Breaking News

TUMFAFIYA 68


 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/10, 10:40 PM] +234 706 815 1331: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH  ,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

6️⃣8️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

 

Jiki wasa wasa yaki dadi gareni a kullun sai kara gaba gaba yake min hakan yasa har na dauke kafa ga zuwa makaranta a lokacin.

   Tun hankalin inna bai dagaba har wani dare dole ta fito da damuwanta fili ta nuna tausayawanta gareni tana fadin kalamai a tausashe saboda ta tsorace da yadda tagani kwance.

   Ganin zan mutu a gida sai magani nake sha ba a san makarin ciwo ba yasa nasa hannatu kiran ummah ta fada mata halinda nake ciki din.

   Sai cewa ummah tayi yanzu hannatu ya kuke son nayi tunda nauyin ta ba a hannun mu yake ba yanzu kawai dai ku kira mijinta ku fada mai abinda yace sai ai hakana.

 Ga hankalin hannatu duk a tashe yake shi kuma macan hakane gashi suna test a lokacin suna gab da zana jerabawan fitane a lokacin.

  Data kirashi cikin daren tana  mashi bayani hankali tashe murya kamar mai kuka yake fadin don Allah ummah tayi hakkuri a taimaka mashi ga halinda yake ciki.

  Amma sai hannatun ta kasa kiran ummah din don yadda sukayi da ita da farko dole dai shi din da kansa cikin dare da inna taga zan mutu ta kira shikuma ya kira sai hankalinta ya daga sosai ta kira shehu da daren nan yanzo suka kamo hanyar gidan mu din.

    Da karfe Biyar da rabi na asuba ummah sukazo da shehu aka daukeni zuwa asibiti muna zuwa fada suka fara cewa yaya akayi har na gala baita haka ba a shigo dani asibiti ba.

    Nan dai suka karbeni baya  korafi da sukasha wurun nurse din tayi muna hanyan ganin likita ya auna yasa a sayo ruwa da magani aka dora min sai lokacin na samu barci mai nauyi ya daukeni sosai.

   Ana idar da sallah asuba yana kiran layin wayana yajishi kashe sai na ummah din ya samu tana kuma azzakar bata magana a lokacin sai ta idar.

  Hakan ya daga mai hankali ganin ya kira har sau uku karshe ma ta kashe wayan gashi duk sauran wayoyin nasu basa shiga a lokacin nan ya soma shirin baro zaria duk da yasan test din dake gareshi yana da muhinmanci sosai a lokacin.

    Ya gama shiri zai fito wayanshi ya dauki kara ummah ce mai kira a lokacin gabanshi na faduwa take fadin tana sallah a lokacin yasa bata daga waya ba.

   Bai tsaya gaida itaba yace ummah ya mai jikin kuma tace da sauki sosai ta samu barci gata nan kwance tana barcin tunda aka fara karin ruwa.

  Sauran gwaje gwaje sunce sai gari yawaye za ayi ka kwantar da hankalinka don da sauki sosai insha Allahu zata samu lafiya yace to ummah da yanzu zan biyo hanya inzo.

  Tace a,a ba ance kuna test bane kokazo me zaka iya mata kadai mata addua shine take bukata ta samu lafiya sosai fa yanzu don numfashin nata ya koma daidaima a yanzu.

  Jin hakan yasa shi ya tsaya ba don yaso hakan ba a lokacin anyi duk wani abinda yadace ayi amma sai cewa sukayi maleria da thaphod ne ke damuna a lokacin.

  Karfe takwas ummah ta kira gida take shedawa mama suna asibiti dani tunda safe mama din ke fadin me kuma ya sameni tace zazzabine dai tayi Allah ya sauwaka ta kashe wayan a gundure.

   Bayan ta kashe take jan tsoki tana fada su gwaggo shafa ne dai sukai tawaga sukazo dubana anyi sa,a lokacin Tani ta kawo kayan da ummah ta umurceta da takawo muna asibitin.

   Da badon hakan ba babu komai da inna tayi yunkurin biyomu dashi asibitin saidai sunzo dubana ita da yaranta tunda farar safiya shine kawai gaskiya kokarinta a lokacin.

   Karfe daya saura yana cikin gusau asibitin ya nufo daga nan ko gida bai isa ya aje kayanshi ba yazo har dakin da nake kwance har lokacin barci nakeyi sosai don gaskiya na wahala.

  Kwana biyu bama barci da hannatu data zauna a wurina a karshema har makarantan itama ta daina zuwa tana zaune tare dani a gida tana kula dani don har mutanen gidansu saida sukazo gaidani.

   Mamako Abba ta kira tana fada wai ummah tana kokarin raba daya biyu duk hakkurin da takeyi da halin ummah zata kaita makura wai suna asibiti dani amma ummah bata fada mata ba sai da ranan nan donta dauketa muguwa kome ?

   Amma ta fada min ta kiraki tun takwas na safe ma don na tambayeta ta kira ta fada maku tace eh yanzun ta gama waya dake ta sanar maku.

   Wai halin hjy salmane kuma baka sani ba ni dai na fada bana son hakan da take min gaskiya da wani abune da yanzu ta kira tana fadama sai kawai ta kashe wayanta lokack guda a hasale.

  Duk da yaji mamakin hakan  data fada amma kuma ba zai iya cewa komai ba a lokacin karshema kiran ummah yayi yana fada don me bata fadawa mutanen gida zancen ciwona ba.

   Ina wani abune aiduk ita tajawa kanta wanan wullakancin tunda ita tanacewa wanan fakirin yaron tace shi zata aura yanzu duk wullakancin daya biyo baya ai ita tajawa kanta kuma ?

    Ummh,humm ka gama kada ka mace da duk mai rai baya wuce kaddaransa a rayuwa ni ban raina da auren zahra da yaron nan ba don bansan dalilin da Allah ya hadasu tare ba.

   Kuma ai naga banina aurawa yarka shiba kai kaga dama ka aura mata shi a matsayinka na ubanta koka taba jin inda mace ta aurawa yarta aure koda kuwa shegiyace ita ?

   Sannan ita hajiyan datace ban fada mata ba Allah ya sheda karfe takwas na kirata na fada mata itace mutum na farko dana fadawa kuma har kusan duk yan uwa sunzo asibitin nan duban mu.

   Kawai idan wani tsegumi takeji dashi ta fada zaifi amma ba wanan ba taje tayishi a wurin ka kaida kake daukan tseguminta ba bincike ko yaushe ni ba wanan bane a gabana yanzu ba.

   Tana fadin hakan ranta ya gama baci sosai a lokacin don haka ta kashe wayan a hasale Allah ya taimaka daga ita sai tani dake shirin zuwa gida a lokacin sai koni dana falka banyiwa kowa magana ba nake jin yadda sukeyi da Abba din.

  Da kuma fadawa Tani abinda ya faru din da takeyi a hasale tana hawaye tare da fadin kasheni suke son yi ni wanab abin ya isheni a yanzu gaskiya idan kayi magana ace kayi hakkuri don yara kuma.

   To hjy idan ba hakkurin ba me za a baki yanzu halin hjy maimuna ne kin saba dashi makircine kawai irin nata ta dauka wani kudi zai turo maki ai laluran nan dashi shine take kokarin bata tsakanin ku ayanzu.

   Makircine kawai irin na mata ita dai kada taga anyiwa yar uwa wani hidima sai a yaranta kadai gashi kuma Allah ya kadara yaran nata da yan uba.

   Ni bashiba Tani yadda Alh ke biyewa maganan ta ya rufe ido yana neman yaciwa mutum mutunci akan zancen ta haka suka kwasa da hjy karima wanan zuwan da sukayi akan dan abu kadan yaso ya bata mata kanta ita kuma ta rufe ido taci masu mutunci dukkansu gaba daya.

   Karshe sukai tafiyan barambaram suka koma kowa da tasa tafiyan jin hakan tani tace kin gani ba haka take ta kokarin yi gareki amma hakkurin ki ya hana tayi nasara akanki shiya take kara kaimi ga aniyarta din.

   Kiyi hakkuri hjy a kullun shi muke baki kinga kar yar nan ta falka ta sameki a cikin yanayin bacin rai haka kuma ba zataji dadin ganin ki hakana ba gaskiya .

  Ni yanzu zan koma kada yaran su dawo su samu ba kowa a gidan kuma su shiga damuwa don ba wani kulawa zasu samu a wurinta ba.

   Mummy kizo wai inji daddy yana falonsa zaune Salima ta fada daga kofa inda take tsaye hanbayenta na cikin aljihun rigan dake jikinta lokacin.

   Ta dago cikin takaici tana kallon yar nata tare da fadi  sai yace idan kinzo ki mun kerere a kai ki fada min ko wai Salima meyasa baki da tunane ke kullun kina abin yara ?

    Mummy shiyasa na kiraki ba nina fadi hakan ba ta fada cikin shagwaba tana junawa zata bar dakin a lokacin tace kaji sakarai ina magana kina kokarin wucewa.

  To kiji da kyau duk wanan sakarcin yanzu ya kamata ki daina shi ki nuna kin girma kinsan ciwon kanki don bamu kadai bane a gidan nan yanzu don kinga ya kwaso muna wa yancan mutanen duk da nasan anyi hakan ne da wani manufa a garemu.

   No mummy ba matarsa bace don haka yana da right din da zai kawota nan mana ta zauna damu saidai abinda  ban yarda ba shine tace zata  rainamu.

   Wani kallon ashe kina da wayau uwar tayi mata ta kawar da kanta gefe daya tana fadin zamuyi maganan hakan anjima yanzu kice masa kin samu ina bayine amma kin fada min.

    Koda ta je fadawa mahaifin nasa saita samu hjy murja a falon zaune zakace bata taba sanin taba a duniya sai cewa da tayi daddy na samu tana bayi amma na fada mata yace is alright zaki iya tafiya.

  Ta juya zata tafi a lokacin hjy murja tayi karfin halin fadin salima mun sameku lafiya ya karatu ?

    Lafiya kawai ta amsa dashi tana ficewa suka kalli juna da mijin tayi wani irin guntun murmushi mai nuna cewa dama na fada maka ai.

    Sai ji tayi yace dama wai baka ga juna bane tun jiya din tace ga alama ka gani kuwa irin abinda nakewa gudu ke nan tun farko nace ka barni gida can din yafi min rufin asiri don nasan halin hjy da yaranta sarai.

   Zasu iya komaiwa mutum idan sunyi niya balle a yanzu gidansu nazo na samesu don haka zasu shiryawa hakan baiyi magana ba sai zuwa can da yace nasan da hakan amma wanan shine tsarina a yanzu naga na hada kan iyalina a wuri daya.

   Sun kai wani lokaci a zaune wurin kafin ya kalleta yace zaki iya tafiya ki barni da ita nan gaba zamu zauna zan fita yanzu zuwa office tayi mai Allah ya tsare ta mike ta fita.

   Shima bai dade a zaune ba ya mike ya shige ya shiryo zai fita suka hade ko kallonta baiyi ba yasa kai zai fice take fadin salima tace kana kirana ?

    Banda wanan time a yanzu ya fada yasa kai ya fita taja tsoki itama ta fice daga falon zuwa part din ta har ta zauna wani zuciya ya debeta ta mike zuwa part din da bakin nasu suke.

  Zaune suke dukkansu a falo suna hira saigata ji sukayi kawai an fado dakin ba sallama hakan bai hana dayan tace a, a hjy Yabi ce yanzun muke maganan ko kun tashi muje mu gaisheki ai.

   Hannu ta daga alaman tayi mata shiru a lokacin kafin ta bisu da kallo daya bayan daya ta sauke idonta akan hjy Murja din tana fadin murja meya kawoki gidana a wanan lokacin?

   Hjy murjan ta dago ta kalleta tayi dan murmushi kafin tace amma dai musulmai kika samu a dakin akala kyayi sallama ko zamu san damu kike zancen a yanzu ?

    Murja watau har kin dauka wuyan ki ya isa yanka a gidan don dan wanan asirin naki da ayanzu kike ganin yana aiki akan Alh ke nan to barin fada maki kiji kuma ki rike idan kina tafiya da rana tsaye ni yabi dare da ranan duk a tsaye nake indai akan gidanane kece kika fara yanzu.

   Lalai kuma kinyi sa,a malamin ki ya iya aiki harda ya iya karya dokana yasaka Alh ya dauko ki daga kauye zuwa wanan gidan a yanzu saidai kinyi kuskure babba na yin hakan .

  Don in kishigone ta gaba ta birkice zaki koma wata kilama wanan karon ba inda kika fito zaki koma ba sai wani bakon waien.

   Kowa na dakin sai binta sukeyi da kallon mamaki daga can inda yan matasan yan matan ke zaune da sauri  dayan ta kunna waya tana daukan komai dake faruwa a dakin lokacin saboda yarinta.

   Hjy yabi ke nan ban kara tabbatar da cewa ke din jahila bace sai yau din nan da kike wanan ikirarin haka a gaba saidai ki sani .

  Ni murja ba yar matsafa band ba kuma jikansu bace a gidanmu musan Allah da Annabinsa tsagwaron su haka kuma da shi na dogara a rayuwana don shine boka da malam din gidan mu kinga tunda har Allah ya amsa min addua na akanki saina kara gode mashi.

   Karya kikeyi munafukan Allah duk inda kike zuwa ai munsani don abin duniya ba boye yake a kasan nan indai indai bera bai daina yawon dare ba wata rana su hade da mage wurin yawon ai.

   Ta jiya a fusace ta bar dakin cikin kunan rai tare da mamakin canzawan hjy murjan don bata taba tsamanin irin haka ba gareta wanan abin ya bata mamaki matuka.

   Abin mamaki baya karewa  sai ga hjy yabi din na fadawa Alh wai yayiwa hjy murja iyaka da ita don ta nuna ba zaman lafiya tazo yiba a nan don tana ganin kamar ka daure mata yanzu.

    Har tana nema taci min a  mutunci a gaban yan uwanta har tana fadin zataga iyakanta yanzu a gidan ke nan dama da wani manufa tazo nan ke nan.

   Ya juyo ya bar abinda yakeyi din gaban mirror dinshi yana fuskantar ta abinda ya dade bai faru tsakaninsu ba ya dan murmusa yace.

  Cikin kada kai Yabi kada ki manta da  cewa ni din nan ni na aje kowan ku a gidan nan haka kuma nasan halin ko wacen ku.

  Don haka ke me kikaje nema a part din ta don naga ni kaina na nemi kizo nan kika bata min lokaci ki kaki zuwa don ki nuna mata koni ban isa dake a gidan nan.

    Don haka kina tsanmanin yanzu zaki samu wani girma a wurin murjan ke nan a gabanta fa kika nuna banda daraja ko kima har a idon yayan ki ?

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/15, 10:17 AM] +234 908 769 2191: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,


No comments