naji yace inafa ke nan zamu tafi ?

   Can America din yace sai naji yayi murmushi yace kai zahra akwaiki da son wasa wanda ko lagos bai taba zuwa ba shine zai tafi har kasan America yin me a can ?

   Allah kuwa kuma yace ka turo mashi da account din ka na bank zai turo maka da kudin da zakai visa da sauransu nima kuma na tura nawa ya bani wanda zaka barmin a nan yace.

   Anya zahra abin nan baiyi yawa ba kuwa mutum ba dan uwanka ba ya kashe maka wanan uban kudin haka gaskiya ya kamata muyi nazari akan maganan nan.

    Amma kasan bamu rokeshi ba shine yayi niyar hakan don ya samu lada masu halin alheri haka suke abinsu sai su duba inda akafi bukata su taimaka don ladan hakan ya kai garesu.

   Tunda nasan shi da wanan halin na sanahi dashi gaskiya don lokacin daga mu har yayyen mu maza haka zai kaimu ayi shopping  kowa ya dauki abinda yake so a dawo gida shiyasa muke jin dadi idan yazo hutu lokacin.

    Wani irin ajiyan zuciya naji ya sauke kafin yace to shike nan ba kinada account dina ba ki tura masa mu gani idan abin mai yuyuwace garemu sai naje.

    Mun dan taba hira mukai sallama na kashe wayan ina tunane kafin barci barawo ya daukeni can tsakiyar dare ina barcin na fara mafalki wai nakaiwa dabbobin su ruwa sai wanan bakar akuyar da suke kira da uwar garke take ce min.

    Kinyi kokari zahra dadin hakkurin ki yana tafe insha Allahu a sanadin ki yau Allah zai cika muna burinmu mu bar bawan Allah yayi rayuwan sallama.

  Zakice mutumce yar uwana muke hira a lokacin da ita sai har nake ce mata kuda suwaye tace nida na tare damu ai tun yana goye muke bibiyan lamarinsa.

  Tun ranan da uwarsa tayi fushin zuciya ta barshi waje a tsakar gida shi kadai ya kwana don mahaifinsa zai wuce ya barta tun wanan ranan muke bin duk wani al,amarinshi.

   Wanan mahaifiyar nasa tayi watau da yawa akan zafin kinshin barin mijinta har ta dorawa dan yaro laifin dabashi bane yayi shima mahaifin nasa ai kiran gagawane ya samu bai isa ya kara kwana uku a wanan garin ba lokacin.

    Amma duk basu gano hakan ba a lokacin saboda idanunsu ya rufe sun kasa fahintar ba tafiyan lafiya zaiyi a wanan lokacin ba.

   Ki tambayeta kiji a cikin darene suna kwance ya zabura yake fada mata inane nan meya kawoshi nan ita din waye har taso dora mai rashin hankali a lokacin.

    Amma da akai mai bayani ya gamsu bai kisu ba ya kuma karbesu hannu bibiya har ya bukaci a barshi yaje dasu garinsu amma iyayyenta sukai tsaye ba zasu yarda da hakan ba.

    Munturashi garin baban shi mun hadashi dashi ya ganshi duk ta hanyar hikima irin namu mune kuma mukasa a karya asirin a yanzu haka yana gab da haduwa da mahaifinshi insha Allahu.

    Munyi maganganu da dama da ita har da wanda ya shafi rayuwata dana gidan mu wanda hakan ya bani mamaki sosai a lokacin.

   In kina son ki gaskanta hakan ki tambayi tsohuwa yadda akayi rikon mijinki ya dawo gareta don sunso ya mutu a lokacin daga mahaifiyarshi har yan uwanta sai tsohuwar nan da mijintane basu yarda da hakan ba.

    Ki fadawa mijin ki in mahaifinshi ya zo gareshi kada ya nuna masa bacin ransa don shima ba yin kansa bane hakan duk da an fadamai a baya.

   Ni zan koma gida dama nazo mu gaisane kuma in isar maki da sako gareku daku kara hakkuri farin cikin ku yana tafe bada dadewa ba amma sai kin hada da hakkuri ga abinda zai biyo baya.

   Ina kallonta sai naga ta shige cikin icen tumfafiyan dake daga can gefen rumfarsu sai wani haske ya baiyana kamar walkiya a lolacin ta bace.

   Sai lokacin wai naji tsoro na yanka wani irin ihu ina salati hakanne ya farkar dani daga barcin kuma ina ihu ni kadai a cikin daki ga wani irin duhu daya mamaye dakin bako dan haske sai hakan ya kara ban tsoro a lokacin.

  Can naji kamar abu yana bin wuyana da sauri na shafa saidai bani ganin komai a lokacin amma ina tamtaman zufa don yadda naji goshina ya jike a lokacin.

  Amarya lafiya kike kuwa ta dai bude kofan mu shiga naji muryan Inna bayan na Dije dake tambayana a lokacin hakan ya sanar dani cewa ihuna yakai ko ina a gidan ba iya cikin mafalki nayi wanan ihun ba ashe ?

   Wayata na laluba inda na ajeta saidai ban jitaba a inda na aje din haka yasa na fara lalubenta da sauri kafin naji wani motsi a dagan dakin kamar wani abu ya fita dakin da sauri lokacin.

   Jin hakan ya kara min kaimi wurin lalubo wayan najita can karshen gado na dauko na haska ina amsa kiran da Dije din ke min a lokacin a gagauce hankali tashe.

   Na samu na amsa ina kokarin bude kofan dan falona jin ina budewa inna ke fadin ko lafiya dai kike wanan ihun haka da tsakar daren nan na bude ina fadin lafiya inna kila mafalki nakeyi.

    Wanan mafalkin ko ba maikyau bane da jinsa tunda baki taba irin sa ba a gidan nan kai wallahi duk munji tsoro mun daukama wani katone ya shigo maki ai kike wannan ihun hakan.

   Kaiya ina wanan zancen ya fito maki kuma haka babu dadin ji a bakinki wanga wani irin fatan banzane kuma ga sarakuwan ki da zaki mata zaton kwarto a dakinta ?

     To umma nidai ban iyawa a cikin daren nan yadda tayi ihun ne yasa na fadi hakan ke wuce muje mu karasa daren tare a nan Dije din ta fada yaran nan na tayaki kwana amma saida aka san yadda akayi aka hanasu kwana tare dake dakin nan.

   Ni ban hanasu ba itace dai take nuna bata so don kafin suzo ta rufe kofanta ta juya ta tafi tana fadi adan hasale tabarmu da Dijen nan muka kwana tare da ita a part dina.

    Washegari sai bayan mun idar da sallah wuri yayi haske ta fita zuwa dakin ta tana min adduan tsari daga duk wani shedani dake bin bayana a rayuwana na amsa da Amin.

  Har nagama shiri na tafi makaranta duk da akwai barci a idona sosai don rashin samun safiya da banyi ba na karfe hudu zuwa biyar da bawa kanji dadinshi a lokacin fiye dana tsakiyan dare.

 Sai wajajen karfe ukune wani irin zazzabi ya fara ziyartana a lokacin sai gashi duk dauriyan da nakeyi na kasa hakan don jiki har yana kaduwa hakorana suna hadewa wuri daya a lokacin don zafin zazzabin daya sauka min lokacin.

 Da taimakon su hannatu na samu na dawo gida tare da ita a ranan haka muka shigo gidan ina gigice cikin wani yanayi.

  Hankalinsu Dije ya tashi ainun don inna batama gidan a lokacin ganin haka yasa Dije fadin Aisha maza karbi canjin nan kije wurin mai kemis ku sayo mata paracetamol ta hade.

   Ta karbi kudin da sauri zuwa wurin mai shago din tasayo maganin aka kawo min ko kallonshi banyi ba don ban masan inda nake ba lokacin.

   Ganin yadda nake hakan ya tayarwa hannatu da hankali tashige daga kuryan dakin ta kira ummah tana fada mata abindake bata wani daga hankali ba sai cewa datayi da hannatun ga Tani nan zuwa ta gani.

    Zuwan tani tazo min da magani daga wurin ummah na tasa akai min hayaki a dakin takumayi dabaran shaka min a hancina lokacin sai da aka dauki lokaci na dan samu nayi attishawa maidan karfi Allah dai ya taimaka iya mune a dakin lokacin daga haka kuma barci ya daukeni lokacin.

   Wayana ke ringing ta dauka master ne jin an daga wayan yake fadin haba dai my princess kinsan ina exam shine koki kirani kiji ya pepper ?

   Hannatu ce master muna gida zahra ce ba lafiya wallahi sai yanzu ta dan samu barci tayi yanzun hakama tana barcine.

   Subbahanallahi bata da lafiya meya sameta ya tambaya cikin damuwa take fada mai dai dukkan abinda ta gani tace kuma a karshe zazzabine dai mai karfi ya rufeta.

  Bakuje asibiti bane da ita hannatu ya tambaya cikin damuwa a muryanshi sai tace munje asibiti sun bata magani nan school cleanic .

    Daga school din muka dawo gida da ita ina gudun mu tafi  FMC daga can ya zama magana kuma amma yanzu ummah ta aiko da magani tasha shine harta samu barcin.

   Ok kun sanar mata ke nan to yaya jikin da sauki yanzu ko ya kara tambaya tace da sauki gaskiya bisa ga dazun din don yanzu har gata tana barci Dije ma tabada kudi kuma an sayo wani maganin  chemist dazun da muka dawo saidai bata samu sha ba.

    Don Allah hannatu idan ta falka kikaga tana jin jikin ki taimaka min ku tafi asibitin zaifi tace insha Allahu, master and please call me indan ta falka tace mai tau.

   Gida kan yanzu ya canza don da can gidan shirune don sauran yaran gidan dake makaranta a lokaci amma zuwan su hjy murja yasa gidan ya rayu tsakanin jiya dayau din nan .

  Har zaka danji hayaniyan mutane jefi jefi babu komai a ran hjy murja din a lokacin sai fargaba da tsoron hjy yabi don sanin halinta da tayi na rashin barwa Allah zance.

   Gashi tun zuwan su garin ba wanda ya lekosu daga bangareta son ko yarta murja bata kara bi ta kansu ba lokacin asalima ta manta da zancen wasu baki a gidan lokacin.

   Andai kawo masu abinci da suka iso haka an kawo masu na dare sunci tun lokacin ba wanda ya kara leko part din nasu sai su kadai ke sha,aninsu suma di  cikin sakin jikinsu suke komai.

   Washegari misalin karfe bakwai da rabi na safe wanan mai aikince tayi sallama ta sake shigo masu dauke da manyan kuloli ta aje masu kana ta gayar dasu da kwana.

   Suna gaisawa ta daga zata wuce taji dayan na fadin mama kece mai aikin gidan nan ko ta juyo tana dan murmushi tace nice dai daga haka tayi sauri ta fice part din.

   Tana fita dayan ta bude dayan kulan taga soyayyen kwaine da irish acikinsa saida aka cika har baki dayan kuma ferfesun kayan cikine a cikinsa mai yawa wanda zai ishesu sai dayan cuscusne yaji hadin kayan labu an zuba mai kamshi da kalan abinci ya canza kala.

    Itace ta dawo dauke da kofuna da bread manya guda uku sai kayan shayi ta aje masu a inda ta aje na farkon suna mata sannu ta dawo da flask din ruwan zafi ta aje ta fita suna mata godiya.

    Wanka suka fara shiga sunayi kafin su zauna gaba dayansu suna karyawa a lokacin nan dayan kewa yan matan fada cewa su dai iya kansu a gidan yadda sukaga yar uwansu tanayi banda rawan kai da saka ido ga komai.

    Sai bayan sun gamane an dan jima Alh ya shigo suka gaisa yake kara masu bangajiya kafin ya dago yacewa matar nasa murja.

 

No comments